Ba abu ba ne mai sauki rike ma'aikatar noma - Nanono
Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
Imam Saleh, Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge
Jirgin fasinja na farko ya kwashi mutane daga Afghanistan

Asalin hoton, Getty Images
Wani jirgin fasinja da ya tashi daga filin jirgin saman birnin Kabul dazu dauke da 'yan kasashen waje fiye da dari daya, ciki har da Amurkawa, ya sauka a Doha babban birnin kasar Qatar.
Jirgin na kasar Qatar shi ne jirgin fasinja na farko da aka yi shata da ya tashi daga Afghanistan tun bayan ficewar Amurka da sauran kasashen yammacin Turai a watan jiya.
Sai dai rahotannin farko sun ce akwai fasinjoji dari biyu ne a cikin jirgin.
Mutlaq al Qahtani, wani jami'in kasar Qatar ne wanda ya ce "Wannan rana ce da ke cike da tarihi, saboda sake bude filin jirgin saman Kabul ga jiragen kasa da kasa, kuma duk da cewa akawi matsaloli, amma za mu shawo kansu tare da taimakon 'yan uwanmu na Afghanistan.
Ana kiyasin akwai daruruwan 'yan kasashen waje da su ka makale a cikin Afghanistan tun da kungiyar Taliban ta kwace kasar a watan jiya.
'Idan duniya ta gaza hana Iran mallakar nukiliya to Isra'ila za ta dauki mataki'

Asalin hoton, Getty Images
Ministan harkokin wajen Isra'ila Iair Lepid ya shaida wa manema labarai cewa ya kamata a dakatar da Iran daga mallakar makamin nukiliya.
Iair Lepid ya bayyana hakan ne a wata ziyarar kwana guda da yakai Moscow, lokacin da ya tattauna da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov.
Ya yi gargadin cewa "Yadda Iran ke ci gaba da kokarin mallakar makamin nukiliya ba matsalar Isra'ila ba ce kawai, a'a matsalar duniya ce baki daya. inda ya ce mallakar makamin a wajen Iran zai haifar da gasar mallakar sa a yankin baki daya.
Ya kara da cewa yayin da Isra'ila ta gamsu da cewa "Rasha na da matukar tasiri" a yankin, "Za mu ci gaba da tsaya wa domin kare kanmu daga barazanar Syria da ta sauran wurare.
Kotu a Jamus ta ci tarar Jerome Boateng dalar Amurka miliyan 2

Asalin hoton, Getty Images
A Jamus, wata kotu ta sami dan wasan kwallon kafan nan dan kasar Jamus Jerome Boateng da laifin cin zarafin tsohuwar matar da yake zama da ita, kuma ta umarce shi da ya biya ta dala miliyan biyu da dubu dari daya.
Dan wasan wanda Jamus ta ci kofin duniya na shekarar dubu biyu da goma sha hudu da shi, ya taba zama mai tsaron baya na kungiyar Beyern Munich.
Ta bayyana cewa ya yi wa matar - wadda ta haifa ma sa 'ya'ya biyu duka ne - yayin da su ke wata gardama a tsibirin Caribbean, wurin da su ka tafi hutu shekara uku da ta gabata.
A karkashin dokokin kasar Jamus, ana iya daure Mista Boateng har na tsawon shekara biyar a kurkuku.
Hazard na daf da komawa kan ganiya in ji Roberto Martinez

Asalin hoton, Getty Images
Kocin tawagar Belgium, Roberto Martinez ya ce Eden Hazard zai koma kan ganiya zai taka wa kasar rawa a Nations League a watan gobe.
Dan wasan ya yi fama da jinyar raunin da ya hana shi sakar tun komawar sa Real Madrid daga Chelsea, wanda ya yi wata 18 ba tare da buga wa Belgium wasa ba.
Tawagar ta je da shi gasar cin kofin nahiyar Turai wato Euro 2020, duk da bai da kuzari a gasar da Italiya ta lashe.
Hazard ya shiga wasan da ya yi canji a karawar da Belgium ta doke Belarus ranar Laraba a fafatawar da suka yi a Kazan, inda tawagar ke daf da samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022.
Ina so a rika tunawa da ni a matsayin wanda ya daidaita Najeriya - Buhari

