Shugaban kasar Ghana ya buɗe babban masallacin kasa a Accra

Wannan shafin na kawo muku rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur, Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge

  1. Ban kwana

    Buhari Fagge ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Shugaban kasar Ghana ya buɗe babban masallacin kasa a Accra

    Ghanian Presidency

    Asalin hoton, Ghanian Presidency

    hugaban ƙasar Ghana Nana Akufo-Addo ya kaddamar da babban masallacin kasar a Accra babbab birnin Ghana a ranar Juma a 16 ga watan Yuli.

    Masallacin wanda shi ne na biyu mafi girma a Afrika ta Yamma yana da Ofishin babban limamin kasa da asibiti da dakunan gwaji da wurin sayar da magani da dakin karatu da kuma wajen ajiye gawa.

    Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook shugaban ya ce buɗe masallacin ya samu halartar manyan baki ciki har da wasu shugabanni daga kasashen ketare.

    Shugaban ya wallafa hotunan bude masallacin akalla sun kai 40.

    Bayan nan kuma shi da wasu jagororin kasar sun nuna girmamawarsu ga shugaban Nijar da ya bar gado Mahamadou Issoufou, wanda Shugaba Nana ya bayyana a matsayin "Aboki kuma dan uwa" wanda ya jagoranci tabbatar da kungiyar kasuwanci kasashen Afrika mara shinge.

    Ghanian Presidency

    Asalin hoton, Ghanian Presidency

    Ghanian Presidency

    Asalin hoton, Ghanian Presidency

  3. Amurka ta gargaɗi kamfanonin ya kasar da ke harkoki a China

    G

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin shugaba Joe Biden ta fitar da jerin shawarwari ga kamfanonin Amurka da ma'aikatansu da ke gudanar da harkokin kasuwancinsu a Hong Kong, biyo bayan abunda Amurka ta kira kakagidan China wajen kakaba dokokin da ke take hakkin dan adam a yankin.

    Amurka ta shaida cewa akwai bukatar kamfanonin su fahimci dokokin na China, ka iya jefa su cikin hadarorin shari'a da asarar kudade har ma da bata musu suna.

    A wani mataki na nuna damuwarta game da ayyukan China a yankin na Hong Kong, Amurka ta sanya wa wasu yan kasar China 7 takunkumi, kan zarginsu da hannu wajen dakile dimokaradiya a yankin na Hong Kong.

    Sai dai ma'aikatar harkokin wajen China ta yi gargadin cewa, kasar ba za ta lamunce ko wanne na'auin tsoma bakin Amurka ga harkokin cikin gidanta ba.

  4. 'Shaiɗanu' ne suka yi zanga-zangar ƙyamar sarauta - Sarkin Eswatini

    Sarki Msawti na III

    Asalin hoton, AFP

    Sarkin masarautar Eswatini Sarki Msawti na III ya bayyana cewa "shaidanu" ne suka gudanar da zanga-zangar kyamar masarautarsa.

    Ya bayyana haka ne karon farko da yake tsokaci kan batun tun bayan zanga-zangar da wasu suka yi a watan jiya.

    Ya ce mutanen, wadanda suka yi kone-kone, sun koma da kasar baya sannan ya sanar da ware $35m (£25m) domin biyan kudin kayayyakin da suka lalata.

    Mutum akalla 50 ne suka mutu a kasar ta Afirka wadda ita ke take bin tsarin sarauta.

    Ranar Juma'a, 'yan sanda sun yi amfani da barkonon-tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar a birnin na biyu mafi girma, Manzini.

    Masu goyon bayan 'yan adawa sun yi kira a gudanar da sabuwar zanga-zanga duk da gayyatar da Sarki Mswati na III ya yi musu domin a tattauna kan korafe-korafensu.

  5. Ana zanga-zanga kan rashin aikin yi a Algeria

    Masu zanga-zanga a lardin Ouargla da ke da arzikin man fetur na Algeria sun rufe hanyoyi sanna suka kona tayoyi inda suka nemi a ba su ayyukan yi da kuma aiwatar da ayyukan ci gaba a yankin.

