Sau 50 Boko Haram na kai mun hari ina tsira - Zulum

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Rufewa

    Masu bibbiyarmu a wannan shafin da hakan nake bankwana da ku a wannan shafin na labarai kai-tsaye, sai kuma gobe Laraba idan Allah ya kai mu. Umaymah Sani Abdulmumin ke cewa a kwana lafiya.

  2. Putin zai tallafawa ƴan fansho saboda hauhawan farashi

    Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanya hannu kan wasu dokoki da za su ba da damar a biya 'yan fanshon kasar wasu tsabar kudade cikin watan gobe, a daidai lokacin da ake gudanar da zaben majalisar kasar.

    Shugaban ya ce biyan kudaden - wadanda su ka kai dala dari da talatin ga kowane dan fansho - tallafi ne gare su saboda yadda hauhawar farashi ya shafi darajar kudaden fanshon da su ka saba karba.

    Mista Putin ya kuma yi wa sojoji da jami'an tsaron kasar alkawarin biyansu irin wadannan kudaden su ma.

    Wani binciken ra'ayin al'ummar kasar na cewa jam'iyyarsa ta United Russia, wato Dunkulalliyar Rasha, ba za ta taka rawar da ta taka ba a lokacin da aka yi babban zaben kasar na baya ba.

  3. Algeria ta yanke hulɗar diflomasiyya da Morocco

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Aljeriya ta yanke huldar diflomasiyya da Moroko, bayan da ta tuhumi makwabciyar ta ta da daukan abin da ta kira "matakan takalar fada". Ta ce za ta inganta tsaro a kan iyakar da ta raba kasashen biyu.

    Aljeriya ta tuhumi Moroko da alhakin tayar da gobarar dajin da ta halaka akalla mutum casa'in.

    Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta dade da yin tsami tsawon gomman shekaru, musamman kan mallakar yankin Yammacin Sahara wanda Moroko ke ikirarin yana cikin kasarta ne.

    Tun alif dari tara da casa'in da hudu aka kulle kan iyakokin kasashen.

  4. Taliban ta hana ƴan Afghanistan tafiya filin jirgin sama na Kabul

    Kungiyar Taliban ta ce daga yanzu ba za ta sake barin 'yan kasar Afghanistan damar shiga filin jirgin saman Kabul ba, kuma ta ce dalilinta shi ne na rashin tsaro a can.

    Taliban din ta kuma tari numfashin taron kolin kungiyar G7 ta kasashe masu karfin tattalin arziki, tana cewa zai yi wuya ta bari a matsa da ranar karshe ta kwashe dukkan 'yan kasar waje da ke son ficewa daga kasar, wanda ranar talatin da daya na wannan watan ne.

    A wani roko na musamman da su ka mika ga Amurka, kakakin Taliban Zabihullah Mujahid, ya roki kasar da ta daina jan hankulan 'yan kasar domin su yi kaura, yana cewa ana bukatar kwarewarsu domin gina kasar.

    Ya kara da cewa an bukaci mata su zauna a gida har zuwa lokacin da aka samar da tsare-tsare da za su tabbatar da za a iya kare lafiyarsu a wuraren aiki.

  5. An ceto mata 19 da aka yi safararsu zuwa Libya daga Najeriya

    Hukumar yaki da bautarwa da fataucin dan Adam a Najeirya ta NAPTIP ta sanar da ceto wasu mata ‘yan kasar 19 da aka yi safarar su zuwa Libya ta jamhuriyar Nijar.

    Hukumar ta NAPTIP ta sami wadan ta ceto su ne a jihar Katsina, sannan sun sami nasarar kama mutum 4 da ake zargin su da hannun a da fataucin mutane.

    Haka zalika yace hukumar tasu ta kuma ceto wasu yara 5 da shekarunsu basu fi 10 zuwa 11 ba da aka dauko su daga jihar Katsina zuwa Kaduna inda aka rarrabasu gidaje domin aikatau.

    A saurari rahoton Khalifa Shehu Dokaji daga Kano

    Bayanan sautiRahoton Khalifa Shehu Dokaji kan matan Najeriya da aka ceto daga Libya
  6. Direbobin gabashin Afirka na yajin aiki kan kashe-kashe a Sudan ta Kudu

    Sama da motoci dubu ɗaya a sassa gabashin Afirka sun daina ketare iyaka tsakanin Uganda da Sudan ta Kudu bayan direbobi sun shiga yajin aiki.

