Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mun kashe tirliyan 8.9 kan manyan ayyuka a 2020 - Osinbajo
Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya
Rahoto kai-tsaye
Imam Saleh and Buhari Muhammad Fagge
Isra'ila za ta bude ofishin 'yan sanda na dindindin a UAE
Jaridar Burtaniya ta Daily Telegraph ta ruwaito cewa 'yan sandan Isra'ila za su bude ofishin dindindin a Hadaddiyar Daular Larabawa a karon farko.
Jaridar ta ruwaito jami'an kasashen biyu sun ce dalilin bude ofishin shi ne shawo kan aikata manyan laifuka a UAE wanda wasu manayn masu aikata laifuka na Isra'ila ke yunkurin yi.
Sun kuma ce sabonta alakar da kasashen biyu suka yi, masu aikata manyan laifukan Isra'ila za su yi amfani da wannan damar domin kutsawa kasar, musamman da tattaunawar yaukaka alakar da ke tsakaninsu ta yadda 'yan kasashen biyu za su rika shiga juna ba tare da matsa bincike ba.
A cewar jaridar ta Burtaniya, yan sandan na Isra'ila za su bude ofishin nasu ne a Dubai. consulate in Dubai.
An kashe wani kasurgumin dan daba a wajen kotu a Delhi
Ana sake duba tsarin tabbatar da tsaro a kotunan da ke Delhi, babban birnin kasar Indiya bayan da wasu mutum biyu sanye da kayan lauyoyi su ka harbe wani kasurgumin dan daba har lahira yayin da ake zaman wata kotu da ke ma sa shari'a.
'Yan sanda sun ce mutane biyun da su ka kashe Jitender Gogi mambobin wata kungiyar masu aikata manyan laifuka ne da ba sa ga maciji da kungiyarsa.
Sai dai 'yan sandan sun kashe maharan a cikin harabar kotun.
Kungiyar lauyoyin Indiya ta ce mambobinta ba za su halarci zaman kotuna ba ranar Asabar saboda harin da aka kai.
An kama gwamman mutane da ke daukar nauyin 'yan bindiga a Burkina Faso
Sama da mutum 70 aka kama a Burkina Faso saboda zargin alaka da kuma halasta kudaden haram da daukar nauyin 'yan bindiga.
Wadanda aka kama ana zarginsu da hannu cikin rikicin da ake yi a yankunann da masu ikirarin jihadi da ke ayyukansu a kasar.
Masu binciken sun ce da akwai masu kai wa wadan nan mutane man fetur cikin dare, inda suke kai musu dubban litar mai a fadin kasar.
Kimanin mutum miliyan 1.5 ne suka rasa muhallansu yayin da ayyukan masu ikirarin jihadin ke kara ta'azzara a Burkina Faso.
'Yan siyasa ne ke da alhakin rikicin Tambura na Sudan Ta Kudu - MDD
Wata tawagar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce manyan 'yan siyasar Sudan Ta Kudu za a zarga da rikicin da ke faruwa a yankin Tambura da ke arewacin jihar Equatoria.
Kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya sun ce jihohi tara cikin 10 a Sudan Ta Kudu na fama da rikici - ga kuma wannan cikicin na kabilanci da ya barke tsakanin kabilun Azande da Balanda a Tambura wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 100.
An rika yi wa mata da yara kanana fyade ana kuma cin zarafinsu ta hanyar lalata, kafin daga baya a kashe su, kamar yadda rahotanni ke cewa.
An kuma ruwaito cewa akalla fararen hula 80,000 ne suka tsere suka bar muhallansu, yayin da daruruwan yara suka rabu da iyayensu.
Mun kashe tirliyan 8.9 kan manyan ayyuka a 2020 - Osinbajo
Mataimakin shugaban kasar Najeriya Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya ta kashe naira tirliyan 8.9 kan manyan ayyukan raya kasa a 2020.
Osinbajo ya bayyana hakan ne a Akwa Ibom yayin kaddamar da ginin Dakkada mai hawa 21 da kuma aza tubalin rukunin gidaje na Dakkada a ranar Juma'a.
Osinbajo ya ce wannan gwamnatin ta Muhammadu Buhari ta zuba kudi a kan manyan ayyukan raya kasa, fiye da duka gwmnatocin da aka yi a baya.