    Lardin na Ouargla, wanda ke kudancin Algeria, shi ne yake da kashi 71 na man fetur din da ake samu a kasar.

    Sai dai mazauna yankin suna zargin cewa ba a yi musu adalci wajen samar da ababen more rayuwa idan aka kwatanta da yankin arewacin kasar.

    Masu zanga-zanga sun ce kamfanin man kasar Sonatrach ya fi daukar ma'aikata daga arewacin kasar.

    An kiyasta cewa talaucin da ake fama da shi a kudancin kasar Algeria ya ninka wanda ake fama da shi a arewaci.

  6. WhatsApp ya toshe shafuka miliyan biyu a India

    WhatsApp

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin WhatsApp ya ce ya toshe shafuka sama da miliyan biyu a kasar India daga watan Mayu zuwa Yuli saboda karya dokoki.

    Kamfanin ya ce kashi 95 bisa dari na wadannan masu amfani da manahajar tasa suna karya dokokin da aka kayyade na adadin sakonnin da za a rika turawa a kasar India.

    WhatsApp din ya sanar da hakan ne a rahotonsa na wata-wata na farko kan bin dokoki a karkashin sabuwar dokar kasar India kan harkokin fasahar sadarwa masu cike da ce-ce-ku-ce.

    Kasar India ce kasuwar kamfanin na WhatsApp mafi girma a duniya, inda mutum kusan miliayan 400 da ke amfani da manahajarsa.

    WhatsApp din, wanda mallakar kamfanin Facebook ne, ya ce manyan abubuwan da ya mayar da hankali a kai su ne hana masu amfani da manahajarsa a kasar India aikewa da sakonni masu illa ko kuma marasa amfani da suka kai wani mataki.

    Ta hanyar amfani da na’urorin fasahar zamani ne, WhatsApp din ke haramta wa mutane masu amfani da shi kusan miliyan takwas damar shiga manahajarsa a fadin duniya a kowane wata.

  7. An yi jana'izar Manjo Janar Huseini Ahmed

    Gawar Janar Huseini

    Asalin hoton, Facebook/HQ Nigerian Army

    An yi jana'izar Manjo Janar Huseini Ahmed wanda 'yan bindiga suka kashe bayan sun far wa a motarsa a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja Alhamis.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya Birgediya Janar Onyema Nwacukwu ya fitar ta ce an binne Janar din sojin ne a makabartar sojoji da ke Abuja ranar Juma'a.

    Babban Hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya, wanda ya halarci jana'izar, ya bayyana tsohon janar na sojin da mutum mai nutsuwa da ya kware a aikinsa.

    An haifi Manjo Janar ranar 16 ga watan Fabrairun 1968 a birnin Maiduguri na jihar Borno.

    Ya yi karatun firamare da sakadanre a jihar Benue, inda daga bisani ya shiga makarantar sojoji ta Nigerian Defence Academy (NDA) a 1988.

    Marigayin ya yi digirinsa a kan harkoin siyasa da sha'anin tsaro, yayin da ya yi digirinsa na biyu a kan tsare-tsaren yaki.

    Ya rike mukamai da dama ciki har da shugaban makarantar sojoji.

    Gawar Janar Huseini

    Asalin hoton, Facebook/HQ Nigerian Army

  8. 'Yar wasan kwaikwayon India Surekha Sikri ta rasu

    Surekha Sikri

    Asalin hoton, Getty Images

    An bayyana tauraruwar fina-finai da kuma wasan dandali ta kasar India Surekha Sikri a matsayin ’yar wasa "mafi shahara" da kuma "mai kwazo da hazaka", bayan mutuwarta tana da shekaru 75.

    Gogaggiyar tauraruwar fina-finan, wacce aka san ta a fina-finai kamar su Badhaai Ho, da shirye – shiryen gidan talabijin kamar Balika Vadhu da sauran wasannin India na dandali da dama, ta yi fama da ciwon bugun zuciya a birnin Mumbai.

