Abin da jaridun Iran ke cewa kan harin 9/11
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Awwal Ahmad Janyau and Buhari Muhammad Fagge
Yadda mahaifiyar Ronaldo ta barke da kuka da ya ci kwallon farko Manchester

Asalin hoton, Twitter
Mahaifiyar dan wasan Manchester United Cristiano Ronaldo ta barke da kuka bayan da dan nata ya jefa kwallon farko a wasansa na farko tun dawowarsa United.
Dan wasan mai shekara 36 ya ci wa Manchester United kwallo biyu a wasan da ta ci 4-1 tsakaninta da Newcastle United.
Lingard da Bruno ne suka zura sauran kwallayen biyu, wanda hakan ya bai wa United din damar zama ta daya a kan teburi bayan gama wasan.
Komawar Ronaldo Manchester United ta matukar karawa kungiyar kwarin gwiwa a tseren da ake yi na ganin wanda zai lashe Premier.
Abin da shugabannin duniya ke cewa kan harin 11 ga watan Satumba

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Joe Biden da matarsa Jill Biden sun isa birnin New York domin bikin cika shekara 20 da kai harin ranar 11 ga watan Satumba.
Ya samu rakiyar tsohon shugaban kasar Barack Obama da Bill Clinton da wasu shahararrun shugabanni a kasar.
Domin tunawa da wannan harin na ta'addanci da aka kai shekara 20 baya, an yi shiru a karon farko saboda harin da aka kai ginin arewaci sai kuma wanda aka kai ginin Kudanci.
An kuma yi shiru a daidai lokacin da aka kai harin na 2001 a daidai kuma ginin. An kuma tuno da mutanen da aka rasa a wannan rana a yayin bikin.

Asalin hoton, Getty Images
Mataimakiyar shugaban kasar Kamala Harris ta nemi kowa ya nuna sadaukarwa ga mutanen.
Shugaba George W Bush ya ce rayuwar mutanen Amurka ta sauya bayan kai wannan mummunan hari.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa "Ba zamu taba mantawa ba. Za mu ci gaba da yaki a kullum domin samun 'yanci.
Firaministan Australia Scott Morrison ya rubuta doguwar makala a kan harin.
Ya rubuta cewa " Duk da radadadin da muke ji a wannan rana, 'yan ta'adda ba su cimma abin da suke so ba na sauya rayuwarmu. Harin 11 ga watan Satumba na tuna mana cewa yancinmu mai rauni ne."
A karon farko Arsenal ta ci wasa a Premier a bana

Asalin hoton, Getty Images
Hankalin kocin Arsenal Mikel Arteta ya kwanta, bayan da kungiyar ta samu makinta na farko a gasar Premier ta bana a kan kungiyar Norwich a filin wasa na Emirates.
Arteta ya fada tsaka mai wuya ne bayan da kungiyarsa ta fara gasar bana da kafar hagu, inda kafin a tafi hutun wasanni yake a matsayi na karshe.
Pierre-Emerick Aubameyang ya ci kwallo daya tilo da suka sha da ita a minti na 66, bayan da Nicolas Pepe ya buga wata kwallo ta daki turke.
Hankalin Arsenal ya tashi bayan da alkalin wasan Michael Oliver ya sai ya duba na'urar da ke taimaka masa kafin ya bayar da kwallon, bayar da kwallon ya samar da kwanciyar hankali a filin wasa na Emirate.
Su wa suka kai harin 9/11, kuma me ya faru?

Asalin hoton, GLV
Ƙungiyar masu tsattsauran ra'ayin addini ta al-Qaeda suka shirya harin daga Afghanistan.
Harin wanda Osama bin Laden ya jagoranta, sun zargi Amurka da ƙawayenta da haddasa rikici a ƙasashen musulmi.
15 daga cikin maharan ƴan ƙasar Saudiyya ne kamar Osama. Biyu kuma daga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, ɗaya kuma daga Masar, ɗaya kuma daga Lebanon.
bayan harin, shugaban Amurka na lokacin George W Bush ya ƙaddamar da yaƙi a Afghanistan - tare da goyon bayan aminanta - domin kakkaɓe al-Qaeda da kuma farautar Osama bin Laden.
Amma sai a 2011 Amurka ta gano maɓuyar Osama a Pakistan kuma ta kashe shi.
Wanda ake zargin ya kitsa harin 9/11, Khalid Sheikh Mohammad, a Pakistan aka kama shi a 2003, tun lokacin ana tsare da shi a gidan yarin Guantanamo Bay, Cuba kuma har yanzu yana jiran shari'a.
A bana dakarun Amurka suka fice daga Afghanistan bayan shafe shekaru 20 suna yaƙi.
Shin Ronaldo zai iya maimaita abin da ya yi a Man United shekara 12 baya?

Asalin hoton, Getty Images
Filin wasa na Old Trafford ya dauki sowa bayan da Cristiano Ronald ya jefa kwallonsa ta farko a kungiyar a wasansa na farko tun bayan dawowarsa.
Shekara 12 da barin kungiyar, dan wasan ya dawo da burin kara maimaita abin da ya yi a baya.
Cikin wasanni shidda da ake yi a yanzu a Premier wasan Man United ne kawai aka zura kwallo wadda Ronaldo ya ci.
Mason Greenwood ya buga wata kallo, inda mai tsaron ragar Newcastle ya gaza kamata Ronaldo ya sata a raga.
Ronaldo ya ruga wajen tuta domin yin murnar cin kwallo kamar yadda ya saba.
Abin da jaridun Iran ke cewa kan harin 9/11

Asalin hoton, Reuters
Harin 9/11 da aka kai a Amurka ya mamaye kanun labaran jaridun Iran a ranar Asabar da ake cika shekara 20 da kai harin.
Jaridar Vatan-e Emruz mai ra’ayin riƙau ta yi zanen tagwayen benen da aka kai harin kamar kafar wando da tutar Amurka da kuma hula da aka yi wa ado da taurari tana faɗuwa ƙasa, ɗauke da kuma kanun labarin cewa “Harin 9/11, farkon faɗuwar Amurka.
Jaridar Oods ta bayyana shakku kan ko shugaba Joe Biden ya saki bayanan da ke tabbatar da gaskiyar harin 9/11,a wani sharhi da ta yi mai taken “Harin 9/11, ƙaryar shekara 20.”
Jaridar Aftab-e Yazd mai da’awar sauyi, ta wallafa hira ne da Ali Bigdeli, malamin Jami’a kuma mai sharhi kan siyasar duniya wanda ya ce “ba zai taɓa yiyuwa a kai hari a cibiyar kasuwanci a Amurka ba tare da haɗin bakin Amurka ba.”
Jaridar ta ambato kalaman Noam Chomsky tana cewa yaƙin Amurka yaƙi ne na tarwatsa duniya, tare da bayyana dawowar Taliban bayan shekara 20.
Crystal Palace ta lallasa Tottenham

Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Zaha ya ci ƙwallo ta farko a kakar bana Odsonne Edouard ya ci ƙwallaye biyu a ranar da ya fara yi wa Crystal Palace wasa inda ƙungiyar ta doke Tottenham
Karon farko kenan da Palace ta yi nasara a kakar bana tare da karya lagon Tottenham da ta lashe wasanninta uku a Premier League.
Wilfried Zaha ya ci wa Palace ƙwallo a bugun fanariti.
Sakamakon ya ba Palace damar haurowa matsayi na 11 a teburin Premier.
Hotunan tunawa da harin 9/11 a birnin New York

Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wata mata da saurayinta yayin da suke tsaye kusa da sunan mahaifinta a bikin na tunawa da 9/11 
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wani jami'in kashe gobara yana rike da hoton abokin aikinsa da ya mutu gabanin bikin 
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wani mutum yana alhini a wurin tunawa da harin 9/11, yana ɗora hannu kan sunayen da aka rubuta a wurin 
Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Tsoffin shugabannin Amurka biyu sun halarci bikin, Barack Obama da matarsa da kuma Bill Clinton da matarsa An fara bikin tunawa da harin 9/11
Shugaban Amurka Joe Biden na jagorantar bikin tunawa da hare-haren 11 ga watan Satumba da aka kai a ƙasar.
An yi shiru na minti ɗaya misalin ƙarfe 08:46 na safe agogon New York lokacin da aka kai harin farko a tagwayen benen cibiyar Kasuwanci ta duniya.
Dangin waɗanda harin ya rutsa da su za su ggabatar da jawabi, daga nan kuma a dinga kiran sunayen waɗanda harin ya kashe.
Tsoffin shugabannin Amurka biyu sun halarci bikin, Barack Obama da matarsa da kuma Bill Clinton da matarsa

Asalin hoton, Getty Images
Hamɓararren shugaban Guinea yana cikin ƙoshin lafiya - Ecowas

Asalin hoton, AFP
Ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta Ecowas ta ce shugaban Guinea Alpha Conde da sojoji suka hamɓarar, yana cikin ƙoshin lafiya.
Wakilanta sun ziyarci Mista Conde, wanda sojoji suka tsare bayan juyin mulki a ranar Lahadi.
Sun kuma tattauna da shugabannin juyin mulkin, cikin har da jagoransu Laftanal Kanal Mamady Doumbouya.
"Shugaba Conde yana nan cikin ƙoshin lafiya", in ji shugaban Ecowas Jean-Claude Kassi Brou bayan ya gana da shugaban mai shekara 83.
Ecowas da Tarayyar Afirka dukkaninsu sun dakatar da Guinea, inda suka baƙaci a gaggauta sakin Mista Conde tare da ƙasar kan kundin tsarin mulki.
Sabuwar gwamnatin sojin ta yi alƙawalin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya, amma shugabannin sojin ba su bayyana yadda za su yi ba da kuma lokaci.
Harin 9/11: Har yanzu wasu na ganin maƙarƙashiya ce bayan shekaru 20

Asalin hoton, Getty Images
Maƙarƙashiyar farko da aka fara yaɗawa ta fara bayyana a Intanet sa'o'i kadan bayan harin ranar 11 ga watan Satumban 2001, kuma bayanai masu cin karo da juna na maƙarƙashiyar sun ƙaru sosai saboda wanzuwar kafofin sada zumunta.
Ko da yake, hukumomin gwamnatin Amurka kan 9/11 da gungun masana sun musanta zargin duk wata maƙarƙashiya, amma ƙungiyoyin masu fafutika na Amurka da kuma ƙungiya mai fafutikar tabbatar da gaskiya kan harin 9/11 sun nace kan cewa an ɓoye gaskiyar lamarin.
Wasu manyan ƴan siyasa, da fitattun mutane da kafofin yaɗa labarai na bayyana shakku kan bayanan hukumomi.
Sabon zancen da ya ɓullo yanzu na zargin makarƙashiya, ya yaɗu, kuma sun yi imani cewa gwamnati ko jami'anta na ɓoye suna da hannu a hare-haren, wasu kuma na zargin cewa gwamnatin Amurka ce ta kai harin ko tana sane kuma ta ƙyale.
Waɗannan ra'ayoyin sun yi daidai da imanin da wasu masu fafutika a intanet na baya bayan nan cewar wani shiri ne na manyan ƙasashe na taƙaita 'yancin ɗan adam don bayar da dama ga wanzuwar gwamnati mai ƙarfin iko a duniya.
Waɗannan ƙungiyoyin sun ta yaɗa tunaninsu a intanet tare da bayyana hujjoji na kimiya.
Lafiya Zinariya: Magungunan tazarar haihuwa da illolinsu
Bayanan sautiLafiya Zianariya kan magungunan tazarar haihuwa da illolinsu Ƴan bindiga sun buƙaci a ba su shinkafa a matsayin kuɗin fansa a Sokoto

