Bissalam
Da haka zamu dakata a wannan shafin sai kuma gobe idan Allah ya kai mu. Umaymah Sani Abdulmumin ke muku fatan alheri.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya
Imam Saleh and Umaymah Sani Abdulmumin
Da haka zamu dakata a wannan shafin sai kuma gobe idan Allah ya kai mu. Umaymah Sani Abdulmumin ke muku fatan alheri.
A yayin jawabinsa na farko a gaban babban zauren majalisar dinkin duniya, Shugaban Amurka Joe Biden ya yi alkawarin kafa wata sabuwar alkibla a dangantakar diflomasiyya bayan ficewar kasarsa daga Afghanistan.
Mista Biden ya shaida wa taron shugabannin kasashen duniya a birnin New York cewa amfani da karfin soji kawai ba zai warware yawancin rikice-rikicen da ke damun duniya ba, musamman matsaloli kamar dumamar yanayi da annobar korona.
Shugaban ya yi hannun riga da wanda ya gada - wato tsohon shugaba Donald Trump wanda ya ce muradun Amurka ne kawai su ka dame shi.
Sai dai a wani shagube da yayi kan China, Mista Biden ya ce Amurka ba za ta so dangantaka tsakanin kasashen biyu ta kara yin tsami ba.
Amma ya ce Amurka za ta yi gasa da dukkan kasashe kuma za ta yi jagoranci bisa abubuwan da ta yi imani za su kawo wa duiya ci gaba.
Sai dai kuma shugaban ya ce zai sake nanata cewa - ba sa fatan ganin an dawo da yakin cacar baka, ko raba kawunan kasashen duniya gida-gida.
Iran ta ce za ta cigaba da tattaunawa da kasashen ketare kan shirinta na mallakar makamashin nukiliya cikin makonni masu zuwa.
An fara tattaunawa kan farfado da yarjejeniyar da aka kulla a birnin Vienna a shekarar 2015 kan sa ido akan shirin na Iran, sai dai ana fuskantar cikas na tsawon watanni.
Yarjejeniyar na daf da rugujewa tun bayan da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da ita, kana ya sake kakaba wa Iran wasu jerin takunkumai na karya tattalin arziki.
A martanin da ita kuma ta mayar, Iran ta rika taka wasu daga cikin tanade-tanaden yarjejeniyar.
Kusan mutum 500,000 ambaliya ta shafa a yankunan jihohi shida na Sudan ta Kudu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Jihohin da abin ya shafa sun hada da Jonglei a gabashin kasar, Yammacin Equatoria, Warrap, arewacin Bahr El- Ghazal, da jihohi biyu da ke kan gaba wajen samar da mai da yankin arewaci kusa da Nilu.
A cewar Majalisar wadanda ambaliyar ta shafa na neman bukatar agajin gaggawa na matsuguni da magunguna da abinci.
Sannan an yi hasashen cewa za a tafka ruwa da ambaliya a cikin 'yan watanni da ke tafe.
Wani bincike ya nuna cewa ƴan Najeriya na cikin waɗanda suka fi fama da ciwon mantuwa a duniya.
Ciwon mantuwa da ake kira 'dementia' na ɗaya daga cikin cututukan da ke barazana ga lafiyar bil'adama.
Kungiyar da ta gudanar da binciken mai sunaAlzheimer's Disease Internationalta ce sama da mutum miliyan 40 ke fama da cutar a duniya ba tare da sun sani ba.
Binciken ya kiyasta cewa kashi 75 cikin 100 na ɗauke da cutar ba tare da sun sani ba, kuma wadanan alkaluma sun fi yawa a kasashen Najeriya da Indiya da kashi 90 cikin 100.
Rahoton ya ƙunshi kundin nazari daga manyan masana 50 a faɗin duniya game da cutar.
Shugabar kungiyar, Paolo Barbarino ta ce tsangwama da rashin wayewa da rashin bincike sun taka rawa wajen samun karuwar masu ɗauke da cutar.
