Rufewa
Masu bibbiyarmu a wannan shafin da haka za mu diga aya a wannan Larabar, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu. Umaymah Sani Abbdulmumin ke cewa a kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Umar Mikail and Umaymah Sani Abdulmumin
Masu bibbiyarmu a wannan shafin da haka za mu diga aya a wannan Larabar, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu. Umaymah Sani Abbdulmumin ke cewa a kwana lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Wata tawagar masana kimiyya ta ce shekarar da tagabata ce tafi kowacce zafi a tarihi a yawancin kasashen Turai, wanda ya dora karin nauyi kan albarkatun da ke doron kasa da al'ummar da ke rayuwa a kanta.
Sun ce an sami karuwar fiye da maki daya da digo tara na ma'aunin celsius, wanda karuwa ce idan aka kwatanta da alkaluman shekarun alif dari tara da tamanin da daya zuwa dubu biyu da goma -- kuma yankin arctic na kololuwar duniya ma ya sami karuwar maki daya fiye da yadda aka saba gani.
Masana kimiyyar su dari biyar da su ka rubuta rahoton na shekara-shekara kan tasirin sauyin yanayi sun kuma ce nau'ukan iskar gas wato greenhouse gases masu dumama yanayi, sun kai matakin da ba a taba gani ba a shekarar dubu biyu da ashirin.
Akalla mutum 8 aka kashe a wani hari da aka kai wa al'ummar Yelewta da ke karamar hukumar Guma ta jihar Benue.
Shaidu sun ce an aikata kisan ne kan wasu ƴan kasuwa da ke rufe shagunansu.
Shugaban karamar hukumar Goma, Caleb Aba ya shaidawa manema labarai a Makurdi cewa an shake mutanen ne har mutuwa.
Aba ya ce ranar kasuwa ce a Yelewta don haka mutane ba sa tashi da wuri, wannan damar ƴan bindiga suka yi amfani da ita wajen kutsawa da kashe mutanen.
Masana daga Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, na gargadin hukumomi cewa damar da ake da ita ta binciken asalin inda kwayar cutar korona ta fito na wucewa.
Masanan, wadanda suka wallafa rahoton farko na WHO kan yadda cutar ta bayyana daga China, sun ce jinkirin na iya hana duniya gano bayanan da ake bukatar samu saboda za su shude.
Wakiliyar BBC ta ce "China ta ki amincewa da kiran da WHO ta yi na aikawa da tawagar ta masanan, bayan da hukumar ta ce a sake duba wani dakin bincike a birnin Wuhan."
Wannan gargadin nasu na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Lafiyar ke janyewa daga aikawa da wata tawagar kwararru zuwa China a karo na biyu.
Jami'ai sun ce kasar nan da masana kimiyya masu yawa wadanda ba sa bukatar a sa musu ido.

Asalin hoton, NNPC
Shugaban kamfanin NNPC a Najeriya, Mele Kyari ya ce ya umarci a binciki zargin sayarwa Najeriya lita miliyan 103 na man fetur a kullum a watan Mayu.
Kyari ya shaida hakan ne a ranar Laraba lokacin da ya bayyana gaban kwamitin majalisar wakilai kan kuɗaɗe.
Kwamitin a yanzu haka na sauraron bayanai kan kudaden da kamfanin ya kashe tsakanin 2022 zuwa 2024.
A lokacin da yake amsa tambayar kwamitin kan sayarwa ƴan najeriyar lita 103 na man fetur a kullum, Kyari ya ce za su binciki gaskiya zancen.
Ya kuma shaida cewa, idan akwai ranar da ake sayer ko shan lita miliyan 103 na fetur, bai sani ba. Amma ya diga ayar tambaya lokacin da aka gabatar masa da wadanan alkaluma. Ya ce babu shaka shi ya shaida hakan kwanaki uku da suka gabata, amma ya ce za su bincika.
Shugaban jam'iyyar PDP reshan jihar Legas, Dr Adegbola Dominic ya rasu bayan fama da annobar korona.
Wannan na zuwa ne kasa da wata guda bayan jam'iyyar ta rasa sakatarenta, Prince Muiz Shodipe-Dosunmu.
Shodipe-Dosunmu ya rasu ne a ranar 28 ga watan Yuli bayan kamuwa da annobar.
Bayan mutuwarsa ce shugaban jam'iyyar, Dominic ya kebe kansa, kafin daga bisani jikin ya yi tsanani har ta kai ga ajalinsa.

