Gwamnatin Afghanistan na gab da rushewa bayan Shugaba Ghani ya fice daga ƙasar
Wannan shafi yana kawo muku bayanai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Fauziyya Kabir Tukur
Mai magana da yawun Taliban ya kira wakiliyar BBC ana tsaka da labarai
Mai shiga tsakani na kungiyar Taliban Suhail Shaheen ya kira wakiliyar BBC Yalda Hakim a waya, a lokacin da ake tsaka da labarai don shaida wa mutane cewa "babu barazana ga rayukansu."
"Muna tabbatar wa da mutane a Afghanistan, musamman na birnin Kabul cewa da rayukansu da dukiyoyinsu duk suna cikin aminci - babu ramuwar gayya a kan kowa," kamar yadda ya gaya mata.
"Mu bayin mutane ne da kuma kasar nan."
'Tafiyar awa biyar na yi zuwa fiin jirgin sama'
Saeedi dalibi ne mai shekara daga Kabul. Ya yi tafiyar fiye da awa biyar don zuwa filin jirgin sama.
"Kafafuna na zogi sosai, har sun duri ruwa, ba na iya tsayuwa sosai," kamar yadda ya shaida wa BBC.
"Garin ya zama kamar barikin soji - mutane sanye da kayan al'adar kasar, amma suna dauke da makamai kuma suna harbi a iska. Hakan ya tuna min da labarin Jihadi da nake ji a wajen iyayena."
Saeedi zai fara karatun digirinsa na biyu ne a Istanbul. Ya koma Kabul ne don yin hutu tare da iyalansa kafin zangon karatu ya soma.
"A yanzu da zan koma makaranta, ina tunanin iyalaina - ba su da wata hanyar tsira. Ban hango alheri a nan gaba ba."
*An sauya sunaye
Taliban na son MDD ta ci gaba da ayyukanta a Afghanistan
Asalin hoton, EPA
Wata mai magana da yawun Asusun Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (Unicef) a kabul ta faɗa wa BBC cewa zuwa yanzu Taliban na "mutunta ofisoshin ƙungiyar".
Sam Mort ta ce Taliban ta buƙaci ƙungiyar ta ci gaba da ayyukanta a Afghanistan.
Ta ƙara da cewa 'yan gwagwarmayar ba sa kyarar kowa kuma yanzu haka ma su ne ke bai wa ayyukan MDD tsaro.
Ta jaddada ci gaba da kulawa da mata da ƙananan yara na Afghanistan, tana mai fatan komawa bakin aiki cikin 'yan kwanaki masu zuwa.
'Yan Afghanistan ne za su yi alkalanci a kan tserewar shugaban kasar'
Asalin hoton, Reuters
Shugaban Kwamitin Koli na Sasantawa na Afghanistan Abdullah Abdullah, ya tabbatar da cewa Shugaba Ashraf Ghani ya tsere daga kasar.
An samar da kwamitin sasantawar ne don yin sasanci da 'yan Taliban.
Da yake bayyana shi a matsayin "tsohon shugaban kasa", Abdulah ya ce Ghani ya tsere daga kasar a irin wannan yanayi da ake ciki."
"Allah zai kama shi kuma al'ummar kasar za su yi alkalanci," kamar yadda ya fada a wani bidiyo a Facebook.
Yawan wadanda suka mutu a girgizar kasar Haiti ya kai 700
Asalin hoton, Reuters
Jami'ai a Haiti sun tabbatar da mutuwar a kalla mutum 724 bayan mummunar girgizar kasa mai maki 7.2 da ta faru a kasar da ke yankin Karibiya.
Masu aikin ceto suna ta aikin neman mutane a karkashin baraguzai.
Gidaje da coci-coci da makarantu na daga cikin gine-ginen da suka rushe a girgizar kasar. Wasu asibitocin sun cika da mutane kuma babu isassun kayan aiki.
Akwai mutane da yawa da ba a gani ba har yanzu sannan a kalla utum 2,800 ne suka jikkata, a cawar jami'ai.
Lamarin ya sake munanan yanayin da dama kasar ke ciki, wacce ke farfadowa daga rikicin siyasar da ta fada bayan kisan gillar da aka yi wa shugaban kasar a watan da ya gabata.
Girgizar kasar ta fi shafar kudu maso yammacin kasar ne musamman wuraren birnin Les Cayes.
