'Yan sanda sun kama wani mutum dauke da AK-47 guda 53 a Jihar Nasarawa

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe Idan Allah Ya kai mu

  2. Putin da Erdogan sun tattauna ta wayar tarho kan Afghanistan

    BBC

    Shugaban Rasha Vladimir Putin da na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan sun tattauna halin da ake ciki a Afghanistan ta wayar tarho.

    "Sabuwar gwamnatin Afghanistan dole ta hada kowa da kuma tabbatar da kowa ya samu wakilci cikinta daga mutanen Afghanistan... kamar yadda Erdogan ya shaida wa Putin.

    Shugabannin kasashen biyu sun dauki gabarar mayar da yaki da ta'addanci a Afghanistan a matsayin abin da suka sa gaba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato fadar Kremlin ta na fadi.

    Shugabannin sun kuma tattauna kan yadda za a ci gaba da tafiyar da filin jirgin Kabul.

  3. Muna samun ci gaba a shirinmu na kafa gwamnati - Taliban

    REUTERS

    Asalin hoton, REUTERS

    Ƴan Taliban sun ce sun samu ci gaba a shirinsu na haɗa sabuwar gwamnati a Afghanistan tun bayan ƙwace Kabul, babban birnin ƙasar a ƙarshen makon da ya gabata.

    Shugaban ɓangaren siyasa na ƙungiyar, Mullah Abdul Ghani Baradar ya isa Kabul don tattaunawa, wadda ake sa rai za ta ƙunshi kwamandojin ƴan bindigar da tsoffin shugabannin gwamnati da malaman addini.

    Ƙungiyar Taliban ta yi alƙawari kafa gwamnatin kowa da kowa a Afghanistan amma mutane da yawa na tantama kan hakan

    Sauran Shugabannin Taliban da ke Kabul sun ƙunshi Khalil Haqqani na ƙungiyar Haqqani kuma ɗaya daga cikin ƴan ta'adda na duniya da Amurka ke nema ruwa a jallo.

  4. Ƙarin kwamandojinTaliban sun isa Afghanistan

    Facebook

    Asalin hoton, Facebook

    Wasu manyan shugabannin Taliban sun isa birnin Kabul daga Doha babban birnin Qatar, inda nan ne tawagar da za ta yi tattaunawar sulhu da jami'an Amurka suka hadu.

    Daya daga cikin manyan 'yan siyasar Afghanistan Abdallah Abdallah ne ya wallafa a shafinsa na Facebook inda hoton da ya sa ya nuna yana gaidar da tsohon jakadan Talibana a Saudiyya Shahabuddin Delawar, da tsohon ministan cikin gida na Taliban Mullah Khairullah Khairkhwa, da kuma Abdul Salam Hanafi da dai sauransu.

    Wasu karin hotunan sun nuna wasu mutane na tattauna wa da Hamid Karzai wanda ya shugabanci Afghanistan daga 2001 zuwa 2014 wanda ke cikin Kabul lokacin da Taliban suka kwace mulki.

    Bayanin da aka wallafa a Facebook din ya ce "halin da ake ciki kenan a wannan kasa, jami'an tsaro, aiki da duka bangarorin siyasa mutunta ikon kasa, martaba turarta duka na cikin maganganun da ake tattauna wa."

    Taliban ta ce za ta kafa gwamnatin da za ta tafi da kowa, amma masu lura da al'amura na dari-darin hakan.

  5. Amurka ta ce 'yan kasarta su ƙauracewa filin jirgin saman Kabul

    BBC

    Amurka ta ce wa ƴan ƙasarta su guji zuwa filin jirgin sama na Kabul saboda barazanar tsaro a wajen ƙofar shiga filin.

    Jami'ai a ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon sun ce gargaɗin na da muhimmanci saboda halin rashin tabbas ɗin da ake fuskanta a wajen filin jirgin.

    Wani wakilin BBC ya ce rikicin da ke gudana a wurin ya ƙara rurucewa inda dubban mutane ke tsananin son su fice daga Afghanistan.

