Nan da watan Janairu 2022 za a fara amfani da 5G a Najeriya - Pantami

Wannan shafi na kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Imam Saleh and Buhari Muhammad Fagge

  1. Nan muka kawo karshen labarai da rahotannin namu sai kuma gobe

  2. Ronaldo ya zama wanda ya fi kowa daukar kudi a kwallon kafa

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan kwallon Manchester United, Cristiano Ronaldo ya karbe mataki na daya daga hannun Lionel Messi a matsayin wanda ke kan gaba a samun kudi a harkar tamaula a duniya, in ji jaridar Fobes mai kididdigar kudi da hada-hada a kasuwancin kwallon kafa.

    Ronaldo mai shekara 36 ya koma Manchester United karo na biyu a bana daga Juventus cikin watan Agusta, bayan shekara 12 da barin Old Trafford.

    Shi kuwa kyaftin din Argentina, Lionel Messi ya bar Barcelona a bana inda ya yi shekara 21, yanzu yana Paris St Germain.

    Dan wasan Portugal din zai samu dala milyan 125 a wannan shekarar yayin da dala milyan 70 za ta shigo masa daga kungiyarsa Manchester United, yayin da zai samu dala miliyan 55 daga harkokin talla.

    Messi ya dawo matsayi na biyu ne bayan abin da zai samu a wannan shekarar yakai dala miliyan 110, inda dala miliyan 75 za ta rika shigar masa daga PSG.

    Neymar zai rika samun dala milayan 95, Kylian Mbappe zai rika samun dala milyan 43 wadanda suke na uku da na hudu.

    Sai Mohamed Salah da zai rika samun miliyan 41 a wannan shekara.

  3. Shugaban Tunisia ya fara samun tirjiya daga makusantansa

    AJ

    Asalin hoton, AJ

    Kakakin majalisar kasar Tunisia ya yi kira ga 'yan kasar da su yi bijirewar lumana ga umarnin shugaban kasar Kais Saied, bayan da ya sanar da zai fadada ikonsa.

    Rached Ghannouchi ya kira shailar da Shugaban ya yi a jiya Laraba koma baya zuwa mulkin kama karya na mutum guda.

    Wannan kokarin na Mista Saied ya biyo bayan dakatar da majalisar kasar da yayi ne a watan Yuli.

    Kuma masu adawa da shi na tuhumarsa da aikata juyin mulki a kasar.

    Sai dai 'yan Tunisia masu yawa na goyon bayan shugaban kasar bayan da su ka ce 'yan siyasar kasar sun gaza tabuka komai.

  4. Afrika ta Kudu za ta hana mazajen da ba a yi wa rigakafi ba kusantar mata

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban da ke lura da tsare-tsare kan kiwon lafiya na wani lardi a Afrika ta Kudu ya bayar da shawarar cewa mata su noke suki kwanciya da mazajensu sai wadanda aka yi wa allurar rigakafi.

    Kafafen yada labarai na kasar sun rawaito cewa mutumin ya ce " Ina ganin shawara ce mai mahimmanci ace, 'in ba a yi allura ba babu saduwa' musamman ga matayen da basu da aure.

    "Hakan zai zama kariya ga bangarori biyun," kamar yadda jaridar The Daily Maverick ta rawaito Nomakhosazana Meth na cewa.

    Wannan kuwa na zuwa ne bayan sakin wani rahoto da ke cewa an fi yiwa mata rigakafin sama da maza.

  5. Nan da watan Janairu 2022 za a fara amfani da 5G a Najeriya - Pantami

    Pantami

    Asalin hoton, Pantami

    Ministan sadarwa da tattalin arzikin Isa Pantami ya ce nan da watan Janairu 2022 za a fara amfani da 5G a Najeriya, wanda hakan zai taimaka wajen sanya idanu kan masu lalata kayan gwanati.

    Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Maiduguri yayin wani taron tattaunawa domin lalubo bakin zaren matsalar masu lalata turakun sadarwa da wutar lantarki.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeria NAN ya ce ma'aikatar yada labarai da al'adu ce ta hada wannan taro wanda kuma gwamnan Borno Babagana Zulum of Borno da mataimakinsa Usman Kadafur da dai sauran masu ruwa da tsaki ne suka halarta.

    Pantami wanda ya samu wakilcin Ubale Maska ya ce kwamitin kolin tarayyar Najeriya ya amince da manhajar 5G wanda kuma hakan zai iya habbaka harkokin sadarwa a kasar.

  6. Aljeriya ta hana jiragen Moroko bin sararin samaniyarta

    Morocco WN

    Asalin hoton, Morocco WN

    Aljeriya ta kulle sararin samaniyarta ga dukkan jiragen saman kasar Moroko, wanda ya kara ta'azzara rikicin diflomasiyyar da ke tsakanin makwabtan biyu.