Sojin Isra'ila sun kashe wani Bafalasdine a gabar yamma da kogin Jodan
Sojin Isra'ila sun harbe wani matashin Bafalasdine a ranar Juma'a yayin wani taho mu gama da suka yi dama su zanga-zanga a garin Beita na birnin Nablus da ke arewacin yamma da gabar kogin Jordan, in ma'aikatar lafiya ta Palasdinawa.
Masu zanga-zangar Fatah da ake yi a Nablus sun sanar da cewa sunan matashin Muhammad Ali Khabisa.
Shekarar shi 27 a duniya, kuma kwanan nan aka haifa masa dansa na farko.
Kamfanin Dillancin Labarai na Falasdinu ya ruwaito cewa wasu mutum takwas na daban na kwance a asibiti sakamakon raunukan da aka ji musu.
Tun daga Juma'ar karshe ta watan Mayu ake samu zanga-zangar taho mu gama tsakanin mazauna kauyen Beita da sojin Isra'ila kan biyan diyyar mutanen kauyen Jabal Sabih.
Zulum zai dauki ungozomomi aiki
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum zai dauki ungozomomi da masu aikin jinya da sauran ma'aikatan lafiya domin kara samun ma'aikata da ake bukata a asibitin haihuwa na Maryam Abacha da ke Maiduguri.
Za a kafa wuta mai amfani da hasken rana a cibiyar karbar haihuwa dake Gwange domin kara samar da ruwa tsaftatacce.
Gwamna Zulum ya bada wannan tabbaci ne a ranar Alhamis lokacin da ya kai wata ziyara asibitocin biyu domin ganin yadda aikin gyaran asibitocin ke tafiya.
Ya kuma bayar da umarnin gina gidajen ma'aikatan dindindin da sauran ma'aikatan lafiya a asibitin haihuwa na Maryam Abacha.
Masar ta hana wadanda ba a yi wa rigakafin korona ba shiga makarantu
Ma'aikatar ilimi ta Masar ta hana malamai da sauran ma'aikata shiga makarantu da jami'o'in kasar idan dai ba a yi mu su cikakken alluran riga-kafi ko gwajin korona ba.
Ministan ilimi na kasar, Tariq Shawqi ya ce tilas ma'aikatan da ba su karbi riga-kafin ba su rika biyan kudin gwaji biyu na cutar a kowane mako kan dala kusan dari daya ga kowane mutum.
Alkaluma daga hukumomin kasar na cewa kashi arba'in cikin dari na malaman makaranta a Masar ba a yi mu su alluran riga-kafin korona ba.
Za a bude makarantun kasar ne nan da mako biyu.
Koriya Ta Arewa ta ce a shirye take ta gyara alaka takwararta ta kudu
'Yar uwar shugaba Kim Jong un na Koriya ta Arewa ta ce kasar a shirye ta ke ta koma teburin tattaunawa da makwabciyarta Koriya ta Kudu idan ba ta takale su ba.
Kalaman Kim Yo-Jong - wadda ke da karfin fada-a-ji - martani ne ga kiraye-kirayen da Koriya ta Kudun ke yi ga Koriya ta Arewa da ta kawo karshen yakin Koriya a hukumance domin samar da zaman lumana a yankin.
Sai dai da farko wani babban ministan Koriya ta Arewan ya yi watsi da kiran, yana cewa lokacin yin haka bai yi ba tukuna.
Wakiliyar BBC ta ce kwatsam a yau Juma'a Kim Yo-Jong ta fitar da wannan sanarwar tana cewa shawara ce mai dadin ji, kuma kasar za ta so a mayar da dangantaka tsakanin makwabtan kasashen.
Tun farkon wannan watan Koriya ta Kudu ta yi gwajin wani roka mai dogon zango daga wani jirgin ruwanta na karkashin ruwa, sa'o'i kadan bayan da Koriya ta Arewa ta yi gwajin nata rokokin guda biyu.
Taliban ta amsa laifin kisan wasu 'yan Afghanistan
Mukaddashin ministan tsaro da Taliban ta nada a Afghanistan ya yarda cewa wasu cikin mayakan kungiyar sun rika kashe 'yan kasar a matsayin mayar da martani duk da cewa kungiyar ta ce ta yi wa kowa afuwa bayan ta kwace mulki a watan jiya.
A cikin wani sakon sauti da ya fitar, Mullah Mohammed Yaqoob ya ce irin wadannan lamuran sun faru ne saboda kiyayya tsakanin wasu 'yan kasar.