    Direbobin sun ce ba za su motsa ba, har sai gwamnatin Sudan ta Kudu ta alkawarta ba su kariya.

    Kenya ta dakatar da duk wani kai sako zuwa ƙasar bayan kisan matukan manyan motocinta biyu a wani harin kwantan-ɓauna a babban titin Sudan ta Kudun.

    Aƙalla ƴan kasuwa 30 da matukan manyan motoci 30 daga yankunan gabashin Afirka aka kashe a wannan shekarar a hanyar da ta hada iyaka tsakanin Uganda da birnin Juba na Sudan ta Kudu.

    Sudan ta Kudu dai har yanzu na farfadowa daga kazamin yakin basasa.

  7. Sojoji sun lashi takobin daukan fansa kan kashe da sace jami'ansu a NDA Kaduna

    Sojoji

    Asalin hoton, NDA

    Hedikwatar tsaro a Najeriya ta lashi takobin lalubo ƴan bindigar da suka kashe tare da sace wasu jami'an sojoji bayan wani hari da suka kaddamar a makantar soji ta NDA a Kaduna.

    Wasu mazauna gidajen da ke NDA sun tabbatar wa BBC Hausa cewa 'yan bindigar sun kashe sojoji biyu sannan suka sace guda ɗaya yayin harin da suka kai ranar Litinin da tsakar dare.

    Sanarwar da shugaban hafsoshin sojin Najeriya Janar Lucky Irabor ya fitar, ta mika sakon ta'azziya ga iyalan sojojin da aka kashe, sannan ya shaida cewa an sake inganta tsaro a makarantar da kewayenta.

    Sannan ya ce yanzu haka an bazama a wani samamen haɗin-gwiwa domin ceto sojan da aka sace da kuma kama ƴan bindigar.

    Sanarwar ta kuma shaida cewa nan gaba za a sake fito da wasu bayanai kan halin da ake ciki.

    Masu sharhi kan lamuran tsaro dai na ganin harin a matsayin wani abin kunya ga sojoji wadanda a baya, duk karfin halin dan bindiga, ba zai daddara ya kai musu hari ba.

    • 'Yan bindiga sun kai hari Makarantar Sojoji ta NDA, sun kashe mutum biyu
  8. Amurka ta musanta tallafawa ƴan tawayen Tigray

    Hukumar agaji ta Amurka ta musanta zargin da ake mata na taimawa ƴan tawayen Tigray da abinci a yankin arewacin Habasha.

    Wannan ya biyo bayan zargi da ake cewa tana taimakawa ƴan tawayen TPLF da abinci gina jiki ga iyaye mata da yara.

    Kafar yaɗa labarai Ethiopia ta rawaito a karshen mako cewa kwamandan TPLF da dakarun gwamnati suka cafke a yankin Amhara an ganshi yana cin biskit da USAid ke ba da wa agaji.

    USAid ta musanta zargin tana mai cewa babu mayaƙan da ta bai wa abinci da gangan, tare da jadada cewa mabukata take kai wa tallafinta.

  9. Sau 50 Boko Haram na kai mun hari ina tsira - Zulum

    Gwamna Zulum

    Asalin hoton, BORNOGOVT

    Gwamnan Borno Babagana Zulum ya shaida cewa sau 50 yana tsallake rijiya da baya daga hare-haren da mayakan Boko Haram ke kai masa.

    Gwamnan ya shaida hakan ne a lokacin wata tattaunawa da ƴan jarida a fadar gwamnatin Abuja bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari.

    Jaridar Daily Trust ta rawaito gwamnan na cewa sama da ƴan Borno dubu 100 aka kashe a rikicin Boko Haram na tsawon shekara 12.

    Sannan ya kuma shaida cewa akwai mayaƙa 2,600 da suka miƙa wuya, cikinsu akwai yara da matan mayaƙan da wasu iyalan tubabun mayaƙa.

    Ya ce cikin wadanda suka miƙa-wuya akwai mutanen da aka tilastawa ɗaukan makami, wasu kuma yara ne da basu mallaki hankalinsu ba.

    Gwamna Zulum ya ce gwamnatin Borno ba ta da niyyar bai wa tubabun mayaƙan sisin kobo da sunan samun bayanai kan sauran mayaƙa.

    Gwamnan ya ce ya tattaunawa da Shugaba Buhari kan mayaƙan da suka tuba, kuma ya ce shi bai ga wani dalili na ƙin karban mayaƙan da suka miƙa-wuya ba.