Asalin hoton, Reuters
Kungiyar Taliban ta shaida wa BBC cewa sai 'yan Afghanistan din da Amurka da kawayenta su ka amince musu ne za ta ba izinin shiga filin jirgin saman Kabul.
Shiga filin jirgin saman na kara zama mai wahala ga 'yan Afghanistan ko da kuwa su na da takardun izinin ficewa daga kasar.
Wasu 'yan Afghanistan da aka shirya kwashe su daga kasar da safiyar yau sun yi watsi da kokarin ficewa, saboda fargabar da su ke yi na rashin tsaro akan hanyar zuwa filin jirgin saman.
A ranar Talata, Kungiyar ta sanar da cewa ba ta son 'yan kasar su rika ficewa.

Asalin hoton, Getty Images
Mayakan ISWAP da Boko Haram sun kashe kansu a wata kazamar rigima da ta kaure tsakaninsu a yankin arewacin Abadam na jihar Borno.
Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa mayakan Boko Haram da suke shirin mika-wuya sun fuskanci ruwan wuta data bangaren ISWAP a wani dajin Dumbawa.
Mayakan na hanyarsu ta mika wuya ga dakarun da ke iyakar jamhuriyar Nijar a makon da ya gabata, lokacin da aka far musu.
Wata majiya kuma ta shaida cewa rashin jituwa tsakanin bangarorin biyu na sake tsananta abin da ke kai wa suna kashe junansu a kullum.

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan bindiga sun sace matar tsohon shugaban kauyen Kofa ta karamar hukumar Kusada a jihar Katsina.
Wani mazaunin garin da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaidawa jaridar Daily Trust ta Najeriya cewa maharan sun farwa kauyen ne da sanyin safiyar Laraba.
Kuma suna nufi gidan shugaban kauyen da ya rasu ranar Talata suka dauke wasu iyalansa, ciki harda matarsa.
Marigayin shugaban kofa da ya rasu dan uwan tsohon shugaban kakakin majalisar Katsina ne, wanda ya rasu ranar Talata.
Da aka tuntube kakakin ƴan sanda Katsina, SP Gambo Isah ya ce zai tuntube jami'in da ke kula da yakin.

Asalin hoton, Getty Images
Shugabar Jamus Angela Merkel ta yi kira da a fara tattaunawa da kungiyar Taliban domin a kare ci gaban da aka samu a Afghanistan na shekaru ashirin da su ka gabata.
Yayin da ta ke jawabin a gaban majalisa a birnin Berlin, shugabar ta nanata cewa zahirin lamarin da ke gaban kowa ba mai dadi ne ba, kuma duk yarjejeniyar da za a kulla da Taliban na iya kasancewa wadda babu sharudda.
Mrs Merkel ta tabo batun ci gaban da aka samu a Afghanistan, kamar raguwar mace-macen kananan yara, da samar da ruwan sha mai tsafta da kuma hasken lantarki.
Mrs Merkel ta kuma ce kokarin da Jamus ke yi na kwashe jama'arta, ciki har da 'yan Afghanistan zai ci gaba har zuwa lokacin da aka kammala shi.
Birtaniya da Faransa sun ce zuwa karshen wannan watan, za su kammala kwashe dukkan 'yan kasashensu da sauran 'yan Afghanistan da su ka yi aiki da su.
Rundunar sojin jamhuriyar Nijar ta ce dakarunta sun kashe masu tayar da kayar baya kimanin dari a yankin kudu maso yammacin kasar, a kusa da kan iyakar kasar da Burkina Faso.
Rundunar sojin Nijar ce ta shirya, kuma ta aiwatar da wannan harin, domin gano wadanda su ka kai harin da ya yi sanadin mutuwar wasu sojojin kasar goma sha tara a watan Yuli.
Rundunar sojin ta ce ta kuma lalata motoci da harsasan masu tayar da kayar bayan.
A kan sami hare-hare daga kungiyoyi masu ikirarin jihadi a wannan yankin da ke kan iyakar Nijar da Mali da Burkina Faso.