    Mai magana da yawun Pentagon ya ce Amurka na aiki tuƙuru don ganin ta fitar da mutane daga Afghanistan, inda aka kwashe kusan mutum dubu huɗu a sa'o'i ashirin da huɗu da suka gabata.

    Ya ce kawo yanzu mutum dubu goma sha bakwai aka kwashe daga Kabul kawo yanzu tun bayan da Taliban ta ƙwace Kabul, ciki kuwa har da Amurkawa dubu biyu da ɗari biyar.

  6. Chadi ta kwashe rabin dakarunta da ke yaƙi da masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin Chadi ta ce ta kwashe rabin dakarunta da ke yaki da masu ikirarin jihadi da ta girke a yankin Sahel.

    Tun 2017, Chadi ta bayar da gudun muwar dakaru 1,200 ga dakarun kasashen G5 na yankin Sahel.

    Duk da tarzomar da ke kara kamari a yakin Faransa ta sanar da rage yawan sojojinta daga 5,000 zuwa 3,000.

    Kakakin sojin Chadi ya ce janye sojin wani salon yaki ne, kuma kasar ba wai ja da baya za ta yi ba a yakin da ake yi da kungiyoyin jihadi.

    Cikin kasashe biyar da suka hada dakarun G5 Sahel, ana yi wa dakarun Chadi kallan mazan fama wadanda suka iya aiki.

    Kudurin yankin na fama da koma baya ne saboda kalubalen kayan aiki.

    Sai dai wannan matakin ya zo ne lokacin da yankin ke cikin damuwa.

  7. Tattauna wa ta musamman da Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Bayero

    Bayanan sautiGane Mani Hanya Da Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero

    A yau Asabar ne ake bikin mika sanda ga sarkin Bichi na biyu mai martaba Alhaji Nasiru Ado Bayero wanda ya hau karagar mulki a watan Maris din Shekarar 2020.

    Albarkacin wannan bikin na yau, BBC ta yi hira ta musamman da sarkin, wanda ya tabo batutuwa da dama ciki harda yadda masarautarsa ta fara tattaunawa da masu zuba jari domin samar da lantarki mai amfani da hasken rana, da kuma inganta babbar kasuwar hatsi ta Dawanau wadda itace mafi girma a yammacin Afirka.

    A filin Gane Mini Hanya na wannan makon, wakilinmu na Kano Khalifa Shehu Dokaji ya fara da tambayar sarkin yadda yaji da wannan ranar ta karbar sanda.

  8. Allegri ya ce Ronaldo bai taba cewar zai bar Juventus ba

    REUTERS

    Asalin hoton, REUTERS

    Cristiano Ronaldo "bai taba nuna alamar zai bar'' Juventus ba in ji kocin kungiyar Massimiliano Allegri.

    A makon nan Ronaldo ya yi rubutu a kafar sa ta sada zumunta cewar rade-radin da ake kan zai bar Juventus ''rashin girmamawa ce a kanshi da kuma a matakin sa na dan kwallo.''

    A wata hira da kocin Juventus, Allegri ya ce kyaftin din tawagar Portugal zai ci gaba da taka leda a Turin.

    "Ronaldo bai taba nuna alamar zai barmu ba,'' ya fada min cewar zai ci gaba da taka leda a Juventus in ji Allegri.

    Ranar Lahadi Juventus za ta ziyarci Udinese a wasan makon farko a gasar Serie A kakar 2021-22.

    Ana ta yada jita-jitar cewar Ronaldo zai bar Juventus a bana, wasu rahotannin sun ce zai koma taka leda Real Madrid ko Paris St-Germain ko kuma Manchester City.

  9. 'Yan sanda sun kama wani mutum dauke da AK-47 guda 53 a Jihar Nasarawa

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Nasarawa ta ce ta kama wani matashi mai suna Abubakar dan shekara 35 dauke da bindiga kirar AK-47 guda 53 da kuma harsasai 260 wanda ba a san inda ya nufa da su ba.

    Kakakin rundunar ASP Ramhan Nansel, ne ya bayyana wa jaridar The PUNCHhakan a ranar Asabar.

    Ya kara da cewa jami'ansu da ke aiki a karamar hukumar Akwanga ne suka samu nasarar kama mutumin.

