Sau 50 Boko Haram na kai mun hari ina tsira - Zulum

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Taliban: Yadda filin jirgi na Kabul ya wayi gari

    Kabul

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban mutane da ke son ficewa daga Afghanistan na can danƙam a kusa da filin jirgi na Kabul babban birnin Afghanistan.

    Aƙalla mutum 20 ne suka mutu sakamakon harbe-harbe da kuma turmutsitsi tun daga makon da ya gabata.

    An kwashe mutum fiye da 10,000 a ranar Litinin kaɗai, amma lokaci na ƙurewa yayin da wa'adin 31 ga Agusta ke ƙaratowa a matsayin lokacin da za a kammala aikin.

    Wani jami'in NATO ya faɗa wa Reuters cewa ana gudanar da aikin ne "a yanayin yaƙi" yayin da dakarun ƙasashen waje ke ta ƙoƙarin kauce wa tsawaita wa'adin wanda aka ƙulla yarjejeniya da Taliban tun farko.

    Taliban ta ce za ta ɗauki mataki matuƙar ƙasashen Yamma suka wuce wa'adin na 31 ga Agusta. Sai dai ana sa ran ƙungiyar G7 ta ƙasashe mafiya girman tattalin arziki za ta nemi Amurka ta tsawaita wa'adin a yau Talata.

  2. Gwamnatin Kano ta haɗa kai da Faransa don haɓaka noma

    Gwamna Ganduje

    Asalin hoton, KNSG

    Gwamnatin Jihar Kano da ke arewacin Najeriya za ta ƙulla yarjejeniya da Faransa domin haɓaka harkokin noma a jihar.

    Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya bayyana hakan yayin da yake karɓar baƙuncin jakadan Faransa a Najeriya, Jérôme Pasquier, ranar Litinin a Kano.

    Ganduje wanda mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta, ya ce haɗin gwiwar za ta samar da sabbin hanyoyin bunƙasa tattalin arzikin Kano.

    Gwamnan ya gode wa Faransa bisa ƙaddamar da aikin tituna a ƙauyuka sannan ya buƙaci masu zuba jari da "su nemi arziki a Kano ta hanyar bincika albarkatu na ɗan Adam da kuma na Allah da ke jihar".

    Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito Mista Pasquier yana cewa ya je Kano ne "domin haɓaka alaƙa tsakanin Najeriya da Faransa".

    "Kano babbar kasuwa ce kuma mai matuƙar muhimnmanci gare mu," in ji shi.

  3. Isra'ila ta sake kai hare-hare a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    A wnai mataki na ramuwar gayya, rundunar sojan Isra'ila ta ce sojojinta sun kai jerin hare-hare a birnin Gaza na Falasɗinawa.

    Ba a bayar da rahoton asarar rayuka ba amma an samu lalacewar wasu kayayyaki, yayin da hukumar kashe gobara ta Isra'ila ta ce ta shawo kan gobarar da dama bayan ta ce Falaɗinawa sun harba mata balambalan mai ɗauke da wutar.

    An sake samun tashin hankali a Gaza, inda Falasdinawa suka ce za su ci gaba da abin da suka kira gagarumar turjiya har sai mahukuntan Isra'ila sun cire shingen da suka sanya wa yankin.

    Mutane da dama sun jikkata a rikicin da aka yi tsakanin bangarorin biyu a karshen mako.

  4. Cutar korona a Najeriya: 565 sun kamu, takwas sun rasu ranar Litinin

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 565 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Litinin.

    Rahoton hukumar ya nuna cewa an samu mutum takwas da cutar ta yi ajalin su har wa yau.

    A jihohi 14 ka samu sabbin mutanen da suka kamu a Litinin in. Su ne:

    • Lagos-205
    • Rivers-73
    • Ondo-63
    • FCT-53
    • Oyo-53
    • Ekiti-37
    • Delta-24
    • Edo-20
    • Benue-12
    • Bayelsa-6
    • Kwara-6
    • Osun-6
    • Ogun-5
    • Adamawa-2

    Jumillar mutanen da suka kamu da korona a Najeriya sun kai 187,588, sai kuma 168,818 da suka warke. Kazalika, akwai kuma mutum 2,276 da suka mutu.

  5. Barka

    Sannunmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa. Kuna tare da Umar Mikail a wannan hantsi na Talata.

    Ku biyo mu domin samun rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙotansu.