'Yan tawaye sun 'fille kan sojojin Kamaru' biyu

Wannan shafin na kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da ma sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur and Umar Mikail

  1. 'Yan kasuwa uku sun mutu a rikici da jami'an rundunar saman Najeriya a Legas

    Chief of Air Staff

    Asalin hoton, TWITTER

    Wani rikici tsakanin jami'an rundunar sojin saman Najeriya da ''yan jagaliya' a Legas ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan kasuwa uku a Legas.

    Mutane da yawa sun samu raunuka a rikicin da aka yi a kasuwar Ladipo da ke unguwar Mushin a jihar ta Legas ranar Talata.

    Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya tursasa wa 'yan kasuwa rufe sana'o'insu.

    Kawo yanzu ba a san dalilin aukuwar rikicin ba,amma wasu da suka shaida lamarin sun ce sojoji da 'yan sanda sun mamaye kasuwar kuma sun dakile tashin hankalin.

  2. Ana gudanar da bikin Bastille a Faransa

    France Bastille

    Asalin hoton, Getty Images

    Faransa na gudanar da bikin juyin juya hali na Bastille tare da daukar karin matakan kariya daga annobar korona.

    Za a gudanar da atisayen sojoji nan gaba a Champs-Elysee da ke Paris amma dole ne sai al'ummar kasar sun nuna shaidar da ta tabbatar da an yi musu rigakafin korona kafin su samu shiga wajen.

    An takaita yawan mutanen da za su iya kallon atisayen sojojin zuwa dubu 10 sannan sanya takunkumi ya zama dole.

    A bara, an soke gudanar da atisayen inda aka gudanar da wani kwarya-kwaryan biki.

  3. Biden ya zabi fitaccen mai adawa da Trump a matsayin jakadan Amurka ga Turkiyya

    Shugaba Joe Biden ya zabi wani fitaccen mai adawa da Trump na jam'iyyar Republican , Jeff Flake a matsayin jakadan Amurka ga Turkiyya.

    Sanata Flake daya ne daga cikin yan Republican da dama da suka goyi bayan Joe Biden a yakin neman zama shugaban Amurka a 2020 tare da mutane irinsu Cindy McCain - matar marigayi Sanata John McCain.

    Mista Flake da Mrs McCain sun sha suka daga jam'iyyar Republican a jiharsu ta Arizona saboda nuna adawa ga mista Trump.

    A watan da ya gabata ne gwamnatin Biden ta gabatar da Mrs McCain a matsayin zabi domin samun mukamin jakadar Amurka ga hukumomin Majalaisar Dinkin Duniya kan abinci da noma.

  4. Adadin 'yan Afrika da ke mutuwa yayin kaura zuwa Turai ya rubanya sau biyu

    'Yan ci rani

    Asalin hoton, Getty Images

    Adadin yan ci ranin da suke mutuwa a kokarin tsallaka teku don isa Turai daga Afirka ya ninka fiye da sau biyu kan abin da aka gani tun shekarar da ta gabata.

    Binciken kungiyar kula da yan ci rani IOM ya nuna karuwar mace-macen na da nasaba da rashin bincike da aikin ceto daga kasashen Turai.

    BBC ta gano cewa cikin watanni shidan farkon wannan shekarar, adadin mutanen da ke kokarin tsallakawa ya karu da kashi 58 amma yawan wadanda suka mutu ya ninka fiye da sau biyu.

    Sama da mutum dubu daya da dari ne suka mutu cikin watanni shidan farko na shekarar nan.

    Binciken ya kuma nuna cewa yayin da karin mutane ke kokarin tsallakawa zuwa Turai, wasu da dama kuma ana tilasta musu komawa kasashe irinsu Libya inda suke fuskantar cin zarafi.

  5. Najeriya za ta karbi riga kafin korona miliyan 41 zuwa karshen Satumbar bana

    Hukumomin Najeriya sun ce suna sa ran karbar riga kafin korona miliyan 41 a kasar zuwa karshen Satumba.

    "Mun samu bayanin cewa karkashin tsarin Covax za a aiko mana da alluran cikin watannin nan masu zuwa. Allurai 3,924,000 daga Oxford/AstraZeneca?Moderna zuwa karshen Yuli ko farkon Agusta 2021," a cewar Shugaban hukumar ci gaban kiwon lafiya a matakin farko Faisal Shuaib.

    Ya kuma ce sama da alluran Pfizer da Moderna miliyan shidda za su samu daga tsarin na Covax a Agusta da allurai miliyan 29 daga Johnson and Johnson a watan Satumba.

    Kawo yanzu Najeriya ta yi wa sama da mutum miliyan uku allura tun daga watan Maris.

  6. Budewa

    Barkanku da kasancewa da mu a wannan shafin inda za mu kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwatanta kamar Ghana da Nijar da da Chadi da dai sauransu.

    Da fatan za ku kasance da mu har yamma.