Taliban: 'Shari'ar Musulunci za mu yi'

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau, Nasidi Adamu Yahaya and Umar Mikail

  1. Ƴan bindiga sun kashe ɗan sanda da ma’aikatan kamfanin mai a Imo

    Rahotanni a Najeriya sun ce wasu ƴan bindiga sun kai hari cibiyar wani kamfanin mai a jihar Imo inda suka kashe jami’in ɗan sanda da maka’aikatan kamfanin guda shiga.

    Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Imo wanda ya tabbatar wa kamfanin dillacin labaru na Reuters da labarin ya ce rundunarsu ta ɗauki matakai a yankin mai fama da hare-hare.

    Kakakin ƴan sandan na jihar Imo Michael Abattam ya ce an kai harin ne a ranar litinin a kamfanin Lee Engineeringda ke aikin gas a yankin Assa.

    Taswairar Najeriya
  2. Amina Mohammed ta yi magana kan makomar Afghanistan

    Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Amina Mohammed ta yi magana kan makomar mata a Afghanistan ƙarƙashin mulkin Taliban.

    A saƙon da ta wallafa a shafinta na Twitter, tsohuwar ministar muhalli ta Najeriya ta ce shekaru biyu da suka gabata a Afghanistan ta tattauna da shugabannin mata kuma sun gabatar mata da saƙo mai ƙarfi cewa: "ba za mu bari a samu koma baya ba ga ci gaban da aka samu na shekara 20."

    A cikin saƙonta, Amina Mohammed ta yi kira ga Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres kan tabbatar kare ƴancin matan Afghanistan.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Turkiyya na gina katanga don hana kwararar ƴan Afghanistan

    Yayin da dubban ƴan Afghanistan ke tserewa daga ƙasar, Turkiya ta sanar da cewa tana gina katanga kan iyakarta da Iran domin daƙile kwararar ƴan gudun hijira daga Afghanistan.

    Katangar za ta yi tsawon kilomita 295 idan an kammala, wadda kuma za a yi wa shinge da waya, kamar yadda kamfanin dillacin labaran AFP ya ruwaito.

    Jaridar Hurriyet Daily ta ambato ministan tsaron Turkiyya Hulusi Aka na cewa za su tsaurara matakai kuma "katangar za a gina ta ne yadda ba za a iya ketarawa ba."

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Taliban ta yi wa jami’an tsohuwar gwamnatin Afghanistan afuwa

    An samu hargitsi a filin jirgin sama a Kabul inda mutane suka dinga maƙale jirgi suna neman ficewa

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, An samu hargitsi a filin jirgin sama a Kabul inda mutane suka dinga maƙale jirgi suna neman ficewa

    Kwanaki biyu bayan ƙwace Kabul fadar gwamnatin Afghanistan, ƙungiyar Taliban ta sanar da yin afuwa ga jami'an gwamnati, tare da yin kira gare su da su koma bakin aiki.

    A filin jirgin sama na Kabul, jirage sun ci gaba da kwashe sojoji da jami'an diflomasiyya da sauran fararen hula.

    An dakatar da zirga -zirgar jiragen sama a ranar Litinin lokacin da ɗimbin mutanen da ke cikin mawuyacin hali suka yi kokarin shiga jirage don tserewa daga birnin na Kabul.

    Wakilin BBC ya ce tituna sun kasance fayau kuma an rufe shaguna da dama a Kabul.

    Babu kiɗan da aka saba a cikin gidajen abinci ko ma a motoci.

    Mata ƙalilan ne ake gani kan titi.

    Tuni aka goge hotunan mata da ke kan allon talla a cikin birnin Kabul.

  5. Corona ta sake kashe mutum 4 a Najeriya

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 584 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Litinin.

    Kuma alƙalumman sun nuna cewa cutar ta sake kashe mutum huɗu a ƙasar cikin sa'a 24.

    Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu a jihar Legas suke, inda aka samu karin mutum 201 da suka kamu, yayin da a jihar Rivers aka samu mutane 149 da gwajin da aka yi musu ya tabbatar da cewa sun kamu da cutar.

    A Abuja babban birnin Tarayya ƙarin mutum 82 suka kamu da cutar.

    An kuma samu ƙaruwar yaɗuwar cutar a jihohin Kano da Kaduna da Sokoto, kamar yadda alƙalumman suka nuna.

    NCDC

    Asalin hoton, NCDC

  6. Maraba

    Muna maraba da ku a wannan shafin da za mu shafe yinin Talata muna kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Sai ku kasance da mu.