Taliban ta sake ƙwace biranen lardi biyu

Wannan shafi yana kawo muku bayanai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi na BBC Hausa a nan muka kawo karshen labarai da rahotanni daga Najeriya da sauran sassan duniya a yau.

    Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu za mu dawo don ci gaba da bayyana muku halin da ake ciki a duniyar.

    Kuna iya komawa kasan shafin don karanta wasu labaran kamar na halin da ake ciki a Afghanistan, da girgizar kasar da ta faru a Haiti da ambaliyar ruwan Japan da dai sauransu.

    Mu kwana lafiya, Allah Ya ba mu alherinsa.

  2. An umarci 'yan yankin Igbo da su bi umarnin dakatar da dokar zama a gida

    An umarci mambobin kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (Ipob) da su bi umarnin da aka bayar na dakatar da dokar zama a gida da aka sa a kudu maso gabashin kasar, kamar yadda lauyan Nnamdi Kanu, Ifeanyi Ejiofor ya ce.

    Ejiofor ya ce ya fadi hakan ne saboda tambayoyin da mambobin Ipob ke masa don sanin ko da gaske ne an dakatar da umarin zama a gida din.

    Ipob, wacce gwamnatin Najeriya ta bayyana a matsayin mai son ta da zaune tsaye ta sanar da dakatar da umanin da ta bayar a baya na hana fita duk ranar Litinin, inda ta ce dokar za ti aiki ne kawai a lokacin da za a gabatar da Kanu a gaban kotu.

  3. An sake gano wata 'yar Chibok da ke hannun Boko Haram

    Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya Babagana Umara Zulum ya karbi wata 'yar makarantar sakandaren Chibok da ke hannun mayakan Boko Haram.

    A wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan yada labarai Isa Gusau ya fitar, ya ce yarinyar ce ta kai kanta ga sojojin kasar a garin Gwoza.

    "Kwamandan runduna ta musamman ta 26 Taskforce Brigade, Birgediya Janar DR Dantani ne ya mika 'yar makarantar mai suna Hassana Adamu da 'ya'yanta biyu ga Gwamna Zulum,'' in ji sanarwar.

    Hassana na daga cikin daliban makarantar sakandaren mata ta Chibok fiye da 200 da mayakan Boko Haram suka sace ranar 14 ga watan Afrilun 2014.

    Ko a ranar 28 ga watan Yulin da ya gabata sai da wata dalibar mai suna Ruth Ngladar Pogu, da wani mutum da ta ce mijinta ne suka mika kansu ga rundunar sojin Najeriya a wani waje a garin Bama,

  4. Sojojin Amurka sun kai wa Taliban hare-hare a birnin Kandahar

    Taliban

    Asalin hoton, EPA

    Dakarun Amurka sun kai hare-haren sama a filin jirgin Kandahar, a cewar wani dan jarida a kasar Bilil Sarwary.

    An kashe gwamman mayakan Taliban, a cewarsa, yana mai ambatar cewa ya ji daga bakim majiyoyin tsaro da kuma jami'an wani asibiti a birnin.

    Kungiyar masu tayar da kayar bayan ta kwace iko da Kandahar, birni na biyu mafi girma a Afghanistan ranar Juma'a.

    Hakan babbar nasara ce ga Taliban saboda kasancewar birnin na dauke da babban filin jirgin sama da harkokin noma da na kasuwanci.

  5. Ambaliya: An umarci mutum miliyan biyu su bar gidajensu a Japan

    Japan Flood

    Asalin hoton, KYODO VIA REUTERS

    An umarci kusan mutum miliyan biyu da su bar gidajensu a yayin da ake mamakon ruwan sama a wasu yankunan Japan.

    Ana ta gargadi ga mazauna yankunan Fukuoka da Hiroshima.

    Wata mata ta rasa ranta, mijinta kuma da 'yarta sun bata bayan da zaftarewar laka ta lalata gidajee biyu a Nagasaki.