    Kakakin ya kara da cewa wata mota kirar Toyota Camry da aka sace a New Nyanya mai lambar Abuja 267 EU ita ma an yi nasarar kamata.

  10. Dole yara mata su ci gaba da neman ilimi a Afghanistan- Unicef

    EPA

    Asalin hoton, EPA

    Lokacin da Taliban ta yi shugabanci a baya a Afghanistan, sun dakatar da karatun duk wata mace da ta haura shekara 10 a kasar.

    Cikin sama da shekara 20 da suka mulki kasar a baya, kungiyoyin agaji da manyan kasashen yamma sun ta zuba jari a harkar koyo da koyarwa a Afghanistan har zuwa yau.

    A yanzu kuma an shiga fargabar cewa tun da sun dawo za su iya kara haramta neman ilimin yara mata a kasar.

    BBC ta tattauna da mai magana da yawun Asusun ba da Tallafin na Majalisar Dinkin Duniya a Afghansitan Sam Mort.

    ta ce duk ta cewa yanayin wajen na kara zama wani barazana, kungiyarsu ta sanya hanna kan wani shri da Taliban a wajan Disambar da ya gabata, domin fadada damar samun ilimin mata a yankunansu.

  11. Buhari ya yi kira ga shugabanni su hada kan al'umma

    Buhari Sallau

    Asalin hoton, Buhari Sallau

    Shugabannan Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabannin masu tasowa da su yi amfani da ikonsu su dakile rarrabuwar kai tare da tabbatar da hadin kan al'umma.

    Buhari ya yi wannan kiran ne a ranar Asabar yayin bikin bayar da sandar girma ga sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero.

    Buhari ya yi kira ga Sarkin dada ya yi koyi da mahaifinsaa Alhaji Ado Bayero, wajen shugbanci na buga misali da kuma tabbatar da hadin kai da kuma dorewar Najeriya.

    Shugaba Buhari dai ya samu wakilcin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari ne.

    Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayar ga sandar girman ga sarkin Bichi Alahaji Nasiru Ado Bayero.

  12. Ethiopia na shirin samarwa Facebook kishiya

    AP

    Asalin hoton, AP

    Habasha ta ce za ta samar da tata manhajar sada zumunta bayan da ta yi zargin kafafen sada zumunta irin su Facebook da yin abin da bai yi daidai ba da muradanta.

    Daraktan gwamnati na bangaren hukumar yada labarai da tsaro ta kasar Shumete Gizaw ne ya bayyana hakan, yana cewa kafafen sadarwa irin su Facebook da Twitter sun fara zama abubuwan da 'yan siyasa ke amfani da su domin yakar gwamnati.

    Ya kuma soki batun cewa an rufe wasu shafuka an kuma goge wasu walllafe-wallafe.

    Gabanin zaben da aka yi a watan Yuni, Facebook ya ce ya goge wani asusu na bogi wadanda aka ce suna da alaka da hukumomin gwamnati da suke da alhakin sanya ido kan harkokin sadarwa a intanet.

    Mista Shumete ya ce Habasha na kokarin samar da kafafen sadarwa da ake aike sako da su irinsu WhatsApp da na yin taro ta bidiyo kamar su Zoom.

  13. 'Tarayyar Turai ba za ta amince da gwamnatin Taliban ba'

    Ursula von der Leyen

    Asalin hoton, @vonderleyen

    Ƙungiyar Tarayyar Turai ta European Union (EU) ba ta amince da gwamnatin Taliban ba a Afghanistan kuma ba za ta yi wata tattaunawar siyasa da ita ba, a cewar shugabar ƙungiyar Ursula von der Leyen.

    Shugabar ta bayyana hakan ne yayin da ta kai ziyara wani sansanin da aka sauke ma'aikatan EU a birnin Madrid da aka kwaso daga birnin Kabul.

    Ana ta kwashe mutane daga Afghanistan biyo bayan ƙwace mulki da Taliban ta yi makon da ya gabata, wadda ta ce bisa tsarin Shari'ar Musulunci za ta gudanar da gwamnatinta.