Hukumar Lafiya ta WHO ta kiyasta cewa adadin mutanen da ke dauke da cutar a duniya za su haura miliyan 130 kafin shekara ta 2050.
Tsohon Sarkin Kano kuma shugaban mabiya Tijjaniya a Najeriya, Muhammadu Sanusi II, ya ja hankalin 'yan kasar kan cin mutunci shugabanni saboda hali na tsananin rayuwa da suke ciki a kasar.
A lokacin jawabi zuwa ga mabiya daga jihohi bakwai a arewa maso yammacin Najeriya, a Sokoto, Sunusi ya nuna cewa yana da yakinin wata rana komai zai sauya don ci gaba.
Sanusi ya kuma nemi hadin-kan al'ummar Musulmi da kuma shawartar kungiyoyin Musulmi domin gina makarantu da bijiro da tsare-tsaren karfafa gwiwa don dogaro da kai.
Sannan ya jadada da yin tuni cewa addinin Musulunci bai yarda da barace-barace ba, da kaucewa duk wasu ayyukan da zai jefa mutum cikin hadari.
Tsohon Sarkin ya kuma yi kira ga mutane da su kasance masu ibada bisa dacewa da dokokin Musulunci.
Gwamna Babagana Zulum ya dakatar da shugabannin gudanarwar kwalajen fasaha na Ramat Polytechinc a Maiduguri, na tsawon wata shida.
Zulum ya kasance dalibi a kwalajen tsakanin 1986 zuwa 1988.
A lokacin wata ziyarar bazata, gwamnan ya kadu da ganin ɓangarori da dama na kwalajen a lalace, kusan makarantar ta mutu murus.
Gwamnan ya ziyarci makarantar da misalin 9 na safe kuma ya tarar da dakunan gwaje-gwajen dalibai ba sa aiki, duk azuzuwa sun yi yana.
Zulum ya umarci kwamishinan ilimi, Dr Babagana Mallumbe ya karɓe ragamar gudanar da makarantar.
Gwamnan ya yi tattaunawar sirri da manyan shugabannin makarantar.
'Yan Najeriya da dama na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan wani bincike da BBC Hausa ta gudanar da ya gano cewa gwamnatocin Najeriya na baya da na yanzu ba su yi komai a kan aikin wutar Mambila da suka yi ta ikirari ba.
Bincike da BBC Hausa ta gudanar ya bankado cewa ba a yi komai ba a wurin da aka ware domin aikin tashar samar da wutar lantarki ta Mambila da ke jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya shekara 40 da fara maganar aikin.
Tun a shekarar 1982 ne lokacin mulkin tsohon shugaban Najeriya Shehu Shagari aka fara maganar tashar wutar wacce a lokacin aka tsara za ta samar da wuta megawat 2,600.
Gwamnatoci da suka shude sun sake fasalta aikin wutar inda a shekarar 2012 karkashin Shugaba Goodluck Jonathan aka kara yawan megawat da tashar za ta samar zuwa 3050.
Shugaba Muhammadu Buhari ma a lokacin yakin neman zabensa ya yi ta nanata cewa zai kammala aikin wutar ta Mambila idan ya zama shugaban kasa, kuma a shekarar 2017 wasu magoya bayan gwamnatinsa sun yi ta yada wasu hotuna da ke cewa na aikin wutar ne.
Bayan sakin rahoton na BBC dai 'yan Najeriya wadanda a baya suka saka rai da cewa wannan gwamnatin za ta share musu hawaye wajen tabbatar da kammaluwar aikin wutar Mambila, sun yi ca da bayyana ra'ayoyinsu kan abin da binciken ya bankado.
Wasu ma hakuri suka dinga bayarwa da neman afuwa kan yada wasu hotuna da suka yi a baya, da ke ikirarin cewa ci gaban da ake yi na aikin wutar ne.
Me ake cewa a shafukan sada zumunta na BBC Hausa?