    An tura fiye da sojoji 150 da 'yan kwana-kwana don su taimaka wajen aikin ceto a yankin.

    Suna ta aikin neman mutanen da ba a gani ba, ta hanyar yin kaffa-kaffa da afkuwar wata zaftarewar lakar sakamakon ruwan sama da ake ci gaba da yi," in ji wani jami'i da ya shaida wa AFP.

    Yankin yammacin kasar abin ya fi shafa amma ana sa ran za a kara yin ruwan sama kamar da bakin kwarya nan da 'yan kwanaki a fadin kasar

    A jumulla, an bayar da sanarwar gargadi ga fiye da mutum miliyan daya da dubum dari takwas, a cewar kafar yada labaran kasar.

  6. Qatar ta bukaci Taliban ta tsagaita wuta

    Taliban

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan Harkokin Wajen Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani, ya gana da shugaban ofishin Taliban ranar Asabar don bibiyar batun inda aka kwana a tattaunawar zaman lafiya.

    "Ministan harkokin kasashen waje ya bukaci Taliban a wajen ganawar da su tsagaita wuta," kamar yadda wata sanarwa a shafin intanet na gwamnatin Qatar ta bayyana.

  7. Mummunar girgizar ƙasa ta kashe mutane da dama a Haiti

    Haiti

    Wata gagarumar girgizar ƙasa ta afku a ƙasar Haiti da ke yankin Caribbean.

    Girgizar ƙasar mai nauyin 7.2 ta faru ne a yammacin ƙasar, yayin da zurfinta ya kai kusan kilomita 12 daga garin Saint-Louis du Sud, a cewar US Geological Survey (USGS).

    Hukumomi sun faɗa wa manema labarai cewa an samu waɗanda suka mutu amma har yanzu ba san adadin waɗanda rasun ba.

    Hotunan da aka wallafa a shafukan zumunta sun nuna yadda gidaje suka zama ɓaraguzai.

    Har yanzu Haiti ba ta gama farfaɗowa daga mummunar girgizar ƙasa da aka yi a 2010 ba.

    Cibiyar USGS ta ce an ji ta a kusan dukkan yankin na Caribbean.

  8. Mutanen da suka kashe mesar da ta daɗe tana cinye musu dabbobi

    Mesa

    Asalin hoton, ALIYU AHMAD ILYARI

    A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne al'ummar wani ƙauye Ilyari, suka samu nasarar kashe wata ƙatuwar mesa bayan da aka ganta tana haɗiye wani ɗan akuya a jeji.

    Waɗanda suka shaida lamarin sun faɗa wa BBC Hausa ko dattajai na garin masu shekara 80 ma sun ce ba su taɓa ganin maciji mai girman wannan mesar ba.

    Al'ummar Ilyari wanda ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Shira a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya sun ce suna zargin mesar ita ce wacce ta daɗe tana haɗiye musu awaki.

    Mazauna ƙauyen Ilyari sun ce an shafe tsawon lokaci awakinsu na ɓata kuma sun rasa ina suke shiga.

    Sai da wannan lamari ya faru suka gane cewa dama maciji ke haɗiye musu dabbobin idan suka shiga jeji kiwo.

    "Awaki da dama muka nema muka rasa a tsawon lokaci ashe maciji ne ke hallaka mana su," kamar yadda wani mazaunin garin ya zarga.

    • Ilyari a Shira: Garin da mutanensa suka kashe mesar da ta daɗe tana cinye musu awaki
  9. Ran shugaban Rwanda ya ɓaci saboda cin Arsenal da aka yi

    Paul Kagame

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Ƙasar Rwanda Paul Kagame ya nuna ɓacin ransa game da kashin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta sha a wasan farko na gasar Premier ta Ingila ta shekarar 2021-2022.

    Bayan shafe shekara 74 ba sa cikin gasar Premier, Brentford ta dawo kuma ta lallasa Arsenal da ci 2-0 a wasan na yammacin Juma'a.