    Ana yi ta ce-ce-ku-ce dai kan tubabun mayaƙan da su ka roki gaffara. Akwai masu ganin ya kamata a yafe musu, wasu kuma na cewa a gurfanar da su.

  10. Amnesty ta ce IS da Al Qaeda reshen Afirka na amfani ne da makaman da aka ƙera a Turai

    Wani bincike da kungiyar Amnesty International ta wallafa a ranar Talata ya bayyana cewa kungiyar IS reshen yankin Sahel da kuma ta JNIM da ake dangantawa da al-Qaeda na amfani ne da makaman da aka kera a nahiyar Turai, musaman ma a Serbia.

    Haka nan kungiyar ta Amnesty ta ce su ma kungiyoyin 'yan bindigamasu mara baya ga gwamnati na amfani da irin wadannan makamai.

    A cewar rahoton ƙungiyoyin na kwasar ganimar makamai ne na dakarun gwamnati lokacin da suka kai hari sansanoninsu ko kuma suka kashe sojoji a fagen daga.

    Sanarwar ta ce har da mayaƙan sa-kai masu goyon bayan gwamnati kamar Dan na Ambassagou a Mali na amfani da makamain da kuma mayakan VDP na Burkina Faso.

    Amnesty ta ce ta tanance hotuna da bidiyo sama da 400 da ƙungiyar Daesh da Al Qaeda reshen Afirka suka yaɗa.

    Ta ce yawancin makaman da aka nuna bindigogi ne ƙirar Kalashnikovs zamanin tsohuwar Daular Soviet, akwai kuma sabbi da mayaƙan ke amfani da su da wani kamfanin makamai na ƙasar Serbia ya ƙera.

    Amnesty ta kuma ce Faransa da Slovakia da Jamhuriyyar Czech suna shigar da makamai a yankin Sahel are da yin kira ga ƙasashen da kuma gwamnatocin yankin Sahel su saka ido kan yadda ake amfani da su.

  11. “Ƴan bindiga sun sace mutum 120 a ƙauyenmu”

    Mazauna garin Goran Namaye da ke jihar Zamfara sun ce yanzu adadin wadanda 'yan bindiga suka sace daga garin ya kai mutum 120.

    Da farko 'yan sanda sun ce mutum hudu ne aka kashe kuma aka sace wasu 50 a harin da masu garkuwa da mutane suka kai garin da tsakar daren ranar Lahadi.

    Wannan na zuwa ne yayin da a jiya, mazauna garin Kurar Mota inda a watannin bayan aka kashe 'yan sanda 13, suka ce maharan sun sake shiga garin cikin daren ranar Litinin.

    Ƴan bindiga masu saar mutane domin kuɗin fansa sun addabi jihar Zamfara, inda har yanzu suke garkuwa da ɗaliban Kwalejin noma ta Bakura da suka sace.

    Ku saurari rahoton Haruna Shehu Tangaza:

    Bayanan sauti“Ƴan bindiga sun sace mutum 120 a ƙauyenmu”
  12. Sarkin Naruhito ya ƙaddamar da gasar nakasassu ta Paralympics

    Sarkin Naruhito na Japan ya bude wasannin Olympics ta masu lalurar nakasa, wato 2020 Paralympic a wani biki da ya gudana a birnin Tokyo.

    Tokyo ya kasance birni na farko a duniya da ya taɓa karbar bakuncin wasannin Paralympics har sau biyu. Ya taba karbar bakuncin wasannin da aka yi a 1964.

    Ana sa ran 'yan wasa fiye da 4,000 daga kasashe fiye da 160 za su fafata da juna cikin kwana 14 masu zuwa.

    Sai dai ilahirin filayen wasanni za su kasance babu 'yan kallo saboda annobar korona.

    Wani wakilin BBC ya ce cutar korona ta kara yaduwa a Tokyo cikin makonnin da su ka gabata, har ta kai ga asibitoci na kukan rashin isassun gadaje a dakunan kula da masu cutar.

  13. Sabon Shugaban Zambia Hakainde Hichilema ya sha rantsuwar kama aiki

    Hakainde Hichilema

    Asalin hoton, ZNBC TV1

    Sabon Shugaban Ƙasar Zambia Hakainde Hichilema ya sha rantsuwar kama aiki a gaban dubban magoya baya da suka taru a Filin Wasa na Heroes da ke Lusaka babban birnin ƙasar.

    Mataimakiyarsa Mutale Nalumango ta zama mace ta farko da ta riƙe muƙamin a Zambia.

