Muzaharar ƴan Shi’a ta haifar da hatsaniya a Sokoto

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Awwal Ahmad Janyau

  1. Labarai da dumi-dumi, Mutum 12 sun mutu a filin jirgin Kabul

    Kungiyar Taliban ta ce mutum 12 ne suka mutu a filin jirgin saman Kabul tun daga ranar Lahadi.

    Wani jami'i da ya yi magana da kamfanin dillancin Labarai na Reuters a boye, ya ce mutanen sun mutu ne dalilin turmutsutsu ko kuma an harbe su ne.

    Ya bai wa taron mutanen da suka yi dandanzo a filin jirgin shawarar su koma gida tun da ba su da jirgin da zai kai su inda suke so, ya kuma ce "Taliban ba su cutar da ko wa ba a filin jirgin."

    An ta samun rahotannin rikici a filin jirgin lokacin da dubban mutane ke kokarin tsere wa daga kasar.

    Har yanzu filin jirgin saman Kabul na karkashin ikon Amurka, sai dai duka titunan yankin a zagaye suke da dakarun Taliban.

  2. An yanke hukuncin sharar masallaci ga mutumin da ya saci Kur'ani a Kano

    BBC

    Wata kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a unguwar Fagge 'Yan Alluna ta yanke wa wani mutum hukuncin sharar masallacin Juma'a na unguwar Fagge na kwana 30 a jere saboda satar kur'anai takwas da ya yi.

    Halifa Abdullahi wanda mazaunin unguwar Yola a Kano, wanda aka zarga da fasa tagar masallacin Tudun Maliki a daren Lahadi tare da kwashe kur'ani mai tsarki guda takwas.

    Masu gadin masallacin ne dai suka cafke wannan mutumi da ake zargi.

    Nan da nan masu gadin suka mika shi ga ofishin 'yan sanda da ke filin Hockey, wadanda a ranar Talata suka mika shi kotun shari'ar.

    Alkalin da ya yanke hukuncin Bello Musa Khalid ya yanke masa hukuncin sharar masallaci Waje da ke unguwar Fagge da ke girman gaske har na tsawon kwana 30 a jere.

  3. Karin mutum 1149 sun kamu da cutar korona a Najeriya

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 1149 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Laraba.

    Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu a jihar Lagos suke, inda aka samu karin mutum 680 dauke da cutar, yayin da a Rivers aka samu mutane 157 da gwajin da aka yi musu ya tabbatar da cewa sun kamu da cutar.

    Ga jerin jihohin da aka samu bullar cutar ranarTalata

    • Lagos-680
    • Rivers-157
    • Akwa Ibom-94
    • Oyo-56
    • Edo-36
    • FCT-34
    • Ogun-31
    • Ekiti-20
    • Delta-16
    • Abia-5
    • Nasarawa-5
    • Osun-5
    • Cross River-4
    • Plateau-3
    • Sokoto-2
    • Kano-1

    A jimillance adadin mutanen da suka kamu a faɗin ƙasar sun kai 184,593 , sai dai 167,738 sun warke. Akwai kuma mutum 2,236 da suka mutu.

    A baya-bayan nan ne aka samu ɓullar sabon nau'in cutar korona da ake kira Delta a Najeriya, wanda masana ke cewa yana da saurin yaɗuwa matuƙa.

  4. Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF ya ce zai rike wasu kudaden Afghanistan

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF ya ce zai rike wasu kudaden Afghanistan din saboda halin da kasar ta shiga.

    Matakin na IMF ya biyo mayan irinsa da Amurka ta dauka na toshe damar amfani da wasu kudaden kasar da ke jibge a bankunanta.

    Kudin da IMF zai hana kasar sun hadar da dala miliyan dari hudu da sittin da ya kamata Afghanistan ta karba a mako mai zuwa a matsayin wani bangare na tallafin asusun kan matsalar tattalin arziki da kasar ke ciki.

    Wakilin BBC ya ce matakin na IMF na baya bayan nan na nuna abunda wani mai magana da yawunsa ya kira rashin fahimtar inda al'amura suka sa gaba game da amincewa da gwamnatin kasar ta yanzu karkashin Taliban.

  5. Ƴan Taliban na ci gaba da amfani da ƙarfi wajen ƙara tabbatar da ikonsu a Afghanistan

    BBC

    Rahotanni na cewa 'yan Taliban na ci gaba da amfani da ƙarfi wajen kara tabbatar da ikonsu a Afghanistan.

    Sun dakatar da zanga-zangar adawa a birnin Jalalabad da ke gabashin kasar, inda rahotanni ke cewa sun harbe mutane da dama, ciki har da yara uku tare da raunata wasu a lardin Kunar.

    Bayanai sun ce an ga yan kungiyar dauke da muggan makamai suna sintiri a babban birnin kasar, Kabul.

    Shugaban Amurka Joe Biden ya ce akwai yiwuwar sojojin Amurka su ci gaba da zama a Afghanistan din fiye da wa'adin karshen wannan watan, idan har hakan zai ba da damar kwashe dukkan Amurkawan da ke kasar.

  6. Budewa

    Barkanmu da safiya da fatan an tashi lafiya.

    Buhari Muhammad Fagge ke fatan kasancewa da ku a wannan yini domin kawo muku labarai da rahotanni daga ko ina cikin sassan duniya.