    Mista Kagame ya sha yin tsokaci a kan Arsenal, ƙungiyar da gwamnatinsa ke ɗaukar nauyi.

    Jim kaɗan bayan kammala wasan, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Ba za mu taɓa lamuntar gazawa ba. Wajibi ne a gina ƙungiyar da za ta dinga yin nasara nasara nasara."

    Kazalika ya buƙaci a samar da "wani tsari da zai yi aiki" sannan ya nuna damuwa kan "bai kamata a saba wa magoya baya da irin wannan yanayin ba".

    Tun a 2018 ne gwamnatin Rwanda ta ƙulla yarjejeniyar da ta kai dala miliyan 42 da Arsenal, wadda ta sa ake rubuta "Visit Rwanda" wato "Ziyarci Rwanda" a hannun rigar ƙungiyar.

  10. Hotunan yadda Burtaniya ta aike sojojinta Kabul

    MoD Handout via PA

    Asalin hoton, MoD Handout via PA

    An saki hotunan dakarun Burtaniya da kasar ta aike zuwa birnin Kabul domin taimaka wa wajen kwaso 'yan Burtaniya da kuma jami'an ofishin jakadancinta da ke Kabul.

    Kimanin sojoji 6000 aka aike domin gudanar da wannan aiki.

    Burtaniya ta nemi duk 'yan kasarta su gaggauta ficewa daga Afghanistan saboda tabarbarewar yanayin tsaro.

    MoD Handout via PA

    Asalin hoton, MoD Handout via PA

    MoD Handout via PA

    Asalin hoton, MoD Handout via PA

  11. Labarai da dumi-dumi, Taliban ta sake ƙwace biranen lardi biyu

    Taliban

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Taliban ta sake kama wasu biranen lardi biyu na yankin Patika da Kunar.

    Ta kama garin Sharan na yankin Paktika da safiyar Asabar, a cewar shugaban majalisar yankin.

    Ya ce sashen tattara bayanan sirri da ofishin gwamna da hedikwatar 'yan sanda da kuma gidan yari duka suna ƙarƙashin ikon Taliban. Sharan yana da nisan kilomita 200 kudu da Kabul, babban birnin ƙasar.

    Asadabad wanda shi ne birnin yankin Kunar, ya faɗa hannun Taliban ne ranar Asabar, kamar yadda wani ɗan majalisa ya faɗa wa BBC.

    Wani bidiyo da ba a tabbatar da ingancinsa ba ya nuna wasu 'yan Taliban na ɗaga tutar ƙungiyar a kan titunan yankin.

    Asadabad na da nisan kilomita 235 gabas da Kabul.

    Yanzu haka Taliban na riƙe da fiye da rabin biranen lardunan ƙasar.

  12. Cikin al'amuran zamantakewa masu sarkakiya akwai batun riƙon 'ya'ya

    Bayanan bidiyo, Bidiyon Zamantakewa

    Daga cikin al'amuran zamantakewa masu matukar sarkakiya akwai batun riƙon 'ya'ya.

    A idanun al'umma, a mafi yawan lokuta iyayen riƙo ba sa tsira daga zarge-zarge da tuhume-tuhume, haka su ma 'ya'yan riƙon.

    Wasu Allah Ya kan ɗora musu nauyin riƙon ko dai 'ya'yan 'yan uwa marayu da ma waɗanda iyayensu ke rayen ko 'ya'yan miji ko 'ya'yan dangi ko na abokan arziki, kai wani lokacin ma har 'ya'yan da babu dangantakar jini.

    Sai dai za a yi ta jin gutsuri-tsoma, wance na cin zalin su wane, tana dukansu tana hana su abinci da sauran matsaloli.

    • Sarƙaƙiyar da ke cikin zamantakewar iyayen da ƴaƴan riƙo
  13. Me ya faru lokacin da Taliban ta taɓa ƙwace Kabul?