    Fadar shugaban kasar Aljeriya ta ce ta dauki matakin ne a matsayin wani martani kan takalar fadan da Moroko ke yi.

    A watan jiya Aljeriya ta yanke dukkan dangantakar diflomasiyya da makwabciyar ta ta.

    Sai dai jami'an kasar Moroko sun bayyana matakin da Aljeriyar ke dauka a matsayin maras tushe kuma mai daure kai.

    A kwanan baya Aljeriya ta tuhumi Moroko da goyon bayan wata kungiyar 'yan aware ta kasar, kuma kasashen biyu sun dade suna zaman doya da manja kan makomar yankin Yammacin Sahara - wanda Moroko ke ikirarin mallakarsa.

  7. Turai nason wayoyi su rika amfani da wurin caji daya

    UW

    Asalin hoton, UW

    Majalisar Gudawarwa ta Tarayyar Turai ta sanar da wani shiri na mayar da dukkan na'urorin da ake amfani da su wajen yin cajin na'urorin latironi na hannu su kasance za su iya aiki kan dukkan na'urorin da aka makala su.

    An dai shafe shekara goma ke nan ana kokarin samar da wannan tsarin.

    Babban Kwamishinan da ke kula da Majalisar, Thierry Breton ya ce sabuwar dokar ba za ta hana sabbin dabarun kere-kere ba kamar yadda wasu kamfanoni ke fargaba, idan dai na'urorin za su samar da wurin makala ta samfurin USB-C a jikin wayar hannu ko dukkan wata na'ura ta hannu.

    UW

    Asalin hoton, UW

    Ya ce samar da cajar da za ta yi aiki a kan dukkan na'urorin hannu na da fa'idodji masu yawa.

    Ya ce wannan shawara ce da za ta kawo sauyi mai ma'ana, wadda da fari za ta biya bukatun masu amfani da kayayyakin latironi, sannan hanyar kara fadada kwarewa ce ga kamfanonin da ke kera kaya kamar wayoyin hannu da na komfuta, kuma za ta kasance ta bai daya bisa tsarin da Tarayyar Turai ke bukata.

  8. Ba na jin tafiyarmu za ta yi daidai da Biden - Erdoğan

    BBC

    Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan, ya ce ba ya zaton tafiyarsa da shugaban Amurka Joe Biden za ta zo daya.

    Erdogan ya bayyana haka ne a New York da ke Amurka inda aka gudanar da babban taron Majalisar Dinkin Duniya.

    Shugaban ya ce "an yi rashin sa a ba mu cimma wani abin azo a gani ba ta bangaren alakar diflomasiyya da Amurka.

    "Na yi aiki sosai da dan gidan Bush na yi da Obama na kuma yi da Trump amma ba na jin hakan zai yiwu da Biden," in ji Erdogan.

    "Ya kamata su sani cewa ba irin tsohuwar Turkiyyar da suka sani ba ce a baya. Wannan Turkiyyar ta daban ce.

    "A bangaren tsaro kuma mun samu habbaka, za kuma mu kara ci gaba," in ji shugaban.

  9. An gano kashin wani jegare da yakai shekara miliyan 165 a Moroko

    BBC

    Masana kimiyya a Landan sun ce kashin da aka samu a Moroka na hakarkarin wata dabba ne da ake kira (jegari) ko kuma (karza), wanda shi ne mafi dadewa da aka taba samu ya zuwa yanzu a duniya.

    Tawagar masana kimiyyar da ke gidan tarihi na Natural History Museum da ke Landan an yi amannar ya kwashe sama da shekara miliyan 160 a cikin kasa.

    Kuma irin shi ne na farko da aka fara samu a Afrika.

    Masu bincike a gidan tarihin sunce wannan kashi bako ne a wajensu.

    AP

    Asalin hoton, AP

  10. Save the Children ta zargi manyan kasashe da watsi da yaran da ke cikin tsananin rayuwa

    Yaran Afrika

    Asalin hoton, Google

    Fitacciyar kungiyar bayar da agaji ta Save the Children ta soki kasashe masu arziki da yin watsi da yaran da ke rayuwa cikin mawuyacin hali a sansanin da aka kafa domin kula da 'ya'yan mayakan kungiyar IS.

    Wani rahoto da kungiyar ta fitar na cewa Birtaniya da Faransa ba su da tsari mai kyau na mayar da yaran kasashensu duk da cewa 'yan kasa ne.

    Kungiyar ta kuma ce yaran da ake tsare da su a sansanin al-Hul na fuskantar rashin abinci mai gina jiki da rashin yanayi mai tsafta da tashin hankali baya ga hatsarin tashin gobara a cikin sansanin mai dubban tantuna.