Wani bidiyo a shafukan sada zumuntaya nuna yadda mazauna yankin ke neman danginsu a cikin baraguzan gine-gine cikin tashin hankali.
Taliban ta saki fursunoni daga gidan yari mafi girma a Afghanistan
Asalin hoton, Mashal Afghan
Wani bidiyo da aka wallafa a intanet ya nuna fursunoni na yawo bayan an sake su daga gidan yari na Pul-e-Charkhi da ke birnin Kabul.
Gidan yarin shi ne mafi girma a Afghanistan.
Tun farko mayaƙan Taliban sun fatattaki sojoji a Bagram, wani tsohon sansanin sojan sama na Amurka, ranar Lahadi.
Daga cikin mutum 5,000 da aka sako daga gidan yarin, akwai mayaƙan Taliban da wasu masu tsattsauran ra'ayi na ƙungiyar Islamic State.
Taliban ta ce ta ƙwace iko da fadar shugaban ƙasa a Kabul
Asalin hoton, Getty Images
Taliban na iƙirarin cewa ta kama iko da fadar shugaban ƙasa a birnin Kabul.
Ɗazun nan Shugaban Ƙasa Ghani ya fice daga ƙasar, sai dai har yanzu babu tabbacin abin da ke faruwa a fadar tasa.
A cewar wani ɗan jarida mai suna Bilal Sarwary, wanda ya tattauna da mutum biyu da ke cikin masu tattaunawar karɓar mulki, daga cikin sharuɗɗan karɓar mulkin akwai cewa Shugaba Ghani zai halarci bikin miƙa mulki a fadar amma kuma shi da jami'an gwamnatinsa sai suka gudu.
"Daga nan ne aka umarci ma'aikatan fadar da su fice, inda aka bar ta fayau," a cewar mutanen.
Daga baya Taliban ta faɗa wa Reuters cewa ta ƙwace fadar. Ya zuwa yanzu jami'an gwamnati ba su tabbatar da hakan ba.
Labarai da dumi-dumi, Ana harbe-harbe a filin jirgin Kabul, in ji Ofishin Jakadancin Amurka
Wasu rahotannin na cewa ana harbe-harbe a filin jirgin saman Kabul, a cewar wani sakon gaggawa da Ofishin Jakadancin Amurka ya fitar.
Jami'ai sun bai wa 'yan Amurka da suka yankin umarnin neman mafaka, a yayin da yanayin tsaron da ake ciki a Kabul ke gaggawar sauyawa.
An nemi duk wasu Amurkawa da suke bukatar barin Kabul su yi rijista ta intanet, bayan kammala kwashe ma'aikatan diflomasiyya.
Shahararren ɗan wasan Bayern Munich Gerd Muller ya rasu
Asalin hoton, Rex Features
Shahararren ɗan ƙwallon Bayern Munich da Jamus, Gerd Muller, ya rasu yana da shekara 75.
Ɗan wasan gaban ya ci wa Yammacin Jamus ƙwallo 68 a wasa 62 da ya buga, ciki har da ƙwallon da ta bai wa ƙasar nasarar lashe Kofin Duniya a 1974 a kan Netherlands.
Muller ya shafe shekara 15 a Bayern Munich, inda ya ci ƙwallaye mafiya yawa a tarihin gasar da ƙwallo 365 cikin wasa 427.
"Yau rana ce ta baƙin ciki ga Bayern Munich da dukkan magoya bayanta," in ji shugaban Bayern, Herbert Hainer.
Kungiyar Kiristoci Ta Najeriya ta yi Allah-wadai da kashe matafiya a Jos
Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar
Kiristoci Ta Najeriya CAN reshen jihar Filato a yankin tsakiyar kasar, ta yi
Allah-wadai da kashe matafiya da aka yi a kan titin Rukuba a ranar Asabar.
A
wata sanarwa da shugaban kungiyar a jihar Polycarp Lubo ya fitar a ranar
Lahadi, ya nemi jami’an tsaro da su gano wadanda suka aikata hakan.
A
ranar Asabar ne wasu bata gari suka tare motocin bas na wasu matafiya da
rahotanni suka ce Musulmai ne, inda suka kasha mutuum 22 tare da ji wa wasu da
dama rauni.
Mr Lubo ya kuma yi Allah-wadai da kasha-kashen
da ake yi Bassa da Riyom a karamar hukuar Jos Ta Kudu da kuma karamar hukumar Barkin
Ladi.
