Shugaban kasar Ghana ya buɗe babban masallacin kasa a Accra

Wannan shafin na kawo muku rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur, Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge

  1. Kungiyar Amnesty ta ce gwmamnatin Habasha na tsare da 'yan Tigray ba a bisa ka'ida ba

    Abiy Ahmed

    Asalin hoton, Reuters

    Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin Habasha da ta dauki matakin saki ko tuhumar dimbin ‘yan kabilar Tigray da ta tsare ba bisa ka’ida ba cikin makonni biyu da suka gabata.

    Amnesty ta ce da alama kamun na da nasaba da tsantsar kabilanci. Sanarwar ta ce an rika kama 'yan kasuwa da kwastomominsu, da masu fafutuka da' yan jarida.

    Kungiyar mai zaman kanta ta ce an saki wasu daga cikin mutanen da aka kama bayan bada belinsu, sai dai da yawa na ci gaba da kasancewa a tsare kuma babu wanda ya san inda suke.

    An tsare mutanen ne bayan da sojojin ‘yan tawayen Tigray suka sake kwace iko da babban birnin yankin, Mekelle, daga sojojin gwamnati a watan jiya.

  2. Budewa

    Barkanku da kasancewa da wannan shafin wanda ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta kamar Nijar da Chadi da Ghana da Kamaru da kuma sauran kasashen duniya.