Yin rigakafi sau ɗaya ba ya ba da kariya daga nau'in Delta na korona

Wasu sabbin bincike biyu sun tabbatar da binciken farko da ke cewa yi wa mutum allurar rigakafin korona na farko da ake yi sau biyu ba ta bayar da kariya sosai daga kamuwa da na'uin cutar na Delta mai saurin yaɗuwa.
Binciken wanda aka wallafa a fitattun mujallun da ake kira Nature da New England sun gano cewa idan aka yi allurar sau biyu tana bayar da kariya mai kyau.
Masana kimiyya sun gano cewa sauyawar da sabon nau'in cutar korona ke yi tana ba shi damar kai wa ƙwayoyin garkuwar jiki hari da rigakafin farko ke bayarwa.
Nau'in Delta ya yi ƙamari a ƙasashen Amurka da Bahrain da Birtaniya da Indonesia kuma yana cigaba da yaɗuwa a wasu kasashen.
A ranar Alhamis ne Najeriya ta ce nau'in cutar ya ɓulla a ƙasar.