    Von der Leyen ta ce za ta buƙaci a ƙara yawan kuɗin tallafin da EU ta ware wa Afghanistan na yuro miliyan 57 a wannan shekarar.

  14. Masu iƙirarin jihadi sun kashe mutum 17 a Nijar

    Sojojin Nijar

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga yammacin Jamhuriyar Nijar na cewa 'yan bindiga masu iƙirarin jihadi sun kashe aƙalla mutum 17.

    Wani ɗan majalisa daga yankin Tillaberi ya bayyana cewa maharan sun kai wa mutanen hari ne a garin Thiam suna tsaka da sallah a yammacin Juma'a.

    A farkon makon nan masu iƙirarin jihadi sun kashe mutum 37 a yankin na Tillaberi da ke kusa da iyakar Mali da Burkina Faso.

    Ɗan majalisar ya ƙara da cewa an kashe mutum fiye da 100 a watan da ya gabata, ciki har da 'yan sanda a yankin.

    Yayin da mutane ke tsoron zuwa gonakinsu, ana gargaɗin cewa iyalai da yawa za su shiga ƙarancin abinci.

  15. Jami'ar Jos ta rufe makarantar saboda matsalar tsaro

    Jami'ar Jos ta rufe makarantar saboda matsalar tsaro

    Asalin hoton, University of Jos

    Hukumar Jami'ar Jos ta dakatar da ayyukan karatu tare da rufe ta baki ɗaya saboda kisan ɗalibai da ke ƙaruwa a kusa da makarantar" jim kaɗan bayan sassauta dokar hana fita da aka saka.

    A cewar wata sanarwa da Rajistira Monday Danjem ya sanya wa hannu, an umarci dukkan ɗalibai da su koma gida ko kuma wani wuri mai kwanciyar hankali har sai hankula sun kwanta.

    Kazalika, hukumar makarantar ta dakatar da jarrabawar da ta shirya farawa ta shekarar karatu ta 2019/2020.

    Matakin jami'ar ya biyo bayan kisan wasu matafiya Musulmai 27 da ake zargin matasan ƙabilar Irigwe da aikatawa ranar Asabar da ta gabata a kan hanyar Rukuba da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.

    Lamarin ya jawo gwamnatin jihar ta saka dokar hana fita a ƙananan hukumomin Jos ta Arewa da Bassa.

  16. Taliban: 'Ƙasashe 12 sun amince su karɓi masu tserewa daga Afghanistan'

    Kabul

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce ƙasashe 12 ne zuwa yanzu suka amince su karɓi 'yan gudun hijirar da ake kwasowa daga Afghanistan.

    Wasu ƙasashe 12 sun amince su zama wurin yin zango ga masu guduwa daga ƙasar, ciki har da Amurkawa da sauransu.

    Blinken ya faɗa cikin wata sanarwa cewa 'yan gudun hijirar Afghanistan da ba a gama tantance su ba domin zama a Amurka za a ajiye su ne a ƙasashen: Albania, Canada, Colombia, Costa Rica, Chile, Kosovo, North Macedonia, Mexico, Poland, Qatar, Rwanda, Ukraine da Uganda.

    Ƙasashen da mutanen za su dinga yin zango kuwa su ne: Bahrain, Birtaniya, Denmark, Jamus, Italiya, Kazakhstan, Kuwait, Qatar, Tajikistan, Turkiyya, Daular Larabawa (UAE), Uzbekistan.

  17. Taliban: Italiya ta kwashe mutum 1,000 daga Afghanistan

    Kabul

    Asalin hoton, Getty Images

    Italiya ta ce dakarun sojanta sun kwashe 'yan ƙasar Afghanistan kusan mutum 1,000 daga birnin Kabul cikin kwana biyar da suka wuce.

    Ma'aikatar Tsaron Italiya ta ce jirgi biyu ɗauke da mutum 207 sun isa birnin Rome daga Kuwait, wurin da ƙasar ke sauke mutanen da ta ɗebo daga Kabul.

    Ƙasar ta aika ma'aikata fiye da 1,500 domin aikin kwaso mutane daga Kabul zuwa Kuwait sannan kuma a kai su Italiya daga baya.