    Sikri ta lashe kyaututtukan fina-finai na kasa uku na a tsakanin shekarar 1988 da 2018 kuma ta fito a matsayin tauraruwa a shahararren jerin wasan kwaikwayo na Balika Vadhu har na tsawon shekaru takwas.

    Sikri, wacce aka haifa a birnin New Delhi, ta lashe kyaututtukan fina-finai na kasa kan fina-finan Tamas da Mammo da kuma Badhaai Ho.

    Mai shirya fina-finai Shyam Benegal, wanda ya yi aiki tare da ita a fim din Mammo, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Press Trust of India cewa: "Tauraruwar fina-finai ce mai basira wacce duk matsayin da aka ba ta takan yi fice a kan shi.

    "Takan fito a matsayi na ban tausayi da kuma na rashin tausayi cikin hazaka. Ta kasance tauraruwar fina-finai mafi kwazo da kuma gogewa."

  9. Majalisar wakilan Najeriya ta zartar da kudurin gyaran-fuska ga dokar zabe da harkar mai

    Bayanan sautiMajalisar wakilan Najeriya ta zartar da kudurin gyaran-fuska ga dokar zabe da harkar mai

    Majalisar wakilan Najeriya ta zartar da kudurin gyaran-fuska ga dokar zabe da na inganta harkar mai.

    Sai dai takwarorin `yan majalisar daga babbar jam`iyyar hamayya ta PDP sun fice daga zauren majalisar a a lokacin da suke zaman.

    A jiya ne zaman ya cije sakamakon rashin jituwa a kan maganar amfani da laturoni wajen kada kuri`a da sanar da sakamakon zabe.

    Latsa hoton da ke sama don sauraren rahoton Ibrahim Isa:

  10. An kashe wani dan jarida a bakin aiki a Afghanistan

    Wani kwamandan dakarun Afghanistan ya ce an kashe wani dan jarida mai suna Danish Siddiqui wanda ke aiki da kamfanin dillanci labarai na Reuters.

    Dan jaridar ya rasu ne a lokacin da yake daukar bayanan yakin da ake yi tsakanin jami'an tsaro da mayakan Taliban a kusa da kan iyakar Afghanistan da Pakistan.

    Bayanai sun ce an kashe shi tare da wani babban jami'in tsaro.

    Siddiqui wanda dan kasar India ne, yana aikin dauko rahotanni tare da dakarun Afghanistan na musamman da ke Kandahar tun a farkon wannan makon.

    Danish Siddiqui ya samu lambar yabo a hotunan da ya dauka na matsalar 'yan ci-rani na kabilar Rohingha a shekarar 2018. Kamfanin Reuters ya bayyana shi a matsayin hazikin dan jarida.

  11. Kashi 50 cikin 100 na rumfunan zaben Najeriya ba su da intanet- NCC

    Majalisar Wakilai

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar NCC a Najeriya ta ce kasa da kashi 50 cikin dari na rumfunan zabe a Najeriya ne ke da intanet din da za a iya aika sakamakon zabe.

    Dama dai majalisar wakilan kasar ce ta gayyaci NCC don yi mata bayani kan yawan layukan intanet a Najeriya kafin ta ci gaba da tattaunawa kan duba yiwuwar aikawa da sakamakon zabe ta intanet a lokacin babban zaben kasar.

    Wani jami'in hukumar Adeleke Adewolu ya bayyana haka ranar Juma'a a lokacin da ya ke bayani a gaban majalisar kan layukan intanet na kasar.

    Ranar Alhamis ne majalisar wakilai ta Najeriya ta yanke shawarar gayyatar hukumar ta NCC don jin ta bakinta kan kwaskwarimar da aka yi wa dokar Zabe ta kasar.

    Mista Adewolu ya bayyana wa majalisar cewa kasa da kashi 50 cikin 100 na rumfunan zabe a kasar ke da layin intanet na 3G da ake bukata don aikewa da sakamakon zabe.

    Ya kuma ce wasu rumfunan zaben na da layin 2G yayin da wasu ba su ma da intanet din gaba daya.

