Ba zan sauya matsayina na janye sojin Amurka daga Afghanistan ba - Biden

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, musamman halin da ake ciki a Afghanistan.

Rahoto kai-tsaye

Halima Umar Saleh and Nasidi Adamu Yahaya

  1. Shugaba Buhari ya taya Babangida murnar cika shekara 80 a duniya

    Buhari da IBB

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban ƙasar Janar Ibrahim Babangida murnar cikarsa shekara 80 a duniya.

    A wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan yaɗa labarai Garba Shehu ya fitar a ranar Litinin, Shugaba Buhari ya ce a matsayinsu na tsoffin kwamandojin yaƙi shi da Janar Babangida, suna da abubuwa iri ɗaya kamar kyakkyawan fata a kan gina Najeriya da haɗin kanta.

    Sanarwar ta ƙara da cewer Shugaba Buhari na fatan ƴan Najeriya masu sa'a irin Janar Babangida da shi kansa, za su jajirce wajen ƙoƙarinsu na taimaka wa ƙasar don kai wa gaci da ci gaba da zaman lafiya.

  2. Amurka ta lalata duk bayanan sirrin ofishin jakadancinta a Afghanistan, Daga Jon Sopel Editan BBC na Amurka Ta Arewa

    Anthony Blinken

    Asalin hoton, b

    Bayanan hoto, Ba wanda ya rage sai Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken, wanda ke ƙoƙarin nuna jarumtaka

    Abin na da matukar daure kai ganin yadda abubuwa ke faruwa da gaggawa - a farkon makon nan jami'an Amurka ke gargadin cewa zai kai tsawon watanni kafin a kwace Kabul.

    Sai ga shi cikin kwanaki kacal hakan ta faru.

    A yanzu kuma, duk da yarjejeniyoyin da aka yi na gyara dangantakar diflomasiyya, sai da ƙyar da gumi Amurkawa ke samun tserewa.

    An umarci jami'ai a ofishin jakadancin Amurka su lalata duk wasu bayanai na sirri, sannan helikwaftoci sun yi ta shawagi don kai ma'aikata filin jirgi.

    Ambasadan Amurka ya tafi sannan an yi ƙasa-ƙasa da tutarsu.

    Ba wanda ya rage sai Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken, wanda ke ƙoƙarin nuna jarumtaka.

  3. Labarai da dumi-dumi, 'Mutum biyar' sun mutu a filin jirgin sama na Kabul

    Filin hirgin saman ya cika da masu son tserewa daga kasar

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Filin hirgin saman ya cika da masu son tserewa daga kasar

    Rahotanni na cewa an samu asarar rayuka sakamakon turmutsutsun da mutane ke yi a filin jirgin sama na Kabul.

    Wasu ganau sun shaida wa BBC cewa a ƙalla fararen hula biyu ne suka mutu a yayin da ɗaruruwan mutanen da ke ƙoƙarin barin Afghanistan suke yi wa filin jirgin saman tsinke.

    Dakarun Amurka waɗanda suka ƙwace iko da filin jirgin a yayin da ake ci gaba da kwashe mutane daga birnin, sun yi ta harbe-harbe a sama don atrwatsa cincirindon mutane da safiyar yau Litinin.

    Amma kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa mutum biyar ne suka mutu sai dai babu tabbas ko harbin bindigar ne ya kashe su ko kuma turmutsutsu.

  4. Khalifan Tijjaniyya Muhammadu Sanusi ya jajanta wa iyalan matafiyan da aka kashe a Jos

    Sarki Sanusi

    Asalin hoton, AU Tumbin Giwa

    Tsohon Sarkin Kano kuma Khalifan ɗariƙar Tijjaniya a Najeriya Muhammadu Sanusi na II, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Filato da kuma jami;an tsaro da su gagauta yin bincike kan waɗanda suka kashe matafiya fiye da 20.