    Taliban

    Asalin hoton, Getty Images

    Shekarar 1996 ne lokaci na karshe da Taliban ta kwace iko da birnin Kabul, inda aka kakkafa tutocin Taliban a ofisoshin gwamnati.

    Abu na farko da suka fara yi shi ne kashe tsohon shugaban kasar Mohammad Najibullah a bainar jama'a.

    A karkashin dokar masu 'tawayen, an haramta wa mata yin aiki sannan an hana yara mata zuwa makaranta.

    Dole ne mata su rufe fuskokinsu sannan idan za su fita daga gida dole sai da dan rakiya namiji kuma muharraminsu (ɗan uwa na kusa).

    An kaddamar da yanke wa mutane hukunci kamar jefewa da yanke hannu.

  14. Gwamnati da 'yan adawar Venezuela na tattaunawa a Mexico

    Wakilai daga bangaren gwamnatin Venezuela da na yan adawa sun fara tattaunawar kawo karshen rikicin siyasa da ya jefa kasar cikin mawuyacin hali.

    Ana zaman sulhun ne a Mexico tsakanin bangarorin da ke tsananin adawa da juna.

    Wakilin BBC ya ce a baya an yi irin wannan zama har sau biyu amma an tashi barambaran.

    Sai dai wannan karon ga alama abubuwa za su sauya, saboda kowane bangare na ganin zai samu abin da yake so.

    Manya daga cikin batutuwan da za a tattauna a zaman sun hada da sakin fursunonin siyasa da kawo karshen takunkumin da aka kakaba wa gwamnatin Shugaba Nicolas Maduro.

    Haka ma bangaren adawar, sun ce dole ne a gudanar da sahihin zabe. A baya sun zargi Mista Maduro da amfani da karfin mulki wajen cin zabe.

  15. 'Saura kilomita 11 'yan Taliban su shiga birnin Kabul'

    Taliban

    Asalin hoton, EPA

    Wani ɗan majalisar dokoki ya shaida wa AFP cewa 'yan Taliban sun isa gundumar Char Asyab mai nisan kilomita 11 kacal daga kudancin babban birnin kasar, Kabul.

    Idan har gwamnati ta tabbatar da hakan, zai zama waje mafi kusa da birnin da suka kai kuma hakan babban koma-baya ne ga dakarun Afghanistan, wadanda ke yaki don hana Taluban shiga Kabul.

    Dubban fararen hula sun tsere zuwa wajen danginsu a Kabul, babban birnin Afghanistan don samun mafaka, yayin da Taliban ke ƙwace iko da birane a kasar.

    A yanzu masu tayar da kayar bayan suna kokarin shiga babban birnin, kuma wasu rahotanni na cewa jiragen yakin Amurka na kai hare-hare a inda 'yan Taliban suke a hanyoyin shiga gundumar Kabul.

    Rahoton baya-bayan nan na leken asiri na Amurka ya nuna cewa Taliban za ta yi kokarin kutsawa birnin Kabul cikin kwana 30.

    Kame birane da suke yi a kasar cikin mako guda da ya wuce na faruwa ne kamar kiftawar ido.

    Ko a jiya Juma'a sai da Taliban ta kwace Pul-e-Alam, babban birnin yankin Loghar, mai nisan kilomita 80 daga Kabul.

    A yanzu Taliban na iko da kusan rabin manyan biranen gundumomi bayan kwace muhimmai da suka hada da Kandahar, birni na biyu mafi girma a ƙasar.

  16. Canada za ta ɗauki 'yan gudun hijirar Afghanistan 20,000

    Canada

    Asalin hoton, @HarjitSajjan

    Jami'an Canada sun sanar da cewa za su faɗaɗa shirinsu na bai wa 'yan gudun hijira mafaka don ɗaukar 'yan Afghanistan kusan 20,000.

    Ministan da ke kula da sha'anin cirani, Marco Mendicino, ya shaida wa manema labarai cewa ƙasashe "na nuna shugabanci na gari" da wannan tsari, wanda zai mayar da hankali a kan wadanda suka fi fuskantar barazana da suka haɗa da masu fafutika da jagororin mata.

