Ƴan bindiga sun ce a ba su kuɗi su ciyar da ɗaliban da suka sace a Kaduna

Wannan shafin na kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Halima Umar Saleh and Awwal Ahmad Janyau

  1. Yankin arewa maso gabashin Najeriya zai kafa kamfanin sufurin jirgin sama

    Gwamnonin yankin arewa maso gabashin Najeriya

    Asalin hoton, Taraba State Government

    Gwamnonin yankin arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana cewa suna yunƙurin kafa kamfanin zirga-zirgar jiragen sama domin samar wa 'yan yankin sauƙin tafiye-tafiye.

    Gwamnonin sun cimma matsaya ne yayin wani taro da suka gudanar a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba ranar Talata.

    Mahalarta taron su ne gwamnonin Borno da Yobe da Gombe da Taraba da Bauchi da Adamawa, waɗanda su ne jihohin yankin.

    "Mun tattauna game da yadda sha'anin sufuri yake a yankin nan kuma mun yanke shawarar kafa kamfanin jirgin sama ta yadda mutanenmu za su samu saukin zirga-zirga," a cewar Gwamnan Gombe Muhammad Inunwa yayin hira da BBC Hausa.

    Kazalika gwamnonin sun tattauna game da matsalolin tsaro da na wutar lantarki.

    Saurari cikakkiyar hirar idan kuka danna hoton ƙasa:

    Bayanan sautiYankin arewa maso gabashin Najeriya zai kafa kamfanin sufurin jirgin sama
  2. Labarai cikin minti ɗaya

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari Minti Daya Da BBC Na Safe 07/07/2021
  3. Hukumomi a Holand sun yi Allah-wadai da harbin ɗan jarida

    Firaministan Holand Mark Rutta, ya yi Allah-wadai da harbin wani fitaccen ɗan jarida mai bincike Peter Er-defrish.

    Shugaban ya bayyana hakan a matsayin hari ga 'yancin' 'yan jarida da zamantakewar Holland.

    Maharin da ya harbi Mista Peter ya same shi ne a ka, jim kaɗan bayan ya bar wani gidan talabijin a tsakiyar Amsterdam.

    Yanzu haka yana kwance a asibiti rai kwakwai mutu kwakwai. ‘Yan sanda sun ce an tsare mutane uku saboda zarginsu da hannu a harin.

  4. Ƙarin mutum 91 sun kamu da korona a Najeriya

    Ƙarin mutum 91 ne suka kamu da cutar korona ranar Laraba a Najeriya, a cewar hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a ƙasar.

    Mutanen sun fito ne daga jiha huɗu. Sai dai babu wanda ya rasa ransa sakamakon cutar.

    Jihohin su ne: Legas - 66, Kwara-12, Rivers-4, Kaduna-3, Oyo-3, Ekiti-1, FCT-1, Plateau-1

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 168,000 aka tabbatar sun harbu da cutar korona a Najeriya. Haka nan, cutar ta yi ajalin mutum 2,122, sai kuma 164,405 da aka sallama bayan sun warke.

  5. Barka da safiya

    Masu bibiyarmu a wannan shafi da fatan mun wayi gari lafiya.

    Umar Mikail ne ke fatan kasancewa da ku a wannan yini na Laraba domin kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya.