'An kama Sunday Igboho a Cotonou yana ƙoƙarin guduwa Jamus'
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, amma zai fi mayar da hankali ne a kan bukukuwan Babbar Sallah.
Rahoto kai-tsaye
Halima Umar Saleh
Rufewa
Asalin hoton, Halima
Bayanan hoto, Halima Umar Saleh ke cewa mu kwana lafiya a kuma ci naman sallah lafiya.
Masu bin mu a wannan shafi barkanku da yamma, da fatan Allah Ya karbi layyarmu.
A nan muka kawo karshen labarai da rahotanni na wasu abubuwan da suka faru a Najeriya da sauran sassan duniya, ciki har da bukukuwan sallah.
Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.
Kuna iya komawa ƙasan shafin don karanta muhimman abubuwan da suka faru a duniyar tamu a yau.
Halima Umar Saleh ke cewa mu kwana lafiya a kuma ci naman sallah lafiya.
Wasu hotunan yadda aka yi shagalin sallah a Afirka
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Waɗannan iyalan sun sha kwalliyar sallah a filin Idi a babban Masallacin Yawunde na Jamhuriyyar Kamaru
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Waɗannan masu ibadar sun halarci Sallar Idin Layya a wani masallaci a Conakry babban birnin Guinea
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Yara na wasa da balam-balam a wajen Sallar Azahar a Masallacin al-Azhar a Alƙahira na Masar
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Mutane na Sallar Idi a Masallacin da ke Dandalin al-Farah a Khartoum babban birnin Sudan
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wannan yarinya ta sha gayu ana ɗaukar ta a hoto bayan kammala Sallar Idin Layya a wani masallaci na kasuwar dabbobi ta Kara a Najeriya
Birtaniya ta buƙaci Najeriya ta mata bayani kan yadda aka kama Nnamdi Kanu
Asalin hoton, AFP
Birtaniya ta buƙaci Najeriya da ta yi bayani kan inda da kuma yadda ta kama jagodan ƴan awatren Biafra Nnamdi Kanu.
Nnamdi Kanu - jagoran ƴan awaren Biafra ya gudu daga Najeriya yana ɓoye a wani waje tsawon shekara hudu, har sai zuwa lokacin da aka gurfanar da shi a gaban kotu a Abuja a watan da ya gabata.
Ana tuhumarsa da laifuka da dama da suka haɗa da cin amanar ƙasa.
Lauyoyinsa sun ce an tsare shi kuma an wulaƙanta shi a Kenya kafin kawo shi Najeriya.
Wani ƙaramin minista a Ofishin Harkokin Wajen Birtaniya, Tariq Ahmad, ya ce gwamnatin Birtaniya na neman ƙarin bayani daga gwamnatin Najeriya kan yadda aka kai ga tsare Mista Kanu.
Manoma na kokawa da tsadar taki a Jamhuriyyar Nijar
Manoma na kokawa da tsadar taki a Jamhuriyyar Nijar, duk da alƙawarin da shugaban ƙasar Mohamed Bazoum ya yi na samar da takin wadatace a farashi mai rahusa a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
A daidai wannan lokaci da ruwan sama ya fara sauka a wasu yankunan kasar ta Nijar, tuni wasu manoman suka fara shuka.
Wasu manoman ma suna ƙorafin cewa lamarin takin zamani zai gagari talaka a bana.
Alhaji lawali Sa'idou, Sarkin moman jihar Katsanar Maradi yankin Gidan-Runji ya yi wa Abdou Halilou karin bayani:
Bayanan sautiHirar Abdou Halilou da Alhaji Lawali Sa'idou Sarkin manoman Katsinar Maradi a Nijar
'An kama Sunday Igboho a Cotonou yana ƙoƙarin guduwa Jamus'
Asalin hoton, Sunday Igboho
Rahotanni daga Najeriya na cewa an kama mai fafutukar kafa kasar Yarbawa
zalla a shiyyar kudu maso yammacin kasar wato Sunday Adeyemi wanda aka fi sani
da Sunday Igboho.
Labarin kamen nasa na zuwa ne makonni uku bayan da jami'an ƴan sandan ciki na ƙasa suna yi dirar mikiya a gidansa da ke Ibadan.
Sun yi hakan ne kwana uku gabanin ranar gudanar da wani gagarumin gangamin 'yan kabilar Yarbawa da ya
kira a birnin Legas.
