Nan da watan Janairu 2022 za a fara amfani da 5G a Najeriya - Pantami

Wannan shafi na kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Imam Saleh and Buhari Muhammad Fagge

  1. An kashe mutane 46 yayin rikici da masu satar shanu a Madagascar

    Makiyaya

    Asalin hoton, Reuters

    Akalla mutane 46 ne aka bada rahoton sun mutu, yayin wata arangamar da mutanen wasu kauyuka suka yi da masu satar shanu a Madagascar.

    An kai harin ne Marovitsika da ke kudancin kasar.

    Bayanai sun ce mahara kusan 120 ne dauke da manyan makamai suka dirar wa jama'a kauyen da na kewayensa.

    Hukumar kare hakkin dan adam ta kasar ta ce za ta kaddamar da bincike mai zaman kansa a kan yadda lamarin ya faru.

    Dama an jima ana samun rikici tsakanin barain shanu da mazauna kauyukan.

  2. Barkanmu da safiya

      • Marubuci, Imam Saleh
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
    Biredi

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Muna kwarya..

    Masu bibiyarmu ta wannan shafi barkanku da safiya da fatan an wayi gari lafiya, daga nan BBC Hausa.

    Muna muku maraba zuwa wannan shafi da muke kawo muku labaran irin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya daban-daban musamman ma Najeriya da Nijar.

    Da fatan za ku kasane da mu tsawon wannan rana.