    Kwana shida kenan tun bayan da ƙungiyar Taliban ta sake ƙwace iko da Afghanistan, abin da ya sa ƙasashe ke rububin kwashe mutanensu da kuma wasu 'yan Afghanistan ɗin.

    Taliban ta ce tsarin Shari'ar Musulunci za ta bi wajen gudanar da mulkinta.

  18. 'Yan fashi sun sace 'mutum 60' a Jihar Zamfara

    'Yan fashin daji

    Asalin hoton, Daily Trust

    Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashi ne sun yi garkuwa da gwamman mutane bayan wani hari da suka kai a ƙauyen Rimi da ke Ƙaramar Hukumar Bakura ta Jihar Zamfara ranar Juma'a.

    Kwamishinan Yaɗa Labarai Ibrahim Dosara ya tabbatar da kai harin, yana mai cewa kusan mutum 60 ne 'yan bindigar suka sace, amma ya ce ba a tabbatar da adadin ba tukunna.

    "A safiyar yau [Juma'a] mun tashi da labarin cewa 'yan fashi sun afka wa ƙauyen Rimi sun sace mutum 60, duk da cewa ba a tabbatar ba," kamar yadda ya faɗa wa gidan talabijin na TVC.

    Ya ƙara da cewa "jami'an tsaro da na gwamnati na ƙoƙarin tabbatar da ainahin adadin mutanen da kuma waɗanda aka ji wa rauni".

    "[Garin] Bakura hanyar ɓarayi ce wadda ta dangane da Dansadau zuwa Birnin Gwari [a Jihar Kaduna] da kuma wasu sassa na Jihar Neja," a cewarsa.

    A ranar Litinin da ta gabata wasu 'yan fashin suka sace ɗalibai da malami da kuma iyalan malamin daga kwalejin harkokin noma ta garin na Bakura.

  19. An fara bikin bai wa sarkin Bichi sandar girma

    Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III
    Bayanan hoto, Sarkin Musulmi Mai Alfarma Sa'ad Abubakar III

    A yau Asabar za a bai wa Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar girma kwana ɗaya bayan ya ƙulla surukuta da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

    Sarkin Kano Aminu Ado Bayero
    Bayanan hoto, Sarkin Kano Aminu Ado Bayero

    Tuni aka fara bikin wanda zai gudana a Masarautar Bichi da ke Jihar Kano, inda ya samu halartar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III.

    Sarkin Zazzau Ahmad Nuhu Bamalli
    Bayanan hoto, Sarkin Zazzau Ahmad Nuhu Bamalli

    Kazalika, Sarkin Kano Aminu Ado Bayero - wanda ɗan uwan sarkin Bichi ne - yana halartar bikin bayan rashin halartar ɗaurin Zarah Nasir Bayero da kuma Yusuf Buhari ranar Juma'a.

    Shehun Borno Abubakar Ibn Umar Garbai
    Bayanan hoto, Shehun Borno Abubakar Ibn Umar Garbai
  20. Sojojin Najeriya sun kama 'mai yi wa Boko Haram safarar taki'

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Rundunar sojan Najeriya ta ce dakarunta sun kama wani mutum da ake zargi da yi wa ƙungiyar Boko Haram safarar takin zamani.

    Dakarun na rundunar Operation Hadin Kai sun cafke Yusuf Saleh ne ranar Juma'a a ƙauyen Bayamari da ke Ƙaramar Hukumar Geidam ta Jihar Yobe, a cewar wata sanarwa daga kakakin rundunar.

    Birgediya Janar Onyema Nwachukwu.ya ce an kama mutumin ɗauke da buhu 38 na takin zamani mai nauyin kilogiram 50 kowanne ɗaya bayan an tsegunta musu.

    Tuni gwamnati ta haramta amfani da takin zamani na Urea saboda yadda 'yan bindiga ke amfani da shi wajen haɗa abubuwan fashewa.

    Mista Nwachukwu ya ce wanda ake zargin yana ba su muhimman bayanai yayin da suke ci gaba da bincike.