Taliban ta umarci mayaƙanta su tsaya a ƙofofin shiga birnin Kabul

Asalin hoton, Other
Lamarin na sauyawa cikin sauri a safiyar nan.
Taliban ta fitar da wata sanarwa da ke umartar mayaƙanta cewa su tsaya a bakin ƙofofin shiga birnin Kabul, suna masu nuna damuwa game da fararen hula da ka iya cutuwa.
Sanarwar ta ce har yanzu gwamnati ce ke da alhakin tsaron birnin, sannan ta ce tana tattaunawa da gwamnati domin karɓar birnin cikin ruwan sanyi.
Kazalika ta nemi 'yan ƙasar da kar su gudu tana jaddada cewa "Taliban na son mutane daga kowane ɓangare na al'umma su zauna a ƙarƙashin gwamnatin Musulunci wadda za ta amfani kowa".
Sai dai kuma, rahotanni na cewa ana jin ƙarar harbe-harbe sannan an ga mayaƙan riƙe da tutoci a kan tituna.