Masu shigar da kara a Birtaniya sun amince za a gurfanar da wani dan kasar Rasha na uku a kotu kan tuhumar kai hari da guba wanda ya kusa halaka wani tsohon ma'aikacin leken asiri na rasha a garin salisbury da ke kudancin Ingila a shekara 2018.
'Yan sandan kasar sun ce mutumin mai suna Denis Sergeev na rike da mukamin manjo-janar ne a wani sashe na rundunar leken asiri ta Rasha, wato GRU.
Sun kuma bayyana sunayen wasu jami'an leken asiri biyu na GRU din (Anatoliy Chepiga da Alexander Mishkin), wadanda su ka shafa gubar novichok a kofar shiga gidan mutumin da su ka so kashe wa wato Sergei Skripal.
Wani dan sanda ne ya gano Mista Skripal da 'yar sa Yulia a sume a kan wani benci a wani wurin shakatawa, kuma daga baya sun shiga wani matsanancin mawuyacin hali.
Sai dai ba za a iya gabatar da Rashawan a kotu ba har sai an kamo su, matakin da Rasha ta ki dauka kuma ta musanta cewa jami'an nata na da hannu a kokarin kashe mutumin.
Gwamantin jihar Kano ta haramata shiryawa da nuna fina-finan kwacen wayar salula, da shaye-shayen miyagun kwayoyi da garkuwa da mutane.
Shugaban hukumar tace fina-finan a Kano, Isma’ila Na’abba Afakallah ya shaida wa BBC cewa irin wadannan fina-finai na gurbata tarbiyar wadanda ke kallon su.
Afakallah ya ce kamata ya yi masu shirya fina-finan na Kanyywood su mayar da hankalinsu kan fina-finan da suka shafi rayuwar al’umma da bunkasa al’adun Hausawa da ci gaban matasa.
Ga ƙarin bayanin da ya yi wa wakilin BBC Khalifa Shehu Dokaji.
'Yan sanda a Malaysia na neman a mayar da wata mata 'yar kasar daga Thailand wadda ta sauya jinsinta daga namiji zuwa mace saboda aikata laifi karkashin dokokin kasar na Musulunci.
Matar mai suna Nur Sajat Kamaruzzaman, ta ki bayyana a gaban wata kotu a watan janair domin amsa tambayoyi na cin mutuncin addinin Islama bayan da ta sanya kayan mata irin wanda matan Malaysia ke sanyawa yayin wani bikin addini da ta halarta.
Idan aka same ta da laifi, za a iya daure ta har na tsawon shekara uku a kurkuku.
Wannan shari'ar ta kasance manuniya kan tsarin shari'ar kasar Malaysia mai rassa biyu - na Musulunci da wanda ta gada daga 'yan mulkin mallaka.
Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya tare da hadin gwiwa da kungiyar tarayyar Turai ya gano cewa fiye da yara dubu dari uku ne aka kashe a shiyyar arewa maso gabashin kasar, a yakin da ake gwabzawa da `yan boko haram.
Kazalika binciken ya ce fiye da yara dubu biyar na fama da matsaloli daban-daban da suka shafi kwakwalwa, sakamakon rikicin.
Sun fitar da wadannan bayanai da alkaluma ne a cikin wata sanarwa da masu magana da yawunsu a Najeriya, wato Falashade Adebayo da Modestus Chukwulaka suka rattaba mata hannu.
Sanarwar ta bayyana cewa fiye da yara dubu dari uku ne aka kashe a shiyyar arewa maso gabashin kasar, a yakin da ake gwabzawa da `yan boko haram a cikin shekaru goma sha biyu da suka wuce.
Har wa yau sanarwar ta ce rikicin ya dai-daita ko kuma raba mutum fiye da miliyan daya da gidajensu a shiyyar.
Wata illar da rikicin ya yi wa kananan yara, kamar yadda sanarwar ke cewa ita ce yadda lamarin ya haddasa wa yara fiye da dubu biyar da rikicin ya tilasta musu barin makaranta matsalolin da suka shafi kwakwalwa, kama daga yawan jin takaici da tsarguwa ko firgici da yawan fada ko zafin-rai da sauran matsaloli dangoginsu.