    Sabon shugaban wanda ya yi nasara kan ɗan hamayya Edgar Lungu da ƙaramin rinjaye a watan da ya gabata, ya ce dole rayuwarsu ta gaba ta fuskanci ƙalubale amma ya ce za su farfaɗo da tattalin arziki.

    Ya yi wa 'yan Zambia alƙawarin samar da ingantaccen abinci a kowace rana. "Babu wani ɗan Zambia da ya kamata ya kwana da yunwa," in ji shi.

  14. Taliban: Ƙasashe huɗu za su sasanta rikicin Afghanistan

    Taliban

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasashen Rasha da China da Amurka da Pakistan na sha'awar su shiga tsakani wajen sasanta rikicin Afghanistan bayan Taliban ta ƙwace iko da ƙasar, a cewar Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov.

    A lokaci guda kuma, Mista Lavrov ya ce Rasha na adawa da tura 'yan gudun hijirar Afghanistan ɗin zuwa tsofaffin ƙasashen Tarayyar Soviet da ke yankin Tsakiyar Asiya ko kuma tura sojojin Amurka.

    A ƙarshen makon da ya gabata Shugaban Rasha Vladmir Putin ya soki Amurka da Turai game da tsugunar da 'yan Afghanistan a ƙasashe ƙawayen Rasha ba tare da biza ba kafin a gama nema musu bizar Amurkar.

    Wasu mayaƙa ƙarƙashin ƙungiyar National Resistance Front of Afghanistan (NRF) sun sha alwashin yaƙar Taliban duk da cewa za su nemi tattaunawar sulhu tukunna.

    Ya zuwa yanzu, an kwashe kusan mutum 50,000 daga ƙasar yayin da Taliban ke shirin kafa gwamnatin Musulunci a Afghanistan.

  15. An tsige kakakin Majalisar Jihar Kebbi da mataimakinsa

    Kebbi

    Asalin hoton, @IsmailaKamba

    'Yan majalisa a Jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya sun sauke kakakin majalisar, Ismaila Abdulmummuni Kamba da mataimakinsa Muhammadu Buhari Aliyu, daga muƙamansu.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa 24 daga cikin 'yan majalisar sun aminta da matakin tsige shugabannin.

    An rantsar da Muhammad Abubakar Lolo - ɗan majalisa mai wakiltar Bagudo ta Yamma - a matsayin sabon kakakin majalisar.

    Kazalika, Mohammed Usman Zuru mai wakiltar mazaɓar Zuru aka rantsar matsayin mataimakinsa.

  16. Labarai cikin minti ɗaya

    Bayanan sautiMinti Ɗaya da BBC na Rana 24/08/2021
    • Wasu 'yan bindiga sun kai hari Makarantar Horon Sojoji ta Nigeria Defence Academy, NDA, da ke birnin Kaduna a arewacin Najeriya. Mazauna gidajen da ke NDA sun tabbatar wa BBC cewa 'yan bindigar sun kashe sojoji biyu sannan suka sace daya yayin harin da suka kai ranar Litinin da tsakar dare.
    • Tsohon Shugaban Chadi Hissene Habre ya rasu ranar Talata yana da shekara 79, kamar yadda Ministan Shari'a na Senegal, Malick Sall ya bayyana. Mista Habre wanda ke zaman ɗaurin rai-da-rai a Senegal bisa aikata laifukan yaƙi a ƙasarsa, ya rasu ne a asibiti, inda wata kafar yaɗa labarai ta Senegal ta ce ya rasu ne sakamakon cutar korona.
    • Dubban mutane da ke son ficewa daga Afghanistan na can danƙam a kusa da filin jirgi na Kabul babban birnin Afghanistan. Aƙalla mutum 20 ne suka mutu sakamakon harbe-harbe da kuma turmutsitsi tun daga makon da ya gabata, yayin da aka kwashe mutum fiye da 10,000 a ranar Litinin kaɗai.
    • Arsenal za ta saurari duk wani tayi da za a yi wa kyaftin dinta Pierre-Emerick Aubameyang mai shekara 32.
  17. Labarai da dumi-dumi, Tsohon Shugaban Chadi Hissene Habre ya rasu

    Tsohon Shugaban Chadi Hissene Habre ya rasu ranar Talata yana da shekara 79, a cewar Ministan Shari'a na Senegal, Malick Sall.

    Mista Habre ya rasu ne a asibiti yayin da yake zaman gidan yari a Senegal bisa aikata laifukan yaƙi da kuma lalata rayuwar 'yan Adam.