    A ƙarshen makon da ya gabata ne wasu ɓata-gari suka kashe matafiyan waɗanda ƴan ɗariƙar Tijjaniya ne da ke kan hanyarsu ta koma wa kudu maso yammacin najeriya bayan halartar taron wa'azi a gidan fitaccen Shehin Tijjaniyar, Dahiru Usman Bauchi.

    A wata sanarwa da ya fitar, Muhammadu Sanusi ya ce "gwamnati ta tsaya a kan amanar da Allah Ya ba ta na kare rayuwar al'umma a yi cikakken bincike a kan waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi a kuma yi musu hukuncin da ya dace."

    Khalifan Tijjaniya ya kuma yi kira ga ƴan ɗarikar tasa da sauran jama'a da su yi haƙuri kar su ɗauki hukunci a hannu, "a bai wa jami'an tsaro damar yin aiki yadda ya dace.

    "Muna roƙon Allah ya bayyana wafdanda suka yi wannan ta'addancin kuma ya ba da ikon yin adalci."

    Sannan ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mamatan da kuma Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

  5. Tsarin shugabancin ƙungiyar Taliban

    Taliban, wato ɗalibai kenan a yaren Pashto, ta kafu ne a farkon shekarun 1990 a arewacin Pakistan sakamakon janyewar dakarun Tarayyar Sabiyet daga Afghanistan.

    An yi amannar cewa masu fafutuka ƴan ƙabilar Pashtun sun fara bayyana ne a wasu tarukan addini - waɗanda yawanci Saudiyya ce ke ɗaukar nauyinsu - waɗanda suke yin kira ga aƙidar Sunni.

    Tsarin shugabancin Taliban
  6. Tsohon shugaban Afghanistan ya ce ba zai bar kasar ba yayin da Ashraf Ghani ya tsere Tajikistan

    A yayin da rahotanni ke cewa shugaban kasar Afghanistan Ahsraf Ghani ya tsere zuwa kasar Tajikistan, shi kuwa tsohon shugaban Hamid Karzai ya ce zai tsaya a Kabul ba zai je ko ina ba.

    Karzai ya saki wani bidiyo a syafinsa na Facebook inda yake cewa mabiyansa zai ci gaba da zama a Kabul Bidiyon ya nuna shi tsaye tare da 'ya'yansa mata uku inda yake cewa "ya ku al'ummar Kabul, ni da iyalana muna tare da ku."

    "Muna fatan a warware matsalolin kasarmu da na babban birninmu ta hanya mai kyau kuma cikin luman," in ji shi.

    "Ina kira ga dakarun tsaron kungiyar Musulynci ta Taliban a duk inda suke, su tabbatar da tsaron rayukan mutane da dukiyoyinsu, daga dakarun tsaronmu har na Taliban."

    Hamid Karzai  da ƴaƴansa

    Asalin hoton, Hamid Karzai Facebook

    Karzai ya shugabanci kasar a 2011 - shekara gida kafin shigar Amurka. Ya rike kasar har zuwa 2014, inda ya zama daya daga cikin shugabannin kasa mafi dadewa a mulki a yankin Asiya.

    Sai dai gwamnatocin kasashen waje sun yi ta sukarsa saboda gaza magance cin hanci da kuma kasa tunkarar shugabannin al'ummomi wajen bai wa mata haƙƙoƙinsu.

  7. Me Taliban ta ce tun bayan ƙwace birnin Kabul?

    Suhail Shaheen

    Wani mai magana da yawun Taliban ya shaida wa BBC cewa ƙungiyarsu na aiki don kafa sabuwar gwamnati a Afghanistan.

    Ƙungiyar ta sake bai wa mayaƙanta umarnin cewa kar su takurawa fararen hula, a yayin da take son sauya tsarin yadda za ta jagoranci ƙasar a zamanance.

    A wani lamari daban kuma, wani mamba a tawagar sasantawa ta Taliban a Qatar ya shaida wa BBC a daren jiya cewa "babu ramuwar gayya" a kan mutanen Afghanistan.