  12. 'Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a wani hari a Sokoto

    Bindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu 'yan bindiga sun kashe sojojin Najeriya biyu sannan sun ji wa wasu da dama rauni tare da yin garkuwa da wasu a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

    Harin ya faru ne ranar Alhamis a Unguwar Lalle ta garin Sabon Birni.

    Wani mazaunin yankin Bashir Usman Gobir ya bayyanawa BBC cewa an kashe sojojin biyu ne a lokacin da suka yi kokarin korar maharan inda suka yi musayar wuta da 'yan bindigar.

    Ya ce maharan sun isa garin ne a kan babura dauke da bindigogi

    Ya kuma ce an yi garkuwa da wani ma'aikacin lafiya da wasu mutane a unguwar a lokacin kai harin.

    Rundunar 'yan sanda ta jihar Sokoto ta bayyana cewa baya ga mutane da aka yi garkuwa da su, maharan su yi awon gaba da dabbobi da dama.

    Za a iya cewa irin wadannan hare-haren 'yan bindiga kan garuruwa da manyan hanyoyi sun zama jiki a Najeriya; amma irin yadda 'yan bindigar ke murje ido su yi gaba-da-gaba da jami'an tsaro kuma su kashe su na kara razana 'yan kasar.

    Ko a ranar Talata wannan makon dai sai da wasu 'yan bindigar suka kashe wasu sojojin kasar biyu a jihar Enugu cikin wani hari da suka kai musu.

  13. Za a rika bude kantina a Saudiyya a lokutan da ake gudanar da sallolin farilla

    Saudi Shops

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a rika bude kantina da sana'o'i a Saudiyya a lokutan Sallar farilla, a wani mataki da ya yi kama da sassauta dokokin musulunci a masarautar.

    Wata sanarwa da ta fito daga Ma'aikatar Kasuwanci ta Saudiyya ta ce matakin na cikin matakan da aka dauka saboda cutar korona, don takaita taron mutane da ke cincirindo a lokacin da shaguna suke a rufe a lokacin da a ke gudanar da salloli a masallaci.

    Ba a sani ba ko wannan matakin zai zama na din-din-din amma wani mai sa ido kan al'amuran Saudiyya ya ce mataki ne mai muhimmanci.

  14. Sama da mutum 100 sun mutu a ambaliyar ruwa a Jamus

    Germany

    Asalin hoton, EPA

    Sama da mutum 100 ne suka mutu sannan daruruwa sun bata a Jamus bayan ambaliyar ruwa mai muni.

    Ruwan sama kamar da bakin kwarya a yammacin Turai da ya haifar da ballewar bakin koguna ya dai-daita yankin.

    Belgium ma ta bayar da rahoton mutuwar mutum 12 bayan mamakon ruwan saman da shugabanni suka ce sauyin yanayi ne ya haifar da shi.

    Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta yi alkawarin tallafa wa wadanda abin ya shafa.

    A Jamus, jihohin Rhineland-Palatinate da North Rhine-Westphalia su ne lamarin ya fi shafa.

    Kasar Netherlands ma na cikin yankunan da ambaliyar ta shafa, da Luxembourg da Switzerland.

  15. Gwamnatin jihar Legas ta rufe kamfanonin ruwan sha 30 a jihar

    Hukumar da ke sa ido kan tsaftace ruwa a Legas (LASWARCO) sun rufe masana’antu 30 bisa wasu laifuka da suka hada da rashin samar da tsaftataccen wurin aiki da kuma kin bin dokokin hukumar.

    Babbar sakatariyar hukumar Mrs Funke Adepoju ta ce hukumar ta rufe masana’antun ne bisa ka’idar tsare mutanen gari daga shan gurbataccen ruwa. Ta kuma ce za a ci gaba da aiwatar da hakan.

    Ta ce: "Duk da cewa alhakin tabbatar da cewa masana’antu sun kasance a bude na kanmu, ba shi zai sa mu bari a ci gaba da aikata laifuka ba, ba tare da mun yi magana ba. Babban aikinmu shi ne tabbatar cewa masana’antu da ke samo ruwan sha sun ci gaba da bin dokoki domin tsare lafiyar al’umma.

    "Tawagarmu ta ziyarci wasu masana’antu da kayan gwaji kuma sakamakon da aka samu ya nuna cewa yawancin masana’antun na aiki ba yadda ya kamata ba, wanda hakan ka iya zama hadari ga mutane. Kamar yadda dokar kare muhalli ta bangaren dokar 313 da aka fitar a shekarar 2017 ta tanada, muna da ikon sanya ido kan masu samar da ruwan sha a kwalabe ko kuma ledodi, babban aikinmu shi ne tabbatar da an yi aikin kan tsari da doka.

  16. Shirye-shiryen sauya wa dakin Ka'aba riga

    Kiswa

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    Kiswa

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    Kiswa

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    Kiswa

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

  17. 'Yan sanda sun kashe wani shugaban masu garkuwa da mutane a Jigawa

    Police

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan sanda a jihar Jigawa sun kashe wani shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane mai suna Abdullahi Bummi.

    An kashe shugaban 'yan bindigan ne a wani samame kan inda suke boyewa a Gallu, karamar hukumar Yankwashi a jihar.

    Haka kuma 'yan sanda sun ceto wata mata mai shekara 65 a samamen da aka gudanar a wani aikin hadin gwiwa na tsakanin rundunonin 'yan sanda na jihar Katsina da Jigawa.

    Jami'in hulda da jama'a na jihar Katsina, SP Gambo Isah ya shaida wa manema labarai cewa an sace matar da aka ceto ce, mai suna Hajiya Hasana Zubairu ran 29 ga watan Yunin wannan shekarar a karamae hukumar Sandamu ta jihar Katsina.

  18. 'Yan bindiga sun kashe wani Janar din Sojan Najeriya a Abuja

    Major Janar Faruk Yahaya

    Asalin hoton, Facebook

    Rundunar sojin Najeriya ta sanar da kashe Manjo Janar Hassan Ahmed na rundunar.

    Ta sanar da cewa an kashe Janar Hassan Ahmed ne lokacin da wasu 'yan bindiga suka far wa motarsa a hanyar Lokoja zuwa Abuja a jiya Alhamis.

    Wata sanarwa da babban hafsan sojin Laftanar janar Faruk Yahaya ya fitar ta bayyana cewa wata tawagar rundunar sojin ta je yi wa matar marigayin ta'aziyya.

    Haka kuma, sanarwar ta ce za a yi wa Janar Faruk jana'iza a makabartar Lungi yau Juma'a da karfe 10 na safe.

  19. Jami'an ba da agaji na ci gaba da neman mutane da suka bata a ambaliyar ruwa a Jamus

    Germany flood

    Asalin hoton, Reuters

    Jami'an ba da agajin gaggawa a yammacin Jamus na ci gaba da neman mutane da dama da suka bata bayan mummunar ambaliyar da ta auku cikin dare a ranar Laraba.

    An samu gawarwakin kusan mutane sittin da suka mutu yayin da gidaje suka ruguje, kana ruwan ya yi awon gaba da motoci da dama.

    Sojojin na ta amfani da jirage masu saukar ungulu domin ceton mutanen da suka makale a rufin gidaje.

    A Belgium, mutane tara sun mutu, ciki har da wata yarinya 'yar shekara goma sha biyar.

    Hakanan ita ma Netherlands ta sha bakar wuya sakamakon ruwan saman da ya janyo ambaliyar.

  20. Shugabannin Afghanistan za su gana da wakilan Taliban

    Manyan shugabannin Afghanistan sun kama hanyar zuwa Doha don ganawa da wakilan Taliban, a kokarin cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

    Rikici tsakanin gwamnatin Afghanistan da Taliban ya kara kamari tun lokacin da sojojin Amurka suka fara ficewa daga kasar.

    Tawagar mai mambobi takwas na karkashin jagorancin shugaban babbar majalisar sasanta rikicin Afghanistan, Dr Abdullah Abdullah, da kuma tsohon shugaban kasar Hamid Karzai.