    Rahotanni na cewa Fiye da yara 60 sun mutu cikin wannan shekarar kawai a sansanin al-Hul da kuma wani sansanin mai suna Raj.

  11. An kama 'yan bindigar da ake zargi da sace daliban Kaduna

    Yan bindiga

    Asalin hoton, ,

    Rahotani daga Najeriya na cewa 'yan sanda sun kama 3 daga cikin barayin da suka sace daliban makarantar Bethel Bepist da ke jihar Kaduna a kwanakin baya

    An yi holen yan bindigar sanye da kayan sojoji a shalkwatar rundunar yan sandan Najeriya da ke Abuja.

    Yayin holen sun ce sun sace daliban ne saboda yadda suka shiga halin rashin kudi.

    A yanzu za a gabatar da su a kotu, wadda za ta tabbatar da zargin da 'yan sandan Najeriyar ke musu ko kuma ta wanke su.

  12. Ana zargin gwamnatin Sudan Ta Kudu da yin bushasha da dukiyar 'yan kasa

    Sudan ta kudu

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani kwamitin kwararru na Majalisar Dinkin Duniya ya ce 'yan siyasa da 'yan kasuwa a Sudan Ta Kudu, sun jima suna bushasha da dukiyar kasar.

    Kwamitin, wanda ke zaman na kare hakkin dan adam a Sudan T Kudun ya ce ya samu kwararan shaidu da ke nuna yadda wasu 'yan siyasa da makusantan gwamnati suka kasafta miliyoyin daloli a tsakaninsu tun daga shekarar 2018.

    Rahoton ya ce yawan kudaden da aka sacen ya kai dala miliyan 73.

  13. Ana neman kasashe su rage kashe kudi saboda bashin da annobar korona ta jibga musu

    Duniya

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani sabon bincike na yin gargadi cewa tilas fiye da kasashe dari su rage yawan kudaden da suke kashewa na samar da kayayyakin more rayuwa -- misali kiwon lafiya da ilimi -- a dalilin dumbin bashin da annobar korona ta jibga musu.

    Masu binciken a Amurka na cewa annobar ta mayar da babbar matsala ta zama gagaruma.

    Sun bayar da misalin kasar Zambia, wadda a yanzu ke kashe rabin dukkan kudaden shigarta wajen biyan basussuka -- lamarin da zai yi illa matukaga yawan kudaden da za su kashe kan kulawa da bukatun jama'ar kasar.

    Binciken da kungiyar Pathfinders for Peaceful, Just and Inclusive Societies ta gudanar ya kara gargadi cewa karuwar nauyin bashi zai kara fadada wagegen gibin da ke tsakanin kasashe masu arziki da marasa galihu.

  14. Amnesty ta zargi shugaban Gambia da gaza kare 'yancin 'yan jarida

    Adama Barrow

    Asalin hoton, Reuters

    Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta zargi shugaban kasar Gambiya Adama Barrow da gaza soke dokokin danniya da ke tauye 'yancin aikin jarida a kasar.

    Kungiyar ta ce an samu rahotannin take hakkin 'yan jarida fiye da 15 a cikin shekaru hudu da suka gabata, a cewar rahoton da ta fitar ranar Laraba.

    Shugaba Barrow ya hau kan karagar mulki a shekarar 2017 bayan alkawarin yakin neman zabe na gyara kura -kuran da ya gada a wajen wanda ya gada Yahya Jammeh.

    To sai dai Amma Amnesty ta ce ba a yi wa dokokin da ke tauye hakkin dan adam ba sauyi ba, ciki har da 'yancin fadin albarkacin baki da yin taro cikin lumana.

  15. Shugaban Brazil zai killace kansa bayan dawowa daga taron MDD

    Bulsunaro

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Brazil Jair Bolsonaro, ya ce zai killace kan shi tsawon kwanaki biyar bayan dawowa daga babban taron majalisar dnkin duniya a birnin New York na Amurka.

    Ministan lafiyar kasar Marcelo Queiroga, ya kamu da cutar korona, an kuma tilasta ma sa zama a wani Otal da ke New York domin karbar magani.

    Wasu karin mutum 50 daga cikin tawagar da Mr Bolsonaro ya je da ita Amurka, za su killace kansu har zuwa ranar Lahadi mai zuwa.

    Sai dai tun da fari hukumar lafiyar Brazil, ta ba da shawarar shugaban da tawagarsa su killace kai na makwanni biyu.

    Sai dai Mista Bolsonaru ya ce bai yi rigakafin korona ba, amma saboda ta taba kama shi a yanzu jikinsa ya na da kariya.

    Ofishin shugaan ya ce za a dinga yi masa gwaji kowacce rana, ba zai killace kan shi ba har sai gwaji ya nuna ya kamu da cutar.