Asalin hoton, Other
Ƴan bindiga masu satar mutane sun nemi a ba su shinkafa maimakon kuɗi domin su saki mutanen da suka yi garkuwa da su a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya, kamar yadda Jaridar DailyTrust ta ruwaito.
Wani mazauni garin Sabon Birni na jihar Sokoto ya shaida wa jaridar cewar ƴan bindigar sun saki yarinyar makwabcinsa bayan an kai masu abinci.
Kuma rahotannin sun ce mudun shinkafa 10 aka kai wa ƴan bindigar suka saki yarinyar.
Haka kuma kuma wasu ƴan bindigar sun buƙaci akai masu buhun shinkafa da kwalayen taliya kafin su saki wani direban mota bayan da farko sun buƙaci a ba su miliyan 15.
An haramta cin kasuwanni a jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina da Kaduna da Neja, matakin da ake ganin ya jefa ƴan fashin cikin yunwa.
Rikicin jam’iyyar APC da makomarta a zaɓen 2023
Babban burin jam`iyyar siyasar da ta kafa gwamnati shi ne ta dade tana jan-zarenta.
Jam`iyyar APC mai mulki a Najeriya za ta kammala wa`adin mulkinta na biyu ne a shekara ta 2023, wannan ne ya sa ta dukufa wajen baza saiwarta a sassan kasar domin ta dore da mulki.
Sai dai kuma wasu na ganin cewa tana da babban kalubale a gabanta, sakamakon rashin cika wasu daga cikin muhimman alkawuran da ta yi wa `yan kasar, musamman ma maganar inganta tsaro, ga kuma ce-ce-ku-cen da ake yi a kan wadansu kararraki da kuma yankin da ya kamata ya karbi mulkin kasar.
Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, kuma jigo a jam`iyyar APC.
A filin Gane Mani Hanya, Ibrahim Isa ya tattauna da shi a kan yadda yake kallon makomar jam`iyya mai mulkin a babban zaben da ke tafe:
Bayanan sautiRikicin jam’iyyar APC da makomarta a zaɓen 2023 Korona ta yi ajalin tsohon Firaministan Ivory Coast
Charles Konan Banny, wanda ya taba riƙe muƙamin firaminista Ivory Coast daga 2005 zuwa 2007, ya mutu a asibitin Paris bayan kamuwa da korona, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na AFP ya ruwaito.
Shugaba Alassane Ouattara ya bayyana alhininsa ga mutuwar Mr Konan Banny, mai shekara 78, yana mai cewa a shafinsa na Twitter cewa " abokinsa kuma ɗan uwa ya yi wa ƙasa aiki" wanda ya taka muhimmiyar rawa ga zaman lafiyar ƙasa
"Ya sauya tunanina kan siyasar Ivory Coast da kuma ƴan siyasa," kamar yadda tsohon firaminista Guillaume Soro, wanda ya gudu daga ƙasar ya bayyana.
Cristiano Ronaldo zai fara haskawa a Old Trafford