    Wata kafar yaɗa labarai ta Senegal ta ce ya rasu ne sakamakon cutar korona, kamar yadda kamfanin labarai na AFP ya ruwaito.

    A lokacin da ya mulki Chadi tsawon shekara takwas, shugaban ya dinga murƙushe 'yan adawa, abin da ya jawo mutuwar mutum fiye da 40,000, a cewar masu bincike.

    A shekarar 2016 ne wata kotu ta musamman - wadda ƙungiyar haɗin kan Afirka (AU) da Senegal suka kafa - ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai.

  18. Ana fargabar akwai 'yan Taliban cikin 'yan Afghanistan da Faransa ta ɗiba

    Kabul

    Asalin hoton, Reuters

    Ana saka ido kan wasu 'yan Afghanistan biyar da aka kwaso daga ƙasar zuwa Faransa bisa zargin suna da alaƙa da ƙungiyar Taliban, kamar yadda ministan harkokin cikin gida ya bayyana.

    Gerald Darmanin ya faɗa wa gidan rediyon Franceinfo cewa daga cikin mutum 1,000 ko fiye da haka da aka ɗebo daga Afghanistan, "ɗaya daga ciki ana tunanin - na maimaita cewa ana tunani - yana da alaƙa da Taliban".

    "Amma ya taimaka wa sojojin Faransa da 'yan jarida," in ji Mista Darmanin. "Muna saka ido kansa shi da abokansa bayan sun shigo Faransa don kawar da duk wani shakku."

    Ya ce ɗaya daga cikin mutanen ya fice daga wurin da aka tanadar musu: "An tsare shi a jiya (Litinin) abin da ke nuna cewa jami'an tsaro na sa ido a kansu sosai."

    Kamfanin labarai na AFP ya ruwaito cewa wasu bayanai na gwamnati sun nuna mutumin ya amsa cewa shi sojan Taliban ne, inda ya shugabanci wani wurin duba ababen hawa a Afghanistan.

  19. Ban yanke shawara kan takarar shugaban ƙasa ba tukunna - Osinbajo

    Osinbajo

    Asalin hoton, State House

    Ofishin Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce sam ba shi da masaniya kan hotunan da ke yawo a wasu sassan kasar na bayyana aniyar tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin shugaban, Laolu Akande ya fitar, ofishin ya ce Osinbajo bai yanke shawarar tsayawa takara ba tukunna.

    "Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ba shi da hannu ko kaɗan wajen rarraba fastar takarar 2023 walau a kan tituna ko kuma a intanet da shafukan zumunta," a cewar sanarwar.

    "Wannan yunƙurin karkatar da hankula ne daga shugabancin ƙasarmu wanda ba a buƙata a yanzu."

    Kwana biyu da suka gabata ne wasu hotuna suka karaɗe biranen Kano da Abuja ɗauke da Yemi Osinbajo da Gwmnan Kano Abdullahi Ganduje a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa.

    Siyasa

    Asalin hoton, Other

  20. Jami'ar Jos: Jihar Kebbi ta tallafa wa ɗalibanta da naira miliyan biyar

    Jami'ar Jos

    Asalin hoton, Other

    Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu ya ware naira miliyan biyar domin tallafa wa ɗalibai 'yan asalin jihar 95 da ke karatu a Jami'ar Jos ta Jihar Filato a arewacin Najeriya.

    Babbar Sakatariya a Ma'aikatar Ilimi Mai Zurfi Hajiya Halima Boyi-Dikko ce ta bayyana hakan ranar Litinin, tana mai cewa matakin ya zo daidai da lokacin da ɗaliban ke buƙatar taimako.

    Tun a makon da ya gabata ne jami'ar ta dakatar da ayyukan karatu sannan ta rufe makarantar saboda dalilai na tsaro biyo bayan kashe-kashen mutane da aka aikata a kusa da jami'ar.

    A ranar 14 ga watan Agusta ne wasu matasa da ake zargin 'yan ƙabilar Irigwe ne suka tare wa wasu matafiya Musulmai hanya suka kashe 27 daga ciki sannan suka raunata wasu da yawa yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Jihar Ondo daga Bauchi.

    Wasu jihohi da dama sun kwashe ɗalibansu daga jami'ar biyo bayan matakin rufe ta da hukumomi suka ɗauka.

    Saboda gudun abin da ka iya biyo baya, gwamnatin Filato ta saka dokar hana fita a ƙananan hukumomi uku na Jos tsawon awa 24, kodayake an sassauta daga baya.