'Yan sanda sun kama wani mutum dauke da AK-47 guda 53 a Jihar Nasarawa

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Ina fargabar za a ci gaba da rasa rayuka a Afghanistan - Joe Biden

    Joe Biden

    Asalin hoton, AFP

    Shugaba Joe Biden na Amurka ya ce yana fargabar za a sake samun asarar rayuka a yunkurin da kasarsa ke yi na kwashe Amurkawa da 'yan Afghanistan da suka yi musu aiki.

    Sai dai ya ce duk da haka za su dage su ga sun kammala aikin jigilar nan da kwana 10 kamar yadda aka tsara.

    Wakiliyar BBC ta ce wasu ƙawayen Amurka sun soki Joe Biden kan yadda ya yi gaggawar kwashe sojojin kasar daga Afghanistan, amma a martaninsa ya ce babu wanda ya fi su sanin abin da ya kamata su yi.

    Rahotanni sun ce jiragen sojin Amurka uku sun ɗauki wasu Amurkawa a wajen filin jirgin saman Kabul, wadanda turmutsutsi bai bari sun shiga filin jirgin ba.

  2. Korona a Najeriya: Mutum uku sun rasu, 304 sun kamu ranar Juma'a

    Buhari

    Asalin hoton, State House

    Mutum 304 ne suka harbu da cutar korona a Najeriya ranar Juma'a da kuma uku da suka rasu, a cewar hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta ƙasar.

    Rahoton da NCDC ta wallafa ya nuna cewa mutanen sun fito ne daga jiha 13 ciki har da Abuja babban birnin ƙasar.

    Jihohin su ne:

    • Rivers (154)
    • Ekiti (33)
    • Edo (20)
    • Abuja (18)
    • Oyo (17)
    • Cross River (15)
    • Delta (15)
    • Akwa Ibom (13)
    • Ogun (11)
    • Bayelsa (4)
    • Sokoto (2)
    • Gombe (1)
    • Nasarawa (1)

    Ya zuwa yanz, jumillar mutum 185,571 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya, ta kashe mutum 2,247. An sallami 168,124 bayan sun warke.

  3. Barkanmu da hantsi

    Maraba da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye.

    Ku biyo ni Umar Mikail domin samun rahotannin abubuan da ke faruwa a sassan diniya daban-daban.

    Sai dai za mu fi mayar da hankali kan Nijar da Kamaru da Ghana da Najeriya.