'Yan tawaye sun 'fille kan sojojin Kamaru' biyu

Wannan shafin na kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da ma sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur and Umar Mikail

  1. 'Yan tawaye sun 'fille kan sojojin Kamaru' biyu

    Kamaru

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani hari da 'yan tawaye suka kai ya kashe sojojin Kamaru biyu tare da fille musu kai, a cewar gwamnatin ƙasar.

    An ga gawarwakinsu da safiyar Laraba a Babadjou, wani gari da ke maƙotaka da yankin Arewa maso Yammacin Kamaru - ɗaya daga cikin garuruwa biyu da 'yan tawaye ke son ɓallewa.

    Magajin Garin Babadjou, Gisèle Tsangue, ya ce 'yan tawaye ne suka kai harin a kan wani wurin duba ababen hawa sannan kuma wani ɗan sanda ɗaya ya ɓata.

    Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce an kashe mutum aƙalla 3,500 a yankin rainon Ingila da ke Arewa maso Yamma da kuma Kudu maso Yamma tun da 'yan tawaye suka fara fafutikar a 2016.

    'Yan gwagwarmaya a yankin Ingilishi na zargin ɓangaren Faransanci mafiya rinjaye da tauye su.

  2. Messi zai ci gaba da zama a Barcelona tsawon shekara 5

    Messi

    Asalin hoton, Getty Images

    Lionel Messi ya amince zai ci gaba da zama a Barcelona zuwa karshen kakar 2026 sannan kuma ya rage albashinsa.

    Messi, mai shekara 34 wanda rahotanni ke cewar yana karbar albashin fan miliyan 123, yarjejeniyarsa ta kare a Barcelona ranar 30 ga watan Yunin da ya gabata.

    Kyaftin din na Barca yana hutu biyo bayan lashe Copa America ya yi tare da ƙasarsa Argentina, kuma ba a fayyace kunshin yarjejeniyar ba.

    Ci gaba da taka leda da Messi zai yi yana daga cikin alkawarin da sabon shugaban Barcelona Joan Laporta ya yi.

    An yi ta alaƙanta Messi da komawa Paris St-Germain ko kuma Manchester City, inda ake cewar zai ci gaba da wasa tare da Pep Guardiola.

    Haka nan an yi ta cewa kyaftin din Barcelona zai koma buga gasar kwallon kafar Amurka.

    Messi ne kan gaba a ci wa Barcelona kwallaye da 672 a raga, kuma ya lashe La Liga 10 da Champions League huɗu.

  3. Afirka ta Kudu: Rikicin nan na jawo wa masarautata abin kunya - Sarkin Zulu

    Sarkin Zulu

    Asalin hoton, AFP

    Sarkin Zulu a Afirka ta Kudu ya yi kira da a zauna lafiya tare da kawo ƙarshen tashin hankalin da ya ce yana jawo wa ƙabilarsa mafi girma a ƙasar abin kunya.

    "Hakan na nuni da wata al'umma da ta zubar da mutuncinta - abin da ya fi baƙanta mani ma shi ne, akasarin waɗanda ke aikata wannan laifin 'yan ƙasar Zulu ne," a cewar sarkin.

    "Hakan ya jawo mana babban abin kunya, yayin da ke nuna wa al'u'ummar mahaifina yatsa.

    "Ban taɓa tunanin bayan mutuwar mahaifina zan ga jama'armu na aikata laifi irin haka ba, suna ƙona ƙasa baki ɗaya."

    Tashin hankali da satar kayan jama'a a Afirka ta Kudu sun ɓarke jim kaɗan bayan kotu ta ɗaure tsohon Shugaban Ƙasa Jacob Zuma, wanda ɗan ƙabilar Zulu ne, tsawon wata 15 bisa laifin raina kotun.

    Lamarin ya fi ƙamari a yankunan KwaZulu-Natal da Gauteng.