Ya ce: “Muna nuna alhininmu da
takaicinmu kan hare-haren baya-bayan nan na Riyom da Jos Ta Arewa da Barakin
Ladi da kuma Bassa, da suka jawo asarar rayuka.
“Shugabancin CAN ya yi tur da wadannan
hare-haren yana kuma rokon jami’an tsaro da su tabbatar da dawowar doka da oda.
“Kowace rai na da muhimmanci kuma ba
za a yarda da kashe mutane don bambancin addini ko kabilarsu ba,” in ji shi.
Ana hana jiragen sama sauka a Kabul saboda hargitsi
Asalin hoton, EPA
Babbar mai aiko da rahotanni daga kasashen waje
Lyse Doucet ta BBC ta yi magana a shirin Newshour yayin da take cikin wani jirgin fasinja mai zuwa Kabul.
"Ina cikin wani jirgin fasinja da ya yi ta shawagi a Kabul kusan awa daya - inda ta cikin taga ina iya ganin tsaunukan Hindu Kush, wadanda wani bangare ne na musamman a tarihin Afghanistan.
Labarin abin da ke faruwa a yau na daya daga cikin wadanda babu wanda ya taba zaton za su faru shekara 20 da suka gabata a lokacin da rundunar sojin da Amurka ke jagoranta ta fara aiki a Afghanistan.
Wannan jirgin da nake ciki na dauke da mutum 400 da suka hada da yara 100, amma sai aka ce mana wani jirgin soji da ya lalace ne a kan titin saukar jirgin shi ya sa ba za mu iya sauka ba.
Ba mu da tabbas ko lallai hakan ne.
Ko saboda jirage na kwashe jami'an Afghanistan ne a wannan kurarren lokacin? Ko kuma saboda sauran jiragen Amurka da Birtaniya ne da suke kwashe 'yan kasarsu? Ba mu da tabbas.
An karkatar da jirgin namu - inda muke komawa Dubai - duk da cewa an ce mana za a bai wa jiragen fasinja damar sauka a can din.
Babu tabbas kan yaushe za a yi hakan, har sai yanayin ya daidaita kuma an tabbatar mana cewa za a iya sauka lafiya kuma mutane za su iya shiga Kabul ba matsala.
Mutum 22 sun rasu a hatsarin karyewar gada a jihar Jigawa
Asalin hoton, @SANKARAJGH
Aƙalla mutum 22 ne ake tunanin sun rasu ranar Lahadi lokacin da wata gada ta karye a Ƙaramar Hukumar Gwaram ta Jihar Jigawa.
Mazauna yankin sun bayyana cewa gadar ta karye ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.
"Mutanen suna cikin tafiya a motoci lokacin da ake zabga ruwan sama, sai aka yi rashin sa'a gadar ta yanke a lokacin kuma ta rufta da su," kamar yadda wani mazaunin Gwaram ya shaida wa BBC.
Rahotanni na cewa mutanen da suka rasu na tafiya ne daga Kano zuwa jihar Adamawa lokacin da lamarin ya faru.
Wata sanarwa da Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwaram ya fitar ta ce lamarin ya faru ne a daren Asabar "don haka a sanar da mutane babu hanya".
Ana kwashe jami'an diflomasiyyar Amurka daga Kabul cikin gaggawa
Asalin hoton, Getty Images
Jiragen helikwafta na ta tashi da sauka a ofishin jakadancin Amurka da ke Kabul, yayin da ake ci gaba da gaggauta kwashe jami'an ofishin daga Afghanistan.
A lokacin da jiragen na Black Hawk da Chinook ke nufar filin jirgin sama na Kabul, wasu daga cikinsu na kunna fitilu masu hayaƙi don hana Taliban kai masu harin roka.
A cewar wakilin kafar yaɗa labarai ta NBC Richard Engel, za a rufe ofishin jakadancin da zarar an kammala kwashe jami'an bayan tattaunawa mai zurfi da Taliban kan wucewa da su cikin tsaro.
Ranar Juma'a ne ma'aikatan ofishin jakadancin suka samu umarnin lalata duk wasu bayanan sirri da abubuwan da ake iya amfani da su a yi wa Amurka farfaganda.
