JAMB ta yi wa El-Rufai raddi kan shawarar fasa rage wa ɗalibai maki

Asalin hoton, KSC
Hukumar shirya jarrabawar share fagen shiga jami'o'in Najeriya JAMB ta mayar wa gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i martani kan shawarar da ya bata, ta fasa rage wa ɗaliban arewacin Najeriya makin da ake bukata na jarrabawar.
Hukumar ta ce ba ita ce ke da alhakin ragewa daliban yankin arewacin Najeriya maki ba.
A cewar JAMB, ''Gwamna El-Rufa'i ya yi kurkure da ya yi tunanin cewa ɗaliban arewacin Najeriya na cin wata gajiya da takwarorinsu na kudancin ƙasar basa ci, wannan kurkusre ne''
Ma magana da yawun hukumar Fabian Benjaminne ne ya mayar wa gwamnan martanin yayin wata zantawa da jaridar Punch a ranar Talata.
Ya ce makin da ake bukata ya danganta da kwas ɗin da kowanne ɗalibi ke son yi, da kuma makin da kowacce jami'a ta iyakance.