    "Muna tabbatar wa mutanen Afghanistan, musamman mazauna Kabul, cewa da dukiyoyinsu da rayukansu duk suna cikin aminci - babu ɗaukar fansa a kan kowa," kamar yadda Suhail Shaheen ya gaya wa wakiliyar BBC Yalda Hakim ana tsaka da labarai.

    Ƴan Afghanistan da dama na tsoron dawowar mulkin kama-karya na shekarun 1990, wadda aka san ta da kashe mutane a bainar jama'a da jefe mutane masu wasu laifuka da kuma haramta wa yara mata zuwa makaranta.

  8. Firaministan Malaysia ya yi murabus

    Muhyiddin Yassin

    Asalin hoton, Reuters

    Firai ministan Malaysia Muhyiddin Yassin ya yi murabus, bayan da ya sanar da sarkin kasar cewa a yanzu, ba shi da rinjaye a Majalisar Dokoki.

    Majalisar ministocinsa ta yi murabus tare da shi.

    Wannan ya biyo bayan rikice -rikicen siyasa da aka shafe watanni ana yi lokacin da abokan hadin gwiwa suka janye tallfin da suke bai wa gwamnatinsa saboda tuhumar cin hanci da rashawa kan wasu 'yan siyasa.

    Mista Muhyiddin ya hau kan mukamin ne watanni 17 da suka gabata a cikin wani juyin mulki na cikin gida, wanda ya rushe gwamnatin Mahathir Mohamad

  9. Dakarun Afghan sun yi saranda a filin jirgin Kandahar

    Kandahar

    A wani yankin na Afghanistan, Taliban ta fitar da sanarwar cewa a ƙarshe ta samu damar wargaza turjiyar da ta fuskanta a filin jirgin saman Kandahar, kuma dubban dakarun ƙasar na musamman ne suka miƙa musu wuya.

    Mayaƙan Taliban ne suka yi wa dakarun ƙawanya tsawon kwana uku.

    Birnin Kandahar, wanda ke kudancin ƙasar, shi ne birnin na biyu mafi girma kuma a can ne sansanin jiragen yaƙi na Bagram yake - inda can ne cibiyar rundunar sojin hadaka da Amurka ke jagoranta take a ƙasar.

  10. Amurka ta ce ta gama kwashe ƴan ƙasarta daga Afghanistan

    Biden

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce yanzu haka dukkan ma'aikatan ofishin jakadancinta da ke Kabul sun koma filin jirgin sama na kasa da kasa na babban birnin na Afghanistan, wanda ta ce yana karkashin kulawar sojojin Amurka.

    Sojojin Burtaniya ma na tallafa wa wajen kwashe fararen hular Burtaniya da Afghanistan.

    Wakiliyar BBC ta ce akwai gagarumar fargaba a tsakanin jama'a a halin da ake ciki, ana jiran jin abun da ka je ya zo.

    Fiye da kasashe 60 na duniya sun rattaba hannu kan wata sanarwa da ke cewa dole ne a ba wa ƴan kasar da ke son ficewa damar yin hakan.

    Taliban ta kwace iko da da Kabul ne bayan shafe shekaru 20 da fatattakarta daga birnin dakarun sojin Amurka suka yi.

    Shugaba Ashraf Ghani ya tsere zuwa Uzbekistan, yana mai cewa ya ajiye mulki ne don gudun zubar da jini.

  11. Mutum 541 ne suka kamu da cutar korona a ranar Lahadi

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 541 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Lahadi.

    Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu a jihar Legas suke, inda aka samu karin mutum 242 dauke da cutar, yayin da a Akwa Ibom aka samu mutane 94 da gwajin da aka yi musu ya tabbatar da cewa sun kamu da cutar.

    Ga jerin jihohin da aka samu bullar cutar ranar Lahadi

    • Lagos-242
    • Akwa Ibom-94
    • Enugu-48
    • Oyo-48
    • Anambra-34
    • Rivers-19
    • Ogun-17
    • Ekiti-15
    • FCT-9
    • Kwara-7
    • Abia-5
    • Delta-2
    • Niger-1
  12. Maraba

    Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin da zai kawo maku labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.