Firaministan Pakistan Imran Khan ya shaida wa BBC cewa gwamnatinsa ba za ta amince da sabuwar gwamnatin da Taliban ta kafa a Afghanistan ba har sai ta rungumi dukkan 'yan kasar, kuma tana kare hakkin dan Adam kana ba ta bari ana amfani da kasar a matsayar wata matattarar 'yan ta'adda ba.
Ya ce za su dauki wannan matakin ne tare da makwabtansu na yankin kamar Iran da Uzbekistan da Tajikistan.
Kungiyoyin kare hakin dan Adam sun bayyana damuwarsu kan rashin shigar da mata cikin gwamnatin kasar bay ga hana 'yan mata da malamai mata halartar makarantun sakandare.
Mista Khan ya ce matakin hana mata samun ilimi ba daga adinin Musulunci aka samo shi ba.
Firaminista Imran Khan ke nan ke cewa:
Matan kasar na da karfin gwuiwa matuka. Ina ganin idan aka ba su lokaci za su tabbatar da an ba su hakkokinsu, kamar shekara daya zuwa biyu zuwa uku.
A halin yanzu ba za a iya cewa komai ba saboda watan farko ke nan na sabuwar gwamnatin bayan an shafe shekara ashirin ana yakin basasa a kasar.
Tun bayan fitar da rahoton na BBC yan Najeriya da kuma masu ruwa da tsaki ke martani a kai.
A martanin dan majalisa mai wakiltar Taraba Ta Tsakiya Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, ya ce aikin tashar wutar Mambila ba karamin aiki ba ne.
Ya ce a saninsa "an bai wa gwamnatin jihar Taraba naira biliyan daya na safiyo don kayyade girman tabkin amma har yanzu ba ta gama aikinta ba."
To amma a cewarsa a ganinsu bai kamata ba a ce gwamnatin tarayya ta bai wa gwamnatin jiha irin wadannan kudade da sunan safiyo ba.
An dade ana ta maganganu daban-daban da zargin jan kafa wurin aikin tashar Mambila, da kuma son sanin inda aka kwana wajen aiwatar da aikin da ake sa ran zai samar wa Najeriya isasshiyar wutar lantarki.
Ko da a shekarar 2020 ma a wata hira da BBC, tsohon ministan wutar lantarki Injiya Saleh Mamman ya ce akwai tatsuniya kan batun wutar ta Mambila.
Idan har aikin ya kammala tashar za ta kasance mafi girma a Najeriya kuma daya daga cikin manyan tashoshin wuta a nahiyar Afirka.
Najeriya na samar da megawat na wuta tsakanin 5,000 zuwa 5400 a lokaci da dukkan tashoshin samar da wuta na kasar ke cikakken aiki.
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati EFCC shiyyar jihar Kwara, ta ce ta cafke wasu dalibai 30 saboda zargin damfara ta intanet a jami’ar jihar Kwara,
Mai magana da yawun EFCC, Mista Wilson Uwujaren ya fada a cikin wata sanarwa a ranar Litinin cewa an kama wadanda ake zargin ne bayan wani rahoton sirri kan zarginsu da hannu a zamba ta yanar gizo.
Ya ce bayan samun bayanan abun da suke aikatawa ne jami'an hukumar suka dira a wasu dakunan kwanan dalibai tare da yin bincike, lokacin ne aka kama wadanda ake zargin.
Jam'iyyar Liberal da firaiministan Canada Justin Trudeau ke jagoranta ta yi nasara a zaben da aka yi a jiya Litinin wanda jam'iyyun siyasa 6 suka fafata.
An ci gaba da kidaya kuri'un da aka kada, sai dai an yi hasashen Mista Trudeau zai rasa rinjaye a majalisar dokoki, wanda daman makasudin sanya zaben na katsahan shi ne samun rinjaye a majalisar.