To bayanan da Haruna Tangaza na BBC Hausa ya tattara daga majiyoyin daban-daban na nuna cewa an
kama Sunday Igboho ne jiya da yamma a filin jirgin sama na Cotonou na kasar Benin mai makwabtaka da Najeriya.
Manyan kafafen watsa labarai
daban-daban a Najeriya sun ce an kama shi ne yana ƙoƙarin hawa jirgi domin
arcewa zuwa kasar Jamus, bayan da su jami'an ƴan sandan ciki suka ayyana shi a
zaman wanda ake nema.
To ko muna da
labarin a inda yake yanzu?
To bisa
rahotannin da BBC ta samu dai yau ne aka ce su hukumomin kasar ta Benin za su
hannunta shi ga mahukuntan Najeriya.
Sai dai abin babu tabbas akai shi ne ko
kawo zancen nan da muke an riga an miƙa shi ko kuma a'a.
Sai dai jaridu
daban-daban sun ambato wasu fitattun ƴar ƙabilarsa ta Yoruba wadanda suka
tabbatar da labarin kamen nasa na cewa suna ƙoƙarin shawo kan hukumomin kasar ta
Benin don ka da su amince su taso keyarsa zuwa nan Najeriya.
Misali an ambato shugaban
gamayyar kungiyoyin neman ƴancin cin gashin kan al'ummar Yarbawa ta Ilana Omo
Oodua Farfesa Banji Akintoye, na cewa shi da sauran masu kishin ƙabilar Yarbawa
suna aikin tare domin bai wa Sunday Igboho duk wani taimakon da yake bukata.
Sannan za su tabbatar da babu wanda ya yi masa wani da doka ta hana da kuma hana taso ƙeyarsa zuwa Najeriya.
Naman sallah na shan suya
Himma ba ta ga rago, ƙamshin suyar nama ya fara tashi a wurare da dama a fadin duniya.
Ga wasu hotuna na yadda wasu suka duƙufa aikin nama.
Asalin hoton, Sadiq Elnafaty
Asalin hoton, Sadiq Elnafaty
Yadda aka yi Idin Babbar Sallah a Masallacin Annabi na Madina
Ga wasu hotuna na yadda aka yi Idin Babbar Sallah a Masallacin Annabi na Madina
Alhazai sun gudanar da manyan ayyukan Hajji huɗu
Asalin hoton, Saudi Gazette
Mahajjata sun gudanar da manyan ayyuka huɗu na Hajji a yau 10 ga watan Dhul Hijjah, wacce aka fi sani da Yaum Al-Nahr ko ranar yanka.
Bayan da suka isa Mina daga Muzdalifah da safiyar yau, sun gabatar da jifan shaiɗan a Jamrah sannan suka tafi Makkah suka yi ɗawafin Ifadah na ranar sallah da Safa da Marwah.
Manjo Janar Mohammed Al-Bassami, kwamandan Dakaru Na Musamman kan Hajji da Umara, ya ce shirye-shiryen tafiyar mahajjatan don yin ɗawafin sun tafi kamar yadda aka tsara Hajjin na bana ya kasance.
Hukumar da ke kula al'amuran Masallatai Biyu Masu Daraja da sauran hukumomi ke kula da tsarin shigar mahajjatan cikin Masallacin Ka'aba, inda alhazan ke shiga ta ƙofofi daban0daban don hana cunkoso.Alhazai za su ci gaba da jifan shaiɗan har nan da kwana uku masu zuwa.
Kalli bidiyon yadda Shugaba Buhari ya koma gida bayan Sallar Idi a Daura
Kusan mutum miliyan 4.5 cutar korona ta kashe a Indiya
Asalin hoton, Reuters
Wani bincike da aka gudanar game da mace-macen da ke da alaƙa da cutar korona a Indiya, ya nuna cewa mace-macen za su iya kai wa miliyan hudu da rabi - fiye da alƙaluman da hukumomi suka bayar har fiye da ninki goma.
Wata cibiyar gudanar da binciken da ke Amurka ta kalli yadda mutane da dama suka mutu fiye da yadda aka yi tsammani.
Masu binciken sun yi amfani da bayanai daban daban guda uku domin kai wa ga kiyasinsu.
Idan har hakan daidai ne, to sun ce annobar ta kasance wani bala’i mafi muni da ya shafi bil adama ta aka taɓa gani a Indiya tun daga lokacin da kasar ta sami ‘yancin kai.