Ya kuma yi gargadi cewa babu wani cikin mayakan da ke da ikon taka afuwar ta hanyar yin ramuwar gayya.
Wadannan kalaman na zuwa ne bayan wasu jerin rahotanni da aka fitar bayan an gudanar da binciken kwakwaf da ke cewa 'yan Taliban ta kashe fararen hula da sojojin da su ka mika kansu ga mayakan kungiyar.
Ranar Juma'a wasu rahotannin sun ce an gano wasu gawarwaki da harbin bindiga a lardin Nangahar da ke gabashin kasar.
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta gabatar da sabbin tuhume-tuheme kan Igboho
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta gabatar da sabbin tuhume-tuhume kan mai fafutukar kafa kasar Yarbawan nan da aka kama, wato Sunday Igboho, biyo bayan hukuncin da wata kotun jihar Oyo ta yake na umartar gwamnatin ta biya shi diyyar Naira biliyan 20.
Ministan shari'a na Najeriya ABubakar Malami ne ya fadi hakan yayin wata zantawa da kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN a birnin New York.
Ya ce ''Gwamnatin tarayya na da damar daukaka kara ko ma gabatar da sabbin tuhume-tuhume kan Igboho' inji shi.
Najeriya ta nemi kyautata alakar kasuwanci da Iran
Gwamnatin Najeriya ta nemi zurfafa alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran yayin da Iran din ke duba yiwuwar fara jigila kai tsaye da tashin jiragen sama zuwa Najeriya.
Ministan Harkokin Waje na Najeriya Geoffrey Onyeama ne ya yi wannan roko a ranar Alhamis yayin wata ganawa ta hadin gwiwa da Ministan Harkokin Wajen Iran, Hossein Amir-Abdollahian.
Kamfanin dillacin labarai na Najeriya ya rawaito cewa mutanen biyu sun yi ganawar ne a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana yanzu haka a birnin New York na AMurka.
An kashe DPO yayin rikici da 'yan Okada a Legas
An kashe wani mukaddashin sifritandan dan sanda na Najeriya wato DPO mai suna Kazeem S Abonde yayin arangama tsakanin 'yan sanda da 'yan Okada a yankin Ajao da ke jihar Legas.
Rahoanni sun ce lamarin ya auku ne yayin da ya jagoranci wata tawagar jami'ansa don tarwatsa matukar babura masu kafa biyun da aka fi sa da 'yan Okada da ke tare hanya.
Jaridar Daily Post Nigeria ta ce yayin hargitsin ne jami'ansa suka watse don buya, lamarin da ya sa abokan fadan nasu suka cim ma sa.
An kone motocin 'yan sanda biyu a yayin rikicin.
Kafin rasuwarsa shine DPO din Ajangbadi.
Shugaban Amurka Biden ya nada dan Najeriya mukami
Shugaban Amurka Joe Biden ya sanya wani dan Najeriya John Dabiri cikin masu ba shi shawara kan bunkasa kimiyya da fasaha.
Fadar mulki ta White House ce ta fitar da sanarwar nadin a ranar Laraba.
Dabiri wanda yanzu haka Farfesan Injiniya ne a cibiyar bunkasa fasaha ta Carlifonia dan Najeriya ne da aka haifa a shekarar 1980.
Ya gudanar ba bincike iri-iri da suka sa shi yin fice a Amurka.
Jami'ar jihar Ondo ta hana dalibai sanya matsatstsun kaya
Hukumar gudanarwar jami'ar Adekunle Ajasin ta jihar Ondo, ta sanya dokar hana sanya matsatstsun kayan da basu kamata ba a jami'ar.
An yi tanadin dauar matakin dakatarwa a kan duk dalibin da aka samu da saba wannan doka.
Cikin wata sanarwa da aka raba wa daliban jami'ar mai dauke da kwanan watan 7 ga watan Satumban nan, jami'ar ta nuna damuwa kan yadda ta ce dalibai na yawan yin shigar da bata kamata ba a makaantar.
Sanarwar ta ce bayan zuzzurfan bincike, wannan makaranta ta yanke shawarra cewa daga yanzu za a dakatar da duk wanda aka samu da saba wannan ka'ida tsawon wata guda, farawa daga ranar 25 ga watan Agusta.
Daukacin fasinjojin da ke cikin wani jirgi da ya kife a Rasha sun mutu
Babu wanda ya tsira bayan da wani jirgi da ke dauke da mutane 28 ya yi hadari a gabashin Rasha a ranar Talata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Rasha ya Ambato jami’an ceto na cewa.
