Yuli ne wata mafi tsananin zafi a tarihi - Ƙwararru

Asalin hoton, Reuters
Masana a Amurka sun tabbatar da cewa Yuli ne wata mafi zafi da kasar ta taɓa gani a tarihi.
Sun ce a watan da ya gabata irin tsananin zafin da ya rika tasowa daga gulbi abu ne da ba taba gani ba tun bayan karni na 20.
Tsananin zafin da aka yi a Amurka cikin watan Yuli ya zarta wanda aka gani shekara 142 da suka wuce, a cewarsu.
Su ma kasashen Turai da suka hada da Italiya da Portugal da Sifaniya na fuskantar tsananin zafin da ba su saba ganin irinsa ba.
Wakilin BBC ya ce tsananin zafi a makon da ya wuce ya kai maki 48.8 a ma'aunin salshiyos a tsibirin Sicily, wani abu daba a taba gani ba a nahiyar Turai.
Haka ma tsananin zafin ya dinga haifar da wutar daji a sassa daban-daban na Turan.