  4. An rufe ɗakunan kwanan ɗalibai a Jami'ar Legas saboda korona

    Jami'ar Legas

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Jami'ar Legas (UNILAG) ta umarci ɗalibai da su bar ɗakunan kwana na makarantar saboda fargabar yaɗuwar cutar korona.

    Kafar talabijin ta Channels ta ruwaito cewa an samu ruɗani a farfajiyar makarantar ranar Talata bayan wasu ɗalibai masu yawa sun kamu da cutar, abin da ya sa majalisar zatrtarwar jami'ar ta yi taron gaggawa ranar Laraba.

    Wata sanarwa daga hukumomin jami'ar ta ce ana kula da waɗanda suka harbu da cutar sannan kuma ana bin sawun mutanen da suka yi mu'amala da su.

    "Halin da ake ciki yana da ban-tsoro musamman idan aka duba yadda ɗalibai ke ƙin bin dokokin kariya daga cutar," a cewar sanarwar.

    "Domin guje wa yaɗuwar cutar a jami'a, majalisar zartarwa yayin wani taron gaggawa a ranar Laraba ta umarci dukkan ɗalibai da su fice daga ɗakunan kwana zuwa 12:00 na daren Alhamis har sai abin da hali ya yi."

    Sai dai ta ce za a ci gaba da gudanar da karatu ta intanet har zuwa ƙarshen zangon karatun da ake ciki.

  5. Matar da ta cillo 'yarta daga benen da ya kama da wuta

    Bayanan bidiyo, Matar da ta cillo ɗanta daga saman benen da ya kama da wuta

    Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

    Wata mata a birnin Durban na Afirka Ta Kudu ta cillo 'yarta daga saman bene bayan an cinna wa benen wuta yayin zanga-zanga ranar Talata. Ana zargin masu zanga-zanga da wawason kayan shaguna ne suka kunna wa benen wuta. Mutane da dama ne suka mutu a kasar, yayin da aka kama daruruwan masu zanga-zanga, bayan daurin da aka yi wa tsohon shugaban kasar Jacob Zuma makon jiya.

  6. Yaya za a kawar da wariyar launin fata a kwallon kafa?

    Bayanan bidiyo, Euro 2020: Yaya za a kawar da wariyar launin fata a kwallon kafa?

    Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

    An gama Euro2020...amma akwai wani batu babba da za a dade ba a manta da shi ba game da gasar.

    Ina maganar nuna wariyar launin fatar da aka yi wa ‘yan wasan Ingila uku bayan da suka barar da fanerati.

    Galibin kalaman nuna wariyar da aka yi wa ‘yan wasan uku bakaken fata an yi ne kafafen sada zumunta.

    ‘Yan wasa bakaken fata da ke wasa a nahiyar Turai suna yawan yin korafi kan yadda ake nuna musu wariya.

    Sai dai akwai wata babbar tambaya a nan: Me ya sa irin wannan batu ba ya tashi idan ‘yan wasan suka yi nasara?

    Sai sanda aka yi rashin nasara, kamar yadda Ingila ta yi a wasan karshe a Euro2020.

    Mene ne kuke ganin za a yi domin tsayar da wannan matsalar?

  7. Tarayyar Turai ta sabunta matakan yaƙi da fitar da gurɓatacciyar iska

    Shugaban hukumar kula da yanayi ta Tarrayar Turai, Frans Timmermans, ya sanar da sabbin tsare-tsaren rage yawan gurɓataciiyar iskar da ake fitarwa wadanda ya ce za su bayar da damar yaƙi da sauyin yanayi.

    Tarrayar Turai na da aniyar ganin cewa ta kawo ƙarshen sayar da sabbin motoci masu amfani da man fetur nan da shekarar 2035.

    Haka kuma ya sanar cewa a karon farko za ta sanya haraji a kan jiragen ruwa masu jigilar kaya da kuma man jirgin sama kuma za ta gabatar da haraji na musaman a kan sinadarin carbon da ake amfani da shi a cikin siminti da karafa.