A shekarar 2019 ne jam'iyyar Liberal ta rasa rinjaye a majalisar a lokacin da aka yi zabe. a bangare guda kuma jam'iyyar Conservative ta 'yan adawa da Erin O'Tooleke jagoranta, ba ta samu wani tagomashi ba.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi 'yan Taliban da keta hakkin dan adam tun bayan karbe iko da Afghanistan a watan da ya wuce.
Wannan na kunshe cikin rahoton da Amnesty ta fitar, ta ce wasu kungiyoyi biyu sun ce Taliban ta fara nun a halin ta ne jim kadan bayan kama ikon kasar.
Wakilin BBC ya ce yawancin cin zarafin an tattare su, sannan Taliban ta lalata ayyukan da ka yi na shekaru 20.
Sannan Amnesty ta zargi dakarun Taliban da kashe farar hula da hana shigar da kayan agaji, da takaitawa jama'a 'yanci musamman mata.
Har wa yau, rahoton ya ce ana kai hari ga masu rajin kare hakkin dan adam, da 'yan jarida da masu zanga-zanga da sauransu.
Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, ya ce idan ba a bar yankin kudu ya samar da shugaban kasa a 2023 ba, jam'iyyar APC za ta zama jam'iyyar siyasa ta arewa.
Ya kuma kalubalanci yankin kudu maso gabas da su gabatar da kwakkwaran dalilin da zai sa a amince dan kabilar Igbo ya zama shugaban kasa na gaba.
Jaridar Daily Trust ta rawaito shi yana faɗar hakan a wani taro mai taken “Tattaunawa da Owelle Rochas Okorocha a bikin cikarsa shekaru 59 ’, wanda ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya, reshen babban birnin kasa Abuja ta shirya.
“Ina goyon bayan gwamnonin kudu kan batun mayar da kujerar shugaban kasa yankin Kudu., mun fara da Kudu maso Yamma lokacin Shugaba Olusegun Obasanjo, ya zama shugaban kasa. Sannan mun koma Arewa lokacin muna da Yar’Adua. Kudanci kuma tare da Goodluck Jonathan, kuma yanzu Arewa ce ke da shugaba mai ci'' inji shi.
"Don haka, me yasa za a canza wannan tsarin yayin da ya kamata mulki ya koma kudu? Abu ne mai kyau a ci gaba da tafiya yadda ake yi.
Idan ba a yi hakan ba, to APC ta zama jam'iyyar arewa, "in ji shi.
Okorocha ya kuma yi kira da a rika sanya mata a al'amuran jagoranci don ba wa kowa hakkinsa.
Sabuwar girgizar kasa ta afka wa tsiburin La Palma na kasar Sifaniya, kwanaki biyu da fuskantar amon wuta a wasu yankunan kasar.
Cibiyar bincike ta kasar ta ce karfin girgizar kasar ya kai maki 3 da digo 8, an kuma ji karfinta har a tsuburin Canarie duk da nian da ke tsakaninsa da inda lamarin ya faru.
Wannan sabon bayani ya sanya hukumomi gaggauta kwashe dubban mazauna yankin da dutsen Cumbre Vieja yake.
Yayin da toka ke ci gaba da zubowa, jami’an yankin sun ce wannan ka iya haddasa fashewar sundukan iskar gas idan ta isa teku.
Rahotanni daga Burundi na cewa akalla mutane 3 aka kasha, wasu gwammai suka jikkata, a hare-haren da aka kai da ababen fashewa a babban birnin kasuwancin kasar Bujumbura.
Ganau sun ce akalla gurneti biyu ne suka tashi a wata tashar motar Bus, lamarin da ya janyo mutane suka firgita.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan wani mummunan hari da aka kai birnin Gitega da wani harin da aka kai da mota a filin jirgin sama na Bujunbura a ranar Asabar, wanda ‘yan tawayen kungiyar RED-Tabara suka dauki alhakin kai shi.