Wasu daga cikin jami'an diflomasiyyar Amurkar za su kasance a filin jirgin na Kabul har bayan kwashe sauran jami'an zuwa wani lokaci a cewa jaridar New York Times.
Labarai da dumi-dumi, Shugaba Ashraf Ghani ya fice daga Afghanistan
Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Ashraf Ghani na Afghanistan ya fice daga ƙasar, a cewar rahotanni.
Wannan na zuwa ne a lokacin da ƙungiyar Taliban ta isa wajen garin.
Rahotannin na nuna cewa mataimakin shugaban ƙasar Amrullah Saleh ma ya fice daga ƙasar.
Mista Ghani na fuskantar tsananin matsin lamba kan ya ajiye aiki yayin da mayakan Taliban suka ƙwace manyan biranen Afghanistan cikin kwanaki 10.
Miƙa wuyan da ƴan Boko Haram ke yi na jefa jihar Borno cikin mawuyacin hali- Zulum
Asalin hoton, BORNO GOVT
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ce miƙa wuya da mayaƙan Boko Haram ke yi a jihar ya jefa ta cikin mawuyacin hali.
Ya ce lamarin na buƙatar kulawar masu ruwa da tsaki da wakilan al'ummomi su hada kai wajen tabbatar da cewa an samo mafita.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ziyarar da ya kai garuruwan Bama da Gwoza na jihar ta Borno.
A cewar gwamnan "mu da muke jihar Barno, muna cikin mawuyacin hali bisa miƙa wuyan da mayaƙan Boko Haram ke yi. Yanzu dole ne mu zaɓi cikin abu biyu masu muni: wannan yaƙin da ya ki ci ya ƙi cinyewa da kuma rungumar waɗannan ƴan ta'addar da suka miƙa wuya suke so su dawo cikinmu."
Ya ce a jihar akwai mutane da dama da ƙungiyar Boko Haram ta kashe wa ƴan uwa kuma har yanzu suna cikin alhinin mutuwarsu, don haka zai yi wuya su iya rungumar mayaƙan masu miƙa wuya har su iya rayuwa tare da su a wuri guda.
"Ko sojoji ma, wannan abu ne mai wuya a garesu saboda akwai abokan aikinsu da ƙungiyar ta kashe. Babu wanda zai iya rungumar makashin masoyinsa hannu bibbiyu," in ji Zulum.
Gwamnan ya ce amsar ƴan Boko Haram na da haɗarin bata wa ƴan uwan waɗanda aka kashe rai kuma suna ma iya yin bore, yayin da a wani ɓangaren kuma ƙin karɓarsu na iya sa mayaƙan Boko Haram ɗin su shiga ƙungiyar ISWAP su ƙara mata ƙarfi.
Gwamna Zulum ya ce zai tattauna da Shugaba Muhammadu Buhari da manyan hafoshin tsaro da shugabannin al'umma da malaman addini da ƴan majalisar wakilai da malaman makaranta da sauran masu ruwa da tsaki musamman waɗanda lrikicin Boko Haram ya shafa don ganin an samo mafita a wannan lamari.
Taliban ta yi alƙawarin mutunta 'yancin mata da 'yan jarida a gwamnatinta
Asalin hoton, Getty Images
Wani mai magana da yawun Taliban ya yi alƙawarin cewa ƙungiyar za ta mutunta 'yancin mata da kuma 'yan jarida yayin da take shirin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya a Afghanistan.
Nasarar da Taliban ke yi - wadda ta sa ta ƙwace kusan baki ɗayan ƙasar cikin kwana 10 kacal - ta jawo damuwa game da halin da matan ƙasar za su shiga.
A lokacin da Taliban ta ƙwace mulki tsakanin1996 zuwa 2002, ƙungiyar ta kafa dokokin Shari'ar Musulunci da suka haɗa da jefe masu aikata zina, da yanke hannun ɓarayi, da hana mata zuwa makaranta 'yan sama da shekara 12.
Sanarwar ta Taliban na ƙoƙarin kwantar da hankalin ƙasashen duniya ne saboda damuwar da suke nunawa.
Kakakin ƙungiyar ya ce za a ƙyale mata su fita daga gidajensu su kaɗai sannan za a bari su ci gaba da karatu da kuma aiki.
Sai dai rahotannin da ake samu daga wasu sassan da ƙungiyar take iko da su sun saɓa da wannan iƙirari. A Kandahar misali, an faɗa wa matan da ke aiki a bankuna cewa daga yanzu wasu 'yan uwansu maza ne za su dinga yin aikin nasu.