    An tsara matakan ne domin taimaka wa kungiyar cimma burinta na rage fitar da gurɓattaciyyar iska nan da shekarar 2050.

  8. 'Yan ESN 'sun kashe' sojojin Najeriya biyu

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Dakarun sojan Najeriya biyu sun rasa rayukansu a lokacin da suke fafatawa da mambobin ƙungiyar Eastern Security Network (ESN) a Jihar Enugu ranar Talata, a cewar rundunar.

    Ƙungiyar ESN ɓangaren soja ne na ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) mai fafutikar kafa ƙasar Biafra a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

    Wata sanarwa daga mai magana da yawun rundunar ranar Laraba, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ta ce lamarin ya faru ne a Adani da ke Ƙaramar Hukumar Uzo-Uwani a lokacin da dakarun ke ƙoƙarin daƙile wani harin 'yan ESN kan wani wurin duba ababen hawa na Iggah/Asaba.

    Ya ƙara da cewa sojoji na bin sawun miyagun da suka aikata kisan.

    Hukumomi a Najeriya na zargin 'yan bindigar IPOB da kashe jami'an tsaro da dama a yankin kudu maso gabas da kuma ƙona ofisoshinsu.

  9. Fafaroma ya koma gida bayan an yi masa tiyata a asibiti

    Fafaroma Francis

    Asalin hoton, Reuters

    Fafaroma Francis ya koma Fadar Vatican ranar Laraba bayan shafe kwana 11 a asibiti sakamakon tiyatar da aka yi masa.

    Dattijon mai shekara 84 ya bar Asibitin Gemelli University a cikin mota mai duhun gilashi, a cewar mai ɗaukar hoto na AFP.

    An kai shi asbitin ne bayan ya yi fama da wata cuta da ta shafi hanjin da ya haɗe da makasayarsa.

    Tun farko Vatican ta ce zai kasance a asibitin ne tsawon mako ɗaya. Fafaroman ya jagoranci addu'ar Angelus daga tagar ɗakin asibitin.

  10. 'Yan sandan Najeriya sun kama ɗalibai 16 da zargin shiga ƙungiyar asiri

    'Yan sandan Najeriya

    Asalin hoton, AFP

    Rundunar 'yan sandan Jihar Neja a Najeriya ta ce ta kama ɗalibai 16 na Jami'ar Ibrahim Babangida da take zargi da shiga ƙungiyar asiri wato cultism.

    Kakakin 'yan sanda DSP Wasiu Abiodun ne ya bayyana hakan ranar Talata cikin wata sanarwa a Minna, babban birnin jihar.

    "Ranar 7 ga watan Yuli da misalin ƙarfe 9:00 na dare, bayan samun rahoton sirri 'yan sandan Lapai suka kama waɗanda ake zargin," a cewarsa cikin rahoton NAN.

    "An kama su ne da zargin zama mambobin ƙungiyar asiri ta Black Axe a wurin saukar baƙi na Gwaranyo da ke yankin Lapai a lokacin da suke bikin shekara a wani ɗaki da ɗaya daga cikinsu ya kama."

    Sanarwar ta ce daga cikin abubuwan da aka ƙwace a hannunsu sun haɗa da gatari da wandon kakin soja da hular soja da tukunya cike da busassun ganye da ake zargin wiwi ce.

  11. Mazauna Durban sun yi dogayen layukan sayayya bayan znga-zanga a Afrika ta Kudu

    An yi dogayen layuka a wajen shagunan da ke garin Durban mai tashar jirgin ruwa a kasar Afrika ta kudu bayan kwanakin da aka shafe ana rikici sakamakon daurin da aka yi wa tsohon shugaban kasa Jacob Zuma a gidan yari.

    Ma’aikatan kashe gobara tare da taimakon wasu mazauna yankin da suka zo da tsintsiya na tsabtace wuraren da aka zubar da shara.

    Masu zanga zanga sun kwashi ganima tare da lalata shaguna, abin da ya janyo karanci kayayakin masarufi.