Asalin hoton, Twitter
Shugaban Najeriya Muhammad ya ce yana so a rika tunawa da shi a matsayin wanda ya daidaita Najeriya ta fuskar tsaro da tattalin arziki da habbakar kasa da nasarar da ya samu wajen yaki da cin hanci da rashawa.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya fitar ya ce Buhari ya bayyana hakan ne a Owerri ranar Alhamis.
Shugaban ya bayyana wa shugabannin kudu maso gabashin Najeriya a wata ziyara da ya kai ta kwana guda a jihar Imo cewa, cikin abin da ya yi kasa da shekara biyu da ya rage na mulkinsa, har yanzu harkar tsaro ita ce abin da ya fi bai wa mahimmanci.
Shugaban ya ce lokacin da yaki da cin hanci ke kara zama abu mai wuya a Najeriya, yana son ya bar wani tarihi da bajinta da za a rika tunawa da shi.
Ahmed Musa ya buga wa Najeriya wasa na 100

Asalin hoton, NFF
Ranar Talata Najeriya ta je ta doke Cape Verde 2-1 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya shiyyar Afirka.
Kyaftin din tawagar Super Eagles ya buga karawar, wadda ita ce ta 100 da ya i, duk da bai ci kwallo ba a wasa.
Nasarar da Najeriya ta samu ya sa ta dare mataki na daya a kan teburi na uku da maki shida, bayan da ta fara cin Liberia 2-0 ranar Juma'a.
Cikin watan Afirilun 2020, koci Lars Lagerback ya bai wa Ahmed Musa goron gayyata, domin buga wasannin shiga gasar cin kofin duniya da Afirka ta Kudu za ta karbi bakunci.
Dan wasan ya samu wannan damar, bayan da ya taimakawa kasar ta lahe WAFU Cup, wanda ya ci Benin kwallo a 2010.
A dai gasar a wasa da Burkina Faso a Abeokuta, Musa ne ya ci kwallon da ya kai Najeriya karawar karshe.
Ba abu ba ne mai sauki rike ma'aikatar noma - Nanono

Asalin hoton, Nanono
Tsohon ministan gona na Najeriya Mohammed Sabo Nanono ya ce ba abu ba ne mai sauki rike ma'aikatar gonar kasar.
Ya ce ma'aikatu masu zaman kansu na matukar taimaka wa wajen mayar da aikin ma'aikatar mai wahala.
Nanono ya bayyana hakan ne yayin mika al'amuran ma'aikatar ga sabon ministan, Dakta Mohammad Mahmood Abubakar, wanda ya gudana a Abuja.
Japan ta fasa karbar bakuncin Fifa Club World Cup ta bana

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta ce Japan ta janye daga karbar bakuncin gasar kofin duniya ta zakarun nahiyoyi ta bana, saboda tsoron yada cutar korona.
Ana buga wasannin tsakanin zakarun nahiyoyi duniya shida a kowacce shekara cikin watan Disamba.
''FIFA tana tabbatar da cewar hukumar kwallon kafar Japan ta sanar mata da cewar da janye wa daga karbar bakuncin gasar kofin duniya ta zakarun nahiyoyi ta 2021, sakamakon cutar korana da ke kara ruruwa a kasar.'' in ji sanarwa.
Japan ce ta karbi bakuncin wasannin da aka yi a 2016, kuma ta yi niyyar gudanar da fafatawar bana don murnar bikin cika shekara 100, in ji wasu rahotanni.
Gwamnatin Japan ta kara sa dokar ta baci a wasu yankunan kasar tun daga ranar Alhamis, bayan da annobar ke kara baraza a kasar.
'Yan jarida sun ba da labarin yadda 'yan Taliban suka lakada musu duka