    "Abin da ke faruwa a Afghanistan yana karya zuciya kuma Canada ba za ta zuba ido ta kasa yin komai ba," kamar yadda Mr Mendicino ya fada a wani taron manrma labarai.

    Shi ma Ministan Harkokin Wajen Canada da ya halarci taron, Marc Garneau, ya ce kare jami'an diflomasiyyar kasar da ke Kabul shi ne abu mafi muhimmanci.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. Yadda taro kan rayuwar Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi II ke gudana

    Muna kawo muku yadda taro kan rayuwar Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi ke gudana kai-tsaye a Facebook.

    Ana gudanar da shi ne a ɗakin taro na Umaru Musa Yar'adua da ke birnin Kaduna a arewacin Najeriya.

  18. Ma'aikatan ƙasashen waje sun fara barin Afghanistan

    Afghanistan

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta ce ta fara aikin kwashe 'yan ƙasarta daga Afghanistan, inda dakaru 3,000 za su aiwatar da shi.

    Ta ce wasu daga cikinsu za su isa ƙasar a ranakun ƙarshen makon nan.

    Amurka ta ƙudiri aniyar kwashe dubban mutane daga birnin Kabul, ciki har da mafi yawan ma'aikatan ofishin jakadancinta da ke birnin.

    A gefe guda kuma Ingila, wadda za ta tura dakaru 600 don taimakawa wajen kwashe 'yan ƙasarta, ta ce za ta rage yawan ma'aikatan ofisoshinta matuƙa. Ita ma Jamus ta ce za ta yi hakan.

    Denmark da Norway za su rufe nasu ofisoshin jakadancin.

  19. Ana taro kan rayuwar Sarkin Kano Murabus Muhammadu Sanusi II

    Muhammadu Sanusi

    Sarakuna da masu riƙe da muƙaman gargajiya sun yi wa garin Kaduna tsinke a safiyar Asabar domin halartar taron shekara-shekara na murnar zagayowar ranar haihuwar Sarkin Kano Murabus Muhammadu Sanusi II.

    Yayin taron wanda shi ne irinsa na farko, masana da ƙwararru za su gabatar da makaloli.

    Taron na gudana ne a ɗakin taro na Umaru Musa 'Yar Adua da ke dandalin Murtala Square.

    Muhammadu Sanusi
    Bayanan hoto, Muhammadu Sanusi tare da sarkin Zazzau da sarkin Ringim da sarkin Awe
  20. An kori ɗan sandan Najeriya daga aiki kan zargin kashe mutum

    IGP Usman Alkali Baba

    Asalin hoton, NG Police

    Rundunar 'yan sandan Jihar Osun a kudancin Najeriya ta kori wani ɗan sanda daga aiki bisa zargin kashe wani mutum a kan babur a garin Osogbo.

    Kamfanin labarai na NAN ya ruwaito cewa Saja Adamu Garba ya harbe wani mai suna Saheed Olabomi ranar 27 ga watan Yuli.

    A cewar kakakin 'yan sandan jihar, SP Yemisi Opalola, an kori jam'in ne bayan gudanar da shari'ar cikin gida.

    "Kamar yadda Kwamishinan 'Yan Sanda Olawale Olokode ya yi alƙawari za a bayyana sakamakon shari'ar...an yi wa F/NO.467549 Sergeant Adamu Garba shari'a bisa ƙa'idojin aikin ɗan sanda na Najeriya," a cewar wata sanarwa.

    "An samu ɗan sandan da laifin aikata zargin da ake yi masa kuma aka kore shi daga rundunar. An tura wa hedikwatar 'yan sanda da ke Abuja hukuncin shari'ar domin ɗaukar matakin gurfanar da shi a gaban kotu."

    Kwamishinan ya ce yana fatan hukuncin zai zama darasi ga sauran 'yan sanda.