Buhari ya ce ƴan Najeriya miliyan 8 ke amfana da tallafinsa

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sassan duniya kai-tsaye

Rahoto kai-tsaye

Imam Saleh and Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Amurka ta nemi sulhu da Koriya Ta Arewa kwana guda bayan ta harba makami cin nisan zango

    Kim Jong Un

    Asalin hoton, Reuters

    Wakilin shugaba Biden a Koriya ta Arewa ya ce kofa a bude ta ke domin tattaunawa, kwana guda bayan kasar ta yi nasarar gwajin makami mai linzami mai cin dogon zango.

    Sung Kim na magana ne a wani taro da aka yi a birnin Tokyo na Japan, tare da manyan jami'an gwamnatin Japan da kuma Koriya ta Kudu.

    Mista Kim ya ce ya na son bayyanawa karara cewa Amurka ba ta da niyyar tsaurarawa Koriya ta Arewa.

    Wakilai uku na tattaunawa kan hanyar da za su karfafawa Pyongyang gwiwar komawa teburin sulhu, ana kuma sa ran za su yi wa Arewar tayin kayan agaji a daidai lokacin da ta ke fama da matsin tattalin arziki da karancin abinci.

  2. Barka da zuwa

    Shayi

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Bismillanku fa

    Jama'a barkanmu da safiya, da fatan an wayi gari lafiya.

    Barka da zuwa wannan shafi da muke kawo muku labaran irin abubuwan da ke faruwa a sassa daban daban na duniya musamman ma kasashen Najeriya da Nijar, Kamaru da Chadi.

    Nine Imam Saleh daga nan sashen Hausa na BBC da zan jagoranci kawo muku labaran a wannan lokaci.

    Da fatan za ku kasance da mu.