Mawallafan binciken sun ce nazarin da suka yi ya saba da ikirarin da Indiya ta yi na cewa kasar na daya daga cikin kasashen duniya da ke da karancin mace-macen dake da alaka da cutar korona.
Yadda Shugaba Mohammed Bazoum na Nijar ya yi Sallar Idi
Wannan wasu hotuna ne da ke nuna yadda Shugaba Mohammed Bazoum na Jamhuriyyar Nijar ya yi Idin Sallar Layya.
Ya wallafa su ne a shafinsa fadar gwamnatin ƙasar na Tuwita.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
An yi ƙoƙarin caka wa shugaban Mali wuƙa a wajen Sallar Idi
Asalin hoton, Getty Images
Wasu mutane sun yi ƙoƙarin caka wa shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya ta Mali Assimi Goïta wuƙa a masallaci, a babban birnin ƙasar Bamako.
Kanal Goïta ya je babban masallacin ne domin yin Idin Sallar Layya.
Hukumomin sun ce an kama waɗanda suka kai masa harin, waɗanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce su biyu ne, sannan a yanzu shugaban ƙasar yana halin lafiya.
Babu tabbacin ko Kanal Goita, wanda ya jagoranci juyin mulkin ƙasar a watan Agustan bara ya ji rauni.
Ministan Harkokin Addinai Mamadou Kone ya shaida wa AFP cewa wani mutum ya yi ƙoƙarin kashe shugaban ƙasar ne da wuƙa."
Daraktan masallacin ya cewa AFP mutumin ya yi niyyar caka wa shugaban ƙasa wuƙar ne amma sai ya samu wani daban.
Kafin juyin mulkin Agustan bara, ƙasar ta fuskanci jerin zanga-zanga kan adawa da cin hanci da ta'addancin masu ta da ƙayar baya.
Kanal Goïta ya sake shiga tsakani a watan Mayu, inda ya maye gurbin wata gwamnatin riƙon ƙwarya a matsayin shugaban ƙasa - amma ya yi alƙawarin miƙa mulki ga farar hula kamar yadda aka tsara a baɗi.
Kwalliyar sallar wasu sarakuna a Najeriya
Asalin hoton, Khalifa Studio
Bayanan hoto, Sarkin Kano Aminu Ado Bayero
Asalin hoton, Khalifa Studio
Bayanan hoto, Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje
An haramta wa ƴan fim sa kayan ƴan sanda a Mozambique
Asalin hoton, Comandante Faísca/Facebook
Bayanan hoto, Wani ɗan fim Aranica Pagere yana yawan sa kakin ƴan sanda a fina-finansa na baya-bayan nan
Shugaban ƴan sandan Mozambique Bernardino Rafael ya bayar da umarnin haramta wa fararen hula saka kakin ƴan sanda ciki har da yan fim.
Ya ce ana amfani da kakin ta wajen nuna rashin ƙimar aikin rundunar, amma ƴan fim sun ce matakin na "kama karya ne."
Wani ɗan fim Aranica Pagere, wanda aka fi sani Comandante Faísca, yana yawan sa kakin ƴan sanda a fina-finansa na baya-bayan nan, ya kuma matakin "babu hankali a ciki," kuma ƴan fim ba za su zuba ido ba.
Hukumomi sun ce an ɗauki matakin ne don kare martabar ƙasar,
Wani lauya Osvanildo Mathe ya ce amfani da kakin ƴan sanda a wajen yin fim ba mummunan abu ba ne, kuma shugaban ƴan sandan ba shi da hurumin da zai ɗauki matakin kan ƴan fim ɗin da ba ƙarƙashinsa suke aiki ba.
Asalin hoton, AFP
An harba rokoki shugaban ƙasa yana tsaka da Sallar Idi a Afghanistan
An harba rokoki zuwa Kabul babban birnin Afghanisatan, suka kuma fashe kusa da fadar shugaban kasa.
An ji karar fashewar kai tsaye a gidan talabijin na gwamnati wanda a lokacin ke watsa addu'o'i da Sallar Idi da Shugaba Ashraf Ghani ke halarta.
Da dama cikin masu ibadar Babbar Sallar, sun firgita amma dai sun ci gaba da ibadar duk da fashewar da ta faru a kusa da su.
Da yake jawabi bayan da aka idar sallar, Shugaba Ghani ya ce Taliban ba ta da muradin zaman lafiya.
Babu dai tabbas kan hasarar rayuka ko jikkata.
