Wane hali ake ciki game da kwashe fararen hula daga Kabul ?

Asalin hoton, Reuters
Dubban mutane na ci gaba da kasancewa a Afghanistan duk da ci gaba da jigilar fararen hulla da jiragen soji ke yi inda aka kwashe mutane kusan dubu ashirin cikin awanni ashirin da hudu da suka gabata.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya dage cewa kokarin Amurka na taimaka wa mutane barin kasar zai ci gaba.
Mista Blinken ya ce kungiyar Taliban na ci gaba da bada hadin kai ba tare da kawo cikas ga wannan aiki ba, kana shugaban kasa ya nemi a yi shiri na musamman ko da zai yanke shawarar dakarunmu su ci gaba da zama a Afghanistan bayan wa'adin da aka sanya.
To sai dai Taliban ta ki amincewa da karin wa'adin, yayin da sakataren tsaron Burtaniya ya fada wa 'yan majalisar kasar cewa zai fi kyautuwa ga 'yan Afghanistan din da ke son ficewa su yi hakan ta kasa.