    Mutum sama da saba'in sun rasa rayukansu kuma an cafke sama da dubu daya tun bayan aka fara zanga zangar.

  12. Mutum-mutumai za su rika bai wa mahajjata ruwan Zamzam

    Hukumomin Saudiyya sun ce za su tura wasu mutum-mutumai cikin masallacin Harami domin su rika raba ruwan zam-zam ga maniyyata aikin Hajjin bana.

    Wata sanarwa da shafin Haramain da ke kula da masallacin Haramin ya wallafa a Tuwita ta ce manufar yin hakan ita ce a kauce wa kamuwa da cutar korona.

    "Hukumar Haramain tana shirin tura mutum-mutumai da zummar gogewa da kuma raba ruwan Zamzam ga masu aikin ibada a masallacin Haramin, lamarin da ya yi daidai da shirin shugabanni na karbar mahajjata na shekarar 2021," in ji sanarwar.

    Da ma dai hukumomin kasar sun bayyana cewa mutum 60,000 ne za su gudanar da aikin hajjin bana, kuma za su kasance mazauna kasar ta Saudiyya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  13. Taliban ta kafa tutarta a kan iyakar Afghanistan da Pakistan

    Taliban

    Asalin hoton, Twitter

    Rahotanni na cewa kungiyar Taliban ta kafa tutarta a wata iyaka mai muhimmanci tsakanin Pakistan da Afghanistan, kuma ta yi ikirarin cewa yanzu ita ce da iko da yankin.

    Hotunan bidiyo da ake ta yadawa a shafukan sada zumunta sun nuna farar tutar a yankin Spin Boldak kusa da Kandahar.

    Jami'an Afghanistan sun musanta kwace ikon yankin, duk da cewa hotuna a shafukan sada zumunta sun nuna 'yan bindigar suna hira da jami'an tsaron Pakistan.

    BBC ta samu bayanai da ke cewa Taliban ta kwace ikon iyakar ne ba tare da turjiya daga Pakistan ba.

    A makonnin baya-bayan nan, 'yan bindigar sun yi ta yunkurin kai hare-hare a fadin kasar inda suka kwace wasu iyakoki daga dakarun Afghanistan ciki har da iyaka da Iran da Tajikistan da Turkmenistan.

    Wannan na zuwa ne a lokacin da Amurka ke janye dakarunta daga Afghanistan kafin wa'adin Satumba 11 da Shugaba Biden ya sa.

    Kungiyar Taliban, mai tsattsauran ra'ayin addinin Islama da Amurka ta dakile ayyukanta, ta kwace ikon wasu tituna masu muhimmanci yayin da suke kokarin datse hanyoyin manyan birane.

  14. Minti Daya Da BBC Na Rana

    Bayanan sautiMInti Daya Da BBC Na Rana14-07-2021
  15. Sojojin Najeriya biyu sun mutu a musayar wuta da 'yan IPOB a Enugu

    'Yan bindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Najeriya da aka tura don hana ayyukan 'yan bindiga a unguwar Adani a karamar hukumar Uzo-Uwani ta jihar Enugu sun dakile wani hari da mayakan kungiyar a-ware ta IPOB suka kai da bindigogi kan shingen sojijin a jiya Talata.

    Wata sanarwa da Burgediya Janar Oyema Nwachukwu, mai magana da yawun rundunar sojin Najeriyar ya fitar ta ce an kashe sojoji biyu a yayin musayar wuta da 'yan bindigar.

    Haka kuma, ya bayyana cewa ana ci gaba da kokarin kamo maharan.

    Ya bukaci al'ummar yankin su taimaka wa jami'an tsaro wajen zama masu bin doka da samar da bayanai kan duk wani bata-gari.

  16. Majalisar Kano ta dage zamanta da Muhuyi Magaji

    Muhuyi Magaji Rimningado

    Asalin hoton, Facebook/Muhuyi_Magaji_Rimingado

    Majalisar jihar Kano ta dage zaman da ta shirya yi na Muhuyi Magaji Rimin Gado ya bayyana gabanta har sai Baba ta gani.