Jirgin mai suna Antonov 26 na kan hanyarsa daga babban birnin yankin Petropavlovsk-Kamchatsky zuwa Palana, wani kauye a arewacin tsibirin Kamchatka, lokacin da aka daina jin duriyarsa, in ji ma'aikatar bada agajin gaggawa ta Rasha.
Kamfanin dillacin labaran Rasha na Interfax ya ruwaito cewa ana tunanin jirgin ya fada cikin wani dutse ne a lokacin da yake shirin sauka a cikin wani yanayi na rashin kyawun gani.
Hukumar kula da zirga -zirgar jiragen sama ta kasar Rasha ta tabbatar da cewa an gano inda jirgin ya fadi bayan da ma'aikatar agajin gaggawa ta aike da jirgi mai saukar ungulu tare da tura tawagogi a kasa don nemansa.
Wasu 'yan Najerya a Amurka sun lashi takobin yi wa Buhari zanga-zanga a Majalisar Dinkin Duniya
Wata kungiyar masu fafuukar neman 'yancin kai ta 'yan Najerya mai lakabin NINAS, ta ce babu gudu ba ja da baya, kan shirinta na yin zanga-zanga a shalkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York, yayin da shugaban kasar Muhammadu Buhari zai gabatar da jawabinsa ga jama'ar duniya a ranar Juma'ar nan.
Cikin wata sanarwa da daraktan watsa labaran kungiyar Maxwell Adeleye ya aike wa jaridar The Nations ta Najeriya, ya zargi gwamnatin shugaba Muhamadu Buhari da daukar nauyin wata zanga-zanga a lokacn don yi wa ta su makarkashiya.
Ya yi zargin cewa gwamnatin na hayar bakake 'yan Amurka domin su saje a matsayin 'yan Najeriya don nuna cewa suna tare da shugaba Buhari.
Majalisar Dokokin Birtaniya ta soki matakin gwamnatin kasar na rage tallafin da take ba wa kasashen Afrika
Kwamitin majalisar dokokin Burtaniya da ke bincikar agajin da kasar ke bayar wa ya bayyana rage kudaden da ake kashe wa ga wasu kasashen Afirka da dama a matsayin abin wuce gona da iri.
Kwamitin na raya ƙasashen duniya ya ce ƙasashe da dama na yankin gabashin Afirka da rikicin ya shafa za su ga taimakon agajin su ya ragu da rabi ko sama da haka, duk da cewa an bayyana su a matsayin yankunan da ake ba fifiko.
Gwamnatin Burtaniya ta daura alhakin hakan ga tasirin annobar korona.
Kasashen sun hada da Habasha, Kenya, Sudan ta Kudu, da Mozambique da Somalia.
Kwamitin ya ce ana bukatar taimakon da Burtaniya ke bayarwa a yankin fiye da kowane lokaci yayin da rikice -rikice da matsala sauyin yanayi ke kara karuwa.
An bayyana sunayen wadanda za a aike wa sammaci kan zanga-zangar majalisar dokokin Amurka
A karon farko, tun bayan kwamitin majalisar Amurka da ke gudanar da bincike kan zanga-zangar da aka yi a cikin majalisar a farkon shekarar nan ya fara aiki, ya gabatar da jerin wadanda za a aikawa sammacin gabatar da rahoton farko.
Cikin wadannan mutane da kwamitin ya bukaci su bayyana gaban shi har da shugaban ma'aikatan fadar tsohon shugaban kasar Donald Trump wato Mark Meadows da mai bashi shawara kan sha'anin siyasa, Steve Bannon.
Wakilin BBC ya ce tashin hankalin da ya faru a ranar 6 g watan junairu shi ne irin sa mafi muni a cikin shekaru 200, ya kuma janyo tsaikon sanar da nasarar Joe Biden na sa'o'i da dama.
Shi ma kwamitin majalisar wakilan Amurka da ke bincike kan yunkurin murde sakamakon zaben shugaban kasa na shekarar, da kutsen da magoya bayan Mr Trump suka yi a ginin na Capitol ya yi nisa a nasa aikin.
An dai kama kusan mutane 600 masu alaka da lamarin na watan Junairun shekarar na a lokacin da ake kokarin tabbatar da shugaba Joe Biden a matsayin wanda ya yi nasara a zabe.