Asalin hoton, NDA
Rundunar sojin Najeriya ta ƙaryata wasu rahotannin da suka ce sojojin da ke bakin aikin tsaron Kwalejin Horon Sojoji ta NDA bacci suke lokacin da ƴan bindiga suka kai hari wanda ya kai ga kashe sojoji biyu da sace soja ɗaya.
Sanarwar da babban jami’in yaɗa labarai na rundunar sojin ya fitar Manjo Janar Benjamin Olufemi Sawyerr ya ce labarin da wasu jaridar Cable ta wallafa ba gaskiya ba ne inda ya ƙalubalanci jaridar ta bayar da shaidar da ke tabbatar da jami’an sojin suna bacci lokacin da ƴan bindigar suka kawo hari.
Labarin da ake yaɗawa na cewa bacci ya kwashi jami’an da ke kula da kamarori na tsaro lokacin da ƴan bindigar suka abka kwalejin NDA.
Ranar Talata ne ɓarayin suka shiga marantar ta NDA suka kashe sojoji biyu suka yi garkuwa da daya.Kuma tun a ranar rundunar sojan ta ce ta dukufa domin kwato sojan nata.
Wasu rahotannin kafafen yada labarai na Najeriya, da ba a tabbatar ba na cewaan tsinci gawar sojan nan da 'yan fashi daji suka sace a kwalejin ta koyon aikin soji da ke Kaduna.
Rundunar sojin ta ce babban hafsan sojin Najeriya da hukumomin NDA sun kaddamar da bincike domin gano yadda har aka samu matsalar da ta ba ƴan bindiga damar shiga kwalejin.

Asalin hoton, PTSG
Gwamnatin Jihar Filato ta sake saka dokar hana fita kwatakwata a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa bayan harin da wasu 'yan bindiga suka kai a Jihar.
Mai magana da yawun gwamnan jihar, Dr Makut Macham, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Laraba.
Matakin na zuwa ne bayan wasu mahara sun far wa ƙauyen Yelwa Zangam da ke gundumar Zangam ta jihar, inda suka kashe kusan mutum 30 - kodayake hukumomi ba su bayyana adadin mutanen ba.
A cewar Gwamna Simon Lalong, dokar hana fitar ta awa 24 za ta fara aiki ne daga 4:00 na yammacin Laraba 25 ga watan Agusta har zuwa sanarwa ta gaba.
Kusan mako biyu kenan da wasu mutane suka tare wa matafiya Musulmai hanya a Rukuba da ke birnin na Jos, inda suka kashe mutum 27 tare da raunata wasu da dama.
Kisan ya sa gwamnatin jihar ta saka dokar hana fita a ƙananan hukumomi uku ciki har da Jos ta Arewa kafin daga baya a sassauta ta. Gwamnatin ta ce har yanzu dokar hana fita daga 6:00 zuwa 6:00 na safe tana nan daram Bassa da Jos ta Kudu.

Asalin hoton, Getty Images
China za ta ƙaddamar da mazahabar siyasa wadda shugaban ƙasar ya ƙirƙira a jadawalin karatuttuka na makarantun ƙasa.
"Mazahabar Xi Jinping" wato "Xi Jinping thought" a Turance za ta taimaka "wajen samar da aƙidun markisanci (Marxistism)," a cewar Ma'aikatar Ilimi cikin wata sanarwa.
Za a shigar da sabuwar manhajar tun daga makarantun firamare zuwa sakandare.
Wannan ne yunƙuri na baya-bayan nan da Mista Xi Jinping ke yi na ƙara jaddada tasirin Jam'iyyar Kwamunisanci a al'ummar China.
Daga cikin darussan, akwai ilimin leburanci "domin farfaɗo da aƙidar son aiki tuƙuru" da kuma darasi kan tsaron ƙasa.