Asalin hoton, MARCUS YAM/LOS ANGELES TIMES/SHUTTERSTOCK
'Yan jarida a Afghanistan sun ce 'yan Taliban sun kama su saboda suna kokarin daukar rahoton zanga-zanga sun kuma tsare su tare da lakada musu mugun duka.
Wasu hotuna da ke yawo a intanet sun nuna wasu 'yan jarida a tube da shatin duka a bayansu, bayan jaridar Etilaatroz ta wallafa kama su a Kabul.
Daya daga cikinsu Taqi Daryabi, ya shaida wa BBC cewa an kai shi wani caji ofis din yansanda inda aka rika tamola da shi.
A ranar Larabar da ta gabata sai da aka hana tawagar BBC ita ma daukar rahoton abin da ke faruwa.
'Yan bindiga sun yi garkuwa da ma'aikatan kamfanin Obasanjo
Bayanan sauti'Yan bindiga sun yi garkuwa da ma'aikatan kamfanin Obasanjo Latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraren rahoton Umar Shehu Elleman:
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da ma’aikata uku a kamfanin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo uku, a wani kauye a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Rundunar 'yan sandaa jihar ta ce a ranar Laraba ce ‘yan bindigar suka tare ma’aikatan uku karkashin kamfanin Obasanjo, Obasanjo Holdings da ke Kobape a karamar hukumar Obafemi-Owode.
An fitar da jadawalin sabuwar shekarar karatu a Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta fitar da sabon jadawalin zangon karatun firamare da sakandare na jihar.
Wata sanarwa da Hukumar da ke luka da harkokin makarantun jihar, wadda Darakta Janar ta hukumar, Umma K. Ahmed ta sanya wa hannu ta ce za a soma sabon zangon karatu na shekarar 2021/2022 ranar Lahadi 12 ga watan Satumba, sannan a kammala ranar Juma'a 17 ga watan Disamba, 2021.
Ta kara da cewa za a soma zangon karatu na biyu ranar 9 ga watan Janairun 2022 inda za a kammala ranar 8 ga watan Afrilu.
Kazalika za a soma zangon karatu na uku ranar 1 ga watan Mayun 2022 kuma a gama ranar 5 ga watan Agustan shekarar.
Sanarwar ta kara da cewa za a bayar da hutu tsakanin wadannan zangunan karatu kuma za a yi dukkan hutun da gwamnatin tarayya take bayarwa a kasa baki daya.
Museveni ya yi barazanar janye dakarun Uganda daga Somalia

Asalin hoton, AFP
Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya yi barazanar janye dakarun kasarsa da ke cikin tawagar da Tarayyar Afirka masu aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia.
Ya yi barazanar ce sakamakon tabarbarewar dangantaka tsakanin shugaban Somalia da firaiministan kasar.
Shugaba Museveni ya taba yin irin wannan barazana a 2011 domin matsa lamba ga shugabannin Somali su daidaita tsakaninsu.
Uganda ta tura dakarunta cikin dakarun Tarayyar Afirka da ke Somalia a 2007. Kasar tana da sojoji fiye da 6,000 cikin dakaru 22,000 na kungiyar da ke Somalia.
An kama jabun dalolin Amurka a Mozambique

Asalin hoton, Getty Images
An kama kusan $16,000 (£11,500) na jabu Mozambique, inda masu bincike suka yi zargin cewa wata kungiyar masu buga jabun dala ce ta buga su.
'Yan sanda sun ce sun kama 'yan kasar Angola guda biyu, kuma za a bayar da sammacin kama wasu mutanen da ake zargi.
Ana zargin 'yan kasar Mozambique da Angola da Afirka Ta Kudu na da hannu a buga kudaden na jabu - kodayake yunkurinsu na yin jabun tambarin kudin Mozambique bai yi nasarab, a cewar 'yan sanda.
'Yan kasar ta Angola da aka kama sun musanta hannu a buga jabun dalar. Daya daga cikinsu ya ce shi dan kasuwa ne wanda ya shiga Mozambique ta hanyar da ta kamata watanni biyu da suka gabata domin samun damarmakin kasuwanci, kuma bai san dalilin da ya sa aka kama shi.
Ƴan Afghanistan na ci gaba da yi wa Taliban tutsu

Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Masu zanga zanga Ana ci gaba da zanga-zanga a Afganistan, a wani mataki na bijirewa dokar hana zanga-zanga da gwamnatin Taliban ta sanya.
Ministan harkokin cikin gida na Taliban ya ce an dauki matakin ne saboda wasu mutane na amfani da zanga zangar don janyo matsalar tsaro da kuma haifar da hargitsi.
A cikin kwarin Panjshir,rahotanni sun ce mayakan Taliban din sun wulakanta kabarin shahararren jagoran masu adawa da Taliban Ahmed Shah Massoud a bikin cika shekara 20 da kasheshi.
Jami’an Amurika sun ce kimanin yan Amurika 200 da yan kasashen waje na shirin barin Kabul a cikin jirage masu saukar ungulu da yammacin yau, bayan Taliban ta amince da kwashe su.
An yi faretin zagayowar ranar da aka kafa Koriya Ta Arewa

Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, Koriya Ta Arewa Koriya ta Arewa ta gudanar da wani fareti domin bikin zagayowar ranar da aka kafa kasar shekara saba'in da uku da ta gabata, sai dai ba ta baje kolin kayan yakinta ba.
Wakiliyar BBC ta ce ba a ga yadda kasar ta saba baje kolin rokokin yaki masu dogon zango ba, inda a wannan karon ta nuna taraktocin yaki da karnukan farauta da kuma motocin kashe gobara.
Shugaba Kim Jong-un ya halarci bikin, sai dai bai yi jawabi ba kamar yadda aka saba.
Masu nazarin siyasar kasar na cewa gwamnatin Koriya Ta Arewa na son nuna wa duniya cewa ta fi mayar da hankali kan harkokin cikin gida ne.
An haramta hawa babura a jihar Jigawa

Asalin hoton, JSG
Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da haramta hawa babura a kananan hukumomi 27 da ke faɗin jihar. daga ƙarfe 9 na dare zuwa 6 na safe.
Gwamnatin ta ce matakin na da alaka da matsalar tsaron da jihar ke fama da ita.
Shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomin jihar Bala Chamo ne ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin wata tattaunawa da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.
Buhari ya lashi takobin kawo ƙarshen kai hare-hare a jihar Imo

Asalin hoton, Ibekwe Chinedu Obinna
Bayanan hoto, Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya lashi takobin kawo karshen kai hare hare a jihar Imo da ke kudancin Najeriya.
Yana magana ne yayin ziyarar kaddamar da wasu ayyuka a jihar.
''Babu wata al'umma da za ta samu ci gaba alhalin tana fama da matsalar tsaro, inji shugaban yayin da yake gabatar da jawabi''
Tsohon shugaban Afghanistan ya nemi gafarar ƴan ƙasar saboda tserewa Taliban

Asalin hoton, Reuters
Tsohon shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya nemi afuwar ƴan ƙasar saboda tserewa, yayin da mayaƙan Taliban ke ƙoƙarin ƙwace iko.
A halin da ake ciki yana neman mafaka a Qatar tun bayan barinsa Afghanistan.
Sai dai a yanzu ya ce ''Barin birnin Kabul shine mataki mafi tsauri da na taɓa ɗauka a rayuwata, ku min afuwa ban jagorance ku har zuwa ƙarshen tuka tuka tik ba''
Ba shiri tsohon shugaban ya sa kafa ya fice daga Afghanistan, lokacin da mayakan Taliban suka ja tunga a wajen birnin Kabul tare da ba wa gwamnati wa'adin yin saranda.
Buhari ya isa jihar Imo, cibiyar IPOB

Bayanan hoto, Shugaba Buhari yayin da yake fitowa daga jirgi Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya isa Jihar Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar a ranar Alhamis, ɗaya daga cikin jihohin da masu fafutukar kafa Biafra ke neman ɓallewa.
Ya yi tafiyar ne a wata ziyarar aiki don kaddamar da wasu ayyuka.
Rahotanni daga jihar Imo na cewa ƙungiyar ta ba da umarnin jama'a su zauna a gida a ranar Alhamis din saɓanin Litinin, wani abu da ake ganin yana da nasaba da ziyarar ta Shugaba Buhari.

Asalin hoton, Bayo Omoboriowo
Bayanan hoto, Lokacin da ake yin taken Najeriya 
Bayanan hoto, Wasu gaggan jam'iyyar APC kenan da suka tarbi shugaban 
Asalin hoton, Bayo Omoboriowo
Bayanan hoto, Masu tarbar shugaban