Bayanan bidiyo, Kalli bidiyon yadda aka harba rokokin shugaban ƙasa na Sallar Idi a Afhganistan
Ƴan kwana-kwana 2,000 na ƙoƙarin shawo kan gobarar daji a Amurka
Asalin hoton, Getty Images
'Yan kwana-kwana fiye da 2,000 na ta ƙoƙarin shawo kan wata gobarar daji a jihar Oregon ta Amurka.
Wutar da ake wa laƙabi da Bootleg Fire, ta tilasta wa dubban mutane barin gidajensu galibi a yankunan karkara, kuma ta ƙona fiye da muraba'in kilomita 1,200.
Ta kuma lalata gine-gine fiye da 160 kawo yanzu.
Wannan wutar da ta kama makwanni biyu da suka gabata, ita ce mafi girma cikin wutar daji fiye da 80 da ke ci a fadin Amurka.
Saƙonnin Barka da Sallah daga wasu manyan ƴan Najeriya
Wasu masu tuwa da tsaki a Najeriya daga malamai zuwa ƴan siyasa da ƴan kasuwa da manyan ma'aikatan gwamnati suna ta wallafa hotunansu na kwalliyar sallah a shafukan sada zumunta tare da yi wa al'ummar Musulmai barka da sallah.
Ga wasu daga cikinsu:
Mai kuɗin duniya Jeff Bezos zai tafi ƙololuwar sararin samaniya a sabon jirgin rokarsa
Asalin hoton, Blue Origin
Mai kuɗin duniya Jeff Bezos zai tafi shawagi ƙololuwar sararin samaniya a yau Talata a cikin sabon jirgin rokarsa mai suna New Shepard.
Zai yi bulaguron ne ƙarƙashin rakiyar ƙaninsa Mark Bezos da Wally Funk, wata mai shekara 82 da aka fara rige-rigen zuwa sararain samaniya da ita da kuma wani ɗalibi mai shkeara 18.
Za su yi tafiyar ne a cikin wata roka mai manyan tagogi da za su ba su damar kallon yadda ƙwallon duniyarmu take daga sama.
Jirgin New Shepard, wanda kamfanin Bezos mai suna Blue Origin ya ƙera, an yi shi ne don bunƙasa zuwa yawon buɗe ido zuwa ƙololuwar sararin samaniya.
"Na ji dadi sosai. Mutane suna ta tambayata ko ina jin tsoro. Gaskiya ban ji wani tsoro ba. Na ƙagu. Na zaƙu na je na ga me zan koya a tafiyar," a cewar Bezos a wata hira da kafar yaɗa labaran CBS.
"Mun yi ta atisaye. Wannan abin hawan ya shirya, sauran matafiya sun shirya, tawagar ta haɗu. Muna cikin jin daɗi dangane da hakan," ya ƙara da cewa.
Asalin hoton, Blue Origin
Sarki Muhammadu Sanusi ya jagoranci Sallar Idi a Kaduna
Asalin hoton, Kaduna Gov Facebook
Mai Martaba tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya jagoranci Sallar idi a Kaduna tare da Gwamna Nasir el-Rufa'i na jihar.
Gwamna El-Rufa'i ne ya wallafa hotunan yadda Sallar Idin ta kasance a Masallacin Idin Murtala Square.\
Ya kuma wallafa saƙon barka da sallarsa ga al'ummar jihar Kadunan inda ya taya su murnar zagayowar wannan rana.
Sannan ya yi kira ga mutane da su yi addu'a ga jihar da ƙasar baki ɗaya a wannan yanayi mai wahala da ake ciki kamar yadda sanarwar ta ce.
Ga dai wasu hotuna na yadda sallar ta kasance.
Asalin hoton, Kaduna Gov
Asalin hoton, Kaduna Gov
Asalin hoton, Kaduna Gov
Shugaba Biden ya gana da Sarki Abdullah na Jordan
Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Biden na Amurka ya tattauna da Sarkin Jordan a Fadar White House - ganawa irinta ta farko da ya yi da wani shugaban kasar Larabawa tun da ya hau karagar mulki a watan Janairun da ya gabata.
Shugaban ya yaba wa Sarki Abdullah a matsayin aboki na ƙwarai kuma mai biyayya, kana ya ce a ko yaushe Amurka za ta taimaka wa Jordan.
An shirya Sarkin wanda ya tsallake wani yunkurin juyin mulki da dan-uwansa ya yi a watan Afirilun da ya gabata, zai yi wani zaman karin kumallo mai nasaba da aiki tare da mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris a yau Talata.