Asalin hoton, State House
Shugban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce harin da 'yan fashin daji suka kai Kwalejin Horon Sojoji ta NDA zai sa gwamnatinsa "ta hanzarta ɗaukar mataki maimakon sanyaya mata gwiwa".
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya fitar, Buhari ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan sojoji biyu da maharan suka kashe ranar Litinin da tsakar dare, yana mai cewa "ba za su rasu a banza ba".
Wasu rahotanni na cewa maharan sun kutsa makarantar ta horar da sojojin Najeriya na ruwa da na ƙasa da na sama a birnin Kaduna bayan sun yi shigar sojoji. Sai dai hukumar kwalejin ta ce sun haura ne ta katangar da ke kewaye da makarantar.
"Ganin cewa harin na zuwa ne a lokacin da sojoji suka matsa wa 'yan fashi da masu garkuwa da mutane da sauran masu laifi, shugaban ƙasa ya ce wannan mummunan aikin zai jawo hanzarta kawo ƙarshen rashin imani kwakwata kuma abin da sojoji ke yunƙurin cimmawa kenan cikin ƙanƙanin lokaci," a cewar sanarwar.
Sanarwar da ya fitar ranar Laraba ta ƙara da cewa "maimakon hakan ya sanyaya gwiwar dakarunmu kamar yadda aka tsara, zai ƙara musu azama ne wajen kawo ƙarshen miyagu a ƙasar nan, a cewar Buhari".
Wani hoto da ya karaɗe shafukan zumunta na nuna gawar sojan da 'yan bindigar suka sace a harin amma BBC ba ta iya tantance gaskiyar lamarin ba.

Asalin hoton, Reuters
Aikin kwashe mutane daga filin jirgi na Kabul na ƙara sauri yayin da ake kwashe kusan mutum 12,000 cikin awa 12 ranar Talata, a cewar gwamnatin Amurka.
Yayin da aka fitar da kusan 6,400 a jiragen sama na sojojin Amurka, jiragen haɗaka sun kwashe sauran mutanen.
Jumilla, Amurka ta samu fitar da mutum 70,700 tun daga ranar 14 ga watan Agusta.
Sai dai kuma mafi yawan ƙasashe suna ganin ba zai yiwu a kwashe duka wadanda suka cancanci ba kafin janyewar Amurka daga birnin Kabul ranar 31 ga watan Agusta, bayan Shugaba Biden ya kawar da duk wata yiyuwar tsawaita zaman dakarun Amurka a kasar.

Asalin hoton, AFP
Ma'aikatar lafiya ta Ivory Coast ta ce mutum na farko da ya kamu da cutar Ebola tun 1994 ya warke.
Mai cutar wata budurwa ce mai shekara 18 daga Guinea, wadda ta yi balaguro zuwa Abidjan a cikin bas cikin mako biyu da suka gabata, inda a nan ne aka gano tana dauke da cutar.
Jim kadan bayan gano ta ne Ivory Coast ta soma yi wa mutanen da suka yi mu'amala da ita gwajin cutar, baya ga wanda ake yi a kan iyakoki.
Gwaje-gwaje biyu da aka yi wa budurwar a yanzu sun nuna cewa ba ta ɗauke da cutar ta Ebola.

Shugaba Joe Biden ya ce 'yan Taliban wadda ke mulkin Afghanistan a yanzu na taimaka wa Amurka wajen aikin kwashe 'yan ƙasar a Kabul.
A yanzu dai an kara zage dantse a aikin, inda ake kwashe mutane kimanin dubu shida a awanni shida kawai.
Mista Biden ya ce za a iya kammala aikin kwashe mutanen da ke son barin Afghanistan zuwa wa'adin karshen watan nan domin kauce wa hare-haren kungiyoyin da ke da alaƙa da ISIS a filin jirgin sama na Kabul.
Duk da cewa ƙasashen ƙungiyar G7 sun nemi ta tsawaita wa'adin, Amurka ba ta amince da buƙatar tasu ba.
Tuni Taliban ta yi gargaɗin cewa ba za ta amince da aniyar ƙara wa'adin ba kuma dole a dakarun ƙasashen waje su fice a lokacin da aka tsara na 31 ga watan Agusta.
Rahotanni na cewa an kashe wani ma'aikacin ƙungiyar agaji ta Red Cross a Kamaru, a cewar ƙungiyar.
An jikkata Diomède Nzobambona mai shekara 62 sakamakon wani hari a garin Bamenda.
Yana aiki ne a sashen ruwan sha da tsafta a yankin arewa maso yamma na renon Ingila.
"Ya zuwa yanzu babu tabbacin abin da ya haddasa mutuwarsa kuma babu wani bayani da za mu bayar a yanzu," a cewar ICRC ciin wata sanarwa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X