A wasu yankunan kuma, ana hana matan fita daga gida su kaɗai - dole sai da namiji ɗan uwansu - sannan ana tilasta musu saka doguwar rigar abaya wato burƙa.
'Yan Afghanistan na tserewa daga Kabul saboda kutsawar Taliban
Asalin hoton, AFP
Mutane na ta tserewa daga babban birnin Afghanistan Kabul a cikin motocinsu, lamarin da ya jawo cunkoson motoci a kan tituna.
An ba da rahotannin cewa 'yan Taliban na hanyoyin shiga birnin amma an bai wa mayakan umarnin kar su yi rikici sannan kar su hana duk mai son fita daga garin
Kamfanin dillancin labaran Reuters da fari ya ruwaito cewa mutane na barin ababen hawansu suna tafiya da kafa zuwa filin jirgin sama.
Kashe-kashen Jos: An tsawaita dokar hana fita a Jos ta Arewa
Asalin hoton, Daily Trust
Gwamnatin Jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Najeriya ta ce dokar hana fitar da ta saka ta zama ta zaman gida baki ɗaya biyo bayan kashe matafiya Musulmai da "matasan ƙabilar Irigwe" suka yi a Jos, babban birnin jihar.
Tun farko an ƙaƙaba dokar hana fitar ce daga 6:00 na yamma zuwa 60:00 na safe a ƙananan hukumomin Jos Ta Kudu da Jos ta Arewa da kuma Bassa. Amma ƙarin ya shafi Jos ta Arewa ne kaɗai.
A ranar Asabar ne matasan suka tare matafiyan tare da kashe kusan mutum 30 sannan suka jikkata wasu kusan 50 a lokacin da suke wucewa ta cikin birnin zuwa Jihar Ondo bayan sun taso daga garin Bauchi.
Sanarwar 'yan sanda ta ce mutum 25 aka kashe a harin tare da jikkata 33.
Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya ya tura tawagar bincike ta musamman ƙarƙashin jagorancin DIG Sanusi N. Lemu.
Ya ƙara da cewa rundunar ta kama mutum 20 da ake zargin aikata kisan sannan ta ceto mutum 33 da aka raunata yayin harin.
Labarai da dumi-dumi, Ministocin gwamnatin Afghanistan na shirin miƙa mulki cikin lumana
Halin da ake ciki a Kabul na ci gaba da ruruwa kamar an cinna wa karmami wuta, inda rahotanni ke ci gaba da shigowa ba ƙaƙƙautawa.
Muƙaddashin ministan harkokin cikin gida na Afghanistan ya bayyana a wani bidiyo na kafar talabijin ta Tolo, yana cewa za a miƙa mulki cikin lumana ga gwamnatin rikon kwarya.
Ya ce ba za a kai wa Kabul hari ba.
Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ambato wani jami'in gwamnatin Afghanistan yana cewa masu sasantawa daga bangaren Taliban suna kan hanyarsu ta zuwa fadar shugaban kasa don shirin karbar mulki.
Tun da fari Taliban ta ce ta bai wa mayakanta umarnin tsayawa a hanyoyin shiga birnin na Kabul.
Kashe-kashen Jos: IGP Usman ya aika tawagar bincike ta musamman
Wata sanarwa daga kakakin rundunar 'yan sanda na ƙasa, Frank Mba, ta ce matakin ya biyo bayan kashe mutum 25 a harin wanda wasu "matasan ƙabilar Irigwe" suka tare matafiya ranar Asabar, inda suka raunata wasu kusan 50.
Sanarwar ta ce DIG Sanusi N. Lemu ne zai jagoranci tawagar sannan kuma za ta ƙunshi jami'ai daga ɓangarorin bincike da dama na rundunar. Kazalika an tura ƙarin jami'an tsaro yankin na Rukuba domin kare sake afkuwar tashin hankalin.
IGP Usman ya ce ya zuwa yanzu an kama mutum 20 da zargin aikata kashe-kashen sannan an ceto mutum 33 da suka ji raunuka yayin harin.
Rahotanni sun ce an tare motocin matafiyan ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa Jihar Ondo da ke kudancin Najeriya bayan sun halaraci taron bikin sabuwar shekarar Musulunci a Jihar Bauchi.