Asalin hoton, @ManUtd
Cristiano Ronaldo ya ce a shirye yake ya fara taka leda a Manchester United bayan ya dawo Old Trafford a ranar da aka rufe kasuwar musayar ƴan wasa.
Manchester United za ta karɓi bakuncin Newscastle United a ranar Asabar a Old Trafford, kuma hankali zai koma ne kan Ronaldo.
Masharhanta dai na ganin babu shakka zuwan Ronaldo zai inganta Manchester United.
Cristiano Ronaldo zai kafa tarihi a wasan Manchester da Newcastle a matsayin ɗan wasan ya fi yawan tazara bai haska ba a gasar Premier.
Shekaru 12 kenan da kwana 118 da ya buga wasansa na ƙarshe da Arsenal a watan Mayun 2009.
Ronaldo ya ci ƙwallaye 392 a haskawa 390 tun barinsa Old Trafford.
Amurka ta tuna harin 9/11 da aka kai shekaru 20
Shugaban Amurka Joe Biden, ya yi kira ga Amurkawa da su haɗa kansu, a saƙonsa da ya aika wa ƴan ƙasar a yau 11 ga watan Satumba, shekara 20 cif tun bayan da wani hari da ƙungiyar Al Qaeda ta kai cibiyar kasuwanci ta Amurka da kuma cibiyar tsaron ƙasar ya yi sanadin mutuwar kusan mutuum 3,000.
Mista Biden ya aika da saƙon nasa ne ta bidiyo inda ya yi gargaɗin cewa duk wani da ke da niyyar cutar da Amurka za a kama shi kuma a sa ya girbi abin da ya shuka.
Shi ma Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken, ya yi jawabi kan wannan rana inda ya ce Ranar 11 ga watan Satumba, ta kasance rana mafi duhu a tarihin Amurka, sai dai kuma ranar ta zo mana da wasu abubuwa da suka hada da nuna soyayya ga bil adama da tausayi da ƙarfin hali.
Hukumomi a Amurka sun bayyana cewa za a saka matakan taro matuƙa a yau domin bikin cika shekara 20 ɗin duk da cewa ba a ga alamun wata barazana ba.

Asalin hoton, Reuters
An kama fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Isra‘ila

Asalin hoton, Reuter
Isra’ila ta kama hudu daga cikin fursunoni shida Falasdinawa da suka tsere daga gidan yarinta ta hanyar haka rami a makon da ya gabata, kamar yadda ‘yan sandan Isra’ila suka bayyana.
An kama biyu ne a wani garejin mota da safiyar Asabar, in ji ‘yan sanda.
Sauran kuma an kama su ne kusa da garin Nazareth a ranar Juma’a.
Tun a ranar Litinin aka kaddamar da farautar fursunonin bayan sun tsere a gidan yarin Gilboa da ke arewacin Isra‘ila, karon farko da fursunoni suka tsere Falasdinawa cikin shekaru 20
Mummunar tarzoma ta ɓarke a gaɓar yamma da kogin Jordan bayan falasdinawan waɗanda suka gudo daga wani gidan yarin mai tsatsauran tsaro.
Rundunar sojin Isra'ila ta bayyana cewa kusan Falasdinawa 600 ne suka yi arangama da sojoji a wani shingen bincike da ke kusa da birnin Jenin.
Wasu daga cikin falasɗinawan sun yi harbi wasu kuma sun jefa abin fashewa da aka haɗa da fetur.
Sojin Isra'ilar sun bayyana cewa sun harbo wani makamin roka da Falasɗinawan suka harba daga Gaza zuwa kudancin Isra'ila
Corona ta kama mutum 39 a Gombe
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 466 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Juma'a.
Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu da cutar a jihar Legas suke inda aka samu ƙarin mutum 134 da suka kamu da cutar a jihar yayin da jihar Ribas aka samu mutum 82 da suka kamu da cutar sai kuma Edo mutum 69.
Ga jerin jihohin da aka samu karin yaduwar cutar ranar Juma'a:
- Legas-134
- Ribas-82
- Edo-69
- Gombe-39
- Abuja (Babban Birnin Najeriya)-32
- Kaduna-21
- Filato-20
- Benue-19
- Kwara-17
- Delta-16
- Akwa Ibom-10
- Bayelsa-5
- Kano-2
A jimillance, adadin mutanen da suka kamu a faɗin ƙasar sun kai 198,239 sai dai 185,780 sun warke.
Akwai kuma mutum 2,588 da suka mutu

Asalin hoton, NCDC