  16. 'Yan Mali sun fito zang-zangar neman kasarsu ta kulla kawance da Rasha

    Mali

    Asalin hoton, Reuters

    Dubban al'ummar Rasha sun fito kan tituna suna zanga-zagar neman gwamnatin kasar ta kulla kawance da Rasha.

    Matakin ya biyo bayan wata sanarwa da gwamnatin soji ta riko ta fitar, inda ta ce an fara tattaunawa da rundunar sojin haya ta Rasha, da ake kira Wagner don yaki da ta'addanci a kasar.

    Hakan na nufin cewa zanga zangar ta goyon bayan gwamnatin kasar ce.

    Sojojin da ke rike da mulki a Malin dai na takun saka da Faransa wadda a baya ita ce uwar gijiyar kasar, saboda kafewar da ta yi kan lallai a gudanar da sabon zabe.

  17. IPOB ta yi barazanar tursasa wa jama'a yin zaman dirshan a gida tsawon wata guda

    Nnamdi Kanu

    Kungiyar IPOB mai fafutukar kasa kasar Biafra, ta yi barazanar tursasawa jama'ar yankin kudancin Najeriya yin zaman dirshan har tsawon wata guda a gida, don nuna adawa da jinkirta shari'ar jagoranta Nnamdi Kanu.

    IPOB ta ce dokar ta ta za ta fara aiki ne da zarar hukumar tsaron farkin kaya ta Najeriya DSS ta gaza gabatar da Mista Kanu a gaban kotu, ranar 21 ga wata mai zuwa, lokacin da za a ci gaba da shari'arsa.

    Kakakin IPOB Emma Powerful ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da jaridar This Day Nigeria ta rawaito.

    Ya ce kungiyarsu ta samu bayanai daga wata majiya, da ke nuna cewa DSS za ta ki gabatar da Kanu a wannan rana, da manufar ci gaba da uzzura masa.

  18. Za a dawo da kallon fim a Mogadisu bayan shafe shekaru 30

    Mogadishu

    Asalin hoton, Reuters

    An fara tantance masu kallon fim na farko cikin shekaru 30 a babban birnin Somalia Mogadishu, amma cike da matakan tsaro.

    Wannan lamari ya sanya kwarin gwiwa a zukatan 'yan kasar, musamman ta fukar farfado da al'adu a kasar da ke fama da masu a'awar kishin Islama.

    Wakilin BBC ya ce ana wannan tantancewa ne a wani dandali, wanda sojoji sukai amfani da shi a matsayin sansani a lokacin yakin basasar kasar, bayan haramta zuwa Silima.

    A shekarar 2012 aka sake bude shi, amma al-Shabab da ke kallon duk wani abu na walwala da nishadi a matsayin sabon ubangiji suka tashi dandalin da ababen fashewa.

    'Yan kallo dai sun kalli fina-finai biyu cikin walwala da nishadi wanda mai shirya fina-finan kasar Ibrahim CM ya jagoranta.

  19. Birtaniya ta ja hankalin duniya game da matsalar sauyin yanayi

    Boris Johnson

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Birtaniya Boris Johnson, ya yi gargadin cewa taron da za a yi a kan sauyin yanayi na watan Nuwamba mai zuwa a Scotland wata gaba ce mai muhimmanci game da makomar dan adam.

    A jawabin da ya gabatar a taron Majalisar Dinkin Duniya, Mr Johnson ya yi kira ga kasashen duniya su yi kokarin rage gurbataccen hayakin da suke fitarwa nan da shekarar 2030.

    Ya ce a wannan gabar ina gayyatarku, ina gayyatar taron MDD a watan Nuwamba, ku zo mu hada karfi da karfe, mu dauki mataki, ina fatan wannan zai kawo sauyi a duniya, yadda za mu yi shagalin hure kyandir din bude sabon babi a duniya.

    Ya kuma yi kira ga kasashe masu arziki musamman China, ta rage amfani da makamashin kwal, sannan kasashe da suka ci gaba masu arziki su ba da tallafin kudaden magance matsalar da sauyin yanayi ke haddasawa.

  20. Aljeriya ta hana jiragen Morocco shawagi a sararin samaniyarta

    Abdelmadjid Tebboune.

    Asalin hoton, Gett

    Kasar Aljeriya ta haramta wa jiragen samarn Morocco shawagi a sararin samaniyarta.

    Matakin na zuwa ne yayin da dangantaka ke kara tsamani a tsakanin kasashen biyu.

    Wata guda da ya gabata ne Aljeriyan ta sanar da katse huldar diflomasiyya tsakaninta da makociyar ta ta Morocco.

    Rahotanni sun ce an amince da wannan sabon mataki na yanzu ne bayan wani taron majalisar tsaron kasar wanda shugaba Abdelmadjid Tebboune ya jagoranta.