    Wannan na zuwa ne bayan rashin bayyanar Muhuyin a gaban kwamitin a yau kamar yadda aka bukata.

    A cewar lauyansa, bai sami amsa gayyatar ba saboda rashin lafiya da yake fama da ita, wanda yake ganin likita a wani asibiti a Abuja.

    Sannan yace kawo yanzu ba a bai wa muhuyi jeirin tuhume-tuhumen da ake yi masa ba.

  17. Wani abu ya fashe a birnin Riyadh na Saudiyya

    Saudiyya ta ce wani abu ya fashe bisa kuskure a wani wurin ajiye makamai a Riyadh babban birnin kasar.

    A wani rahoto da aka wallafa a shafin Al Arabiya TV an ambato mai magana da Ma'aikatar Tsaron Kasar, Turki al-Maliki ya sanar da cewa lamarin ya faru ne a wajen birnin Kharj.

    Sai dai babu wanda ya samu rauni a fashewar wadda ake bincike a kanta yanzu.

    Lamarin na faruwa ne a dai-dai lokacin da 'yan tawayen Houthi a Yemen mai makwabtaka suka karfafa hare-harensu na makamai masu linzami da jirgi marar matuki a 'yan kwanakin nan.

  18. Majalisar wakilan Najeriya ta gargadi gwamnati kan bai wa 'yan kwana-kwana bindiga

    Federal Fire Service

    Asalin hoton, Federal Fire Service

    Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci gwamnatin Najeriya ta yi watsi da matakin bai wa jami'an kashe wuta na kasar bindiga.

    Gwamnatin ta sanar da shirinta na mika wa majalisar dokoki kudirin yi wa dokar 'yan kwana-kwana garambawul ta hanyar bai wa jami'an damar rike makamai don kare kansu daga hare-haren da ake kai masu a yayin gudanar da ayyukansu.

    Sai dai majalisar ta bukaci gwamnatin ta dakatar da matakin.

    Honarabul Thomas Ereyitomi wanda ya gabatar da bukatar a gaban majalisar ya bayyana cewa hukumar 'yan kwana-kwana hukuma ce ta farar hula ba ta tsaro ba.

    Sannan ya ce hankali ma ba zai dauka ba idan aka ba su damar rike bindiga saboda ba sa bukatarta.

  19. Kungiyar kasashen Afrika ta yi Alla-wadai da rikicin Afrika ta Kudu

    Tashi hankali a South Africa

    Asalin hoton, EPA

    Hukumar kasashen Afrika ta yi tir da rikicin Afrika ta Kudu da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 72.

    Zanga-zanga ta barke ne dalilin tsare tsohon Shugaba Jacob Zuma inda aka shiga fasa shaguna da lalata gine-gine a lardin.

    "Shugaban Hukumar, Moussa Faki Mahamat ya yi kakkausar suka kan rikicin da ya barne da ya yi sanadiyyar mutuwar farar hula da lalata dukiyoyin jama'a,: a cewar wata sanarwar hukumar.

    An aike da sojoji don dakile rikicin sannan an kama dubban masu zanga-zanga.

  20. EFCC ta kama mutum 30 da ake zargi da aikata zamba ta intanet

    A kalla mutum 30 ne jami'an hukumar EFCC suka kama a yayin wani samame a Otel din Parktonian a unguwar Lekki ta jihar Legas.

    A lokacin samamen na ranar Talata, jami'an EFCC sun samu shiga dakunan wadanda ake zargin ne ta hanyar kwace makullan dakunansu daga jami'an otel din da karfin tsiya.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa EFCC ta bayyana cewa an kama mutanen ne bisa zargin aikata zamba ta intanet.

    EFCC ta ce ta samu bayanan siri da suka tabbatar mata da cewa otel din ya zama matattarar masu aikata zamba da yaudara ta intanet, shi ya sa ta aika jami'anta.