An gano gawar mutum 60 da jirgi ya kife da su a Jihar Kebbi

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. Macron ya isa Rwanda domin ziyara

    Shugaban Faransa Emmanuel Macros ya isa Rwanda a kokarin sake gida alakar diflomasiyya tsakaninsa da Kigali.

    A taron da aka yi a Paris a makon jiya, Macron ya shaida wa manema labarai cewa, ya yarda da matsayar shugaban Rwanda na cewa a sake "gina alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

    Macros zai gabatar da bayani a dandalin tarihi da ke Kigali amma babu tabbas ko zai nemi ahuwa a hukumance.

    Minisratan harkokin wajen Rwanda ne ya wallafa hotunan zuwan shugaba Macron.

    Rwanda Foreign Affairs Ministry

    Asalin hoton, Rwanda Foreign Affairs Ministry

    Rwanda Foreign Affairs Ministry

    Asalin hoton, Rwanda Foreign Affairs Ministry

    Rwanda Foreign Affairs Ministry

    Asalin hoton, Rwanda Foreign Affairs Ministry

  2. Farashin kudin biredi da biskit ya karu da kashi 30 a Najeriya

    a

    Asalin hoton, Google

    Kungiyar masu biredi ta Najeriya ta umarci duka mambobinta da su kara farashin kayansu da kashi 30 cikin 100 saboda karuwar farashin sinadaren hada biredi da dangoginsa.

    Umarnin na zuwa ne bayan da aka cimma matsayar a karshen tattaunawar majalisar zartarwar kungiyar da aka yi a Abuja.

    Da yake bayani kan dalilan kara farashin shugaban kungiyar na kasa Mansur Umar, ya ce karuwar farashin Siga da bota da filawa duka na cikin abubuwan da suka janyo daukar wannan matakin nasu.

    Lokacin da yake yaba wa gwamnatin tarayya kan daidaita shirinta na yin filawa da makani, shugaban ya ce farashin filawar da suke siya a kasa da naira miliyan shida da a duk mota guda yanzu suna sayanta kan naiara miliyan 9.

  3. Macron yana ziyarar sauya daidaita alakar diflomasiyya a Rwanda

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron na ziyarar daiidaita alkar diflomasiyya a Rwanda, bayan da alakar ta yi tsami kan rawar da ake zargin Faransa da takawa yayin kisan kare dangi da aka yi a kasar a 1994.

    Ziyarar ta biyo bayan sakin wani rahoto ne da aka saki a watan Maris, wanda ya ce gwamnatin kasashen rainon Faransa kan rashin mayar da hankali kan kisan.

    Rahoton wanda aka yi maraba da shi a Kigali, ya zargi Faransa da taka rawar kai tsaye a cikin yanka 'yan kabilar Tutsi sama da 800,000 da Hutsi suka yi.

    An ruwaito Shugaba Paul Kagame a baya-bayan nan yana cewa Rwanda ba zata manta da abin da ya faru ba amma za ta iya yi wa Faransa ahuwa kan rawar da ta taka.

    Ana sa ran Macron zai gabatar da bayani a dandalin tunawa da wannan kisan kare dangi da ke Kigali.

    Kuma ana sa ran zai nada wakilin Fanarsa a Kigali a karon farko cikin shekara shida.

  4. Labarai da dumi-dumi, Sojojin da suka aiwatar da juyin mulki a Mali sun saki Shugaban kasar da Firaiministansa

    e

    Asalin hoton, Reuters

    Shugabanin da suka yi juyin mulki a Mali sun saki shugaban kasar na rikon kwarya Bah Ndaw da Firaiministansa Moctar Ouane.

    An sake su ne da misalin karfe 01:00 na daren ranar Alhamis, kamar yadda wakilin BBC Ebrin Brou ya ruwaito.

    Mutanen biyu an tsare su ne a sansanin sojin kasar tun ranar Litinin.

    "Mun ba da gaskiya kan wannan duniyar ta mu," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP aka rawaito wani jami'in soji na fada.

    Shugaban kasar da Firaiministansa an tilasta musu su yi murabus daga matsayinsu bayan kama su - wanda wannan ne juyun mulki na biyu da aka yi a kasar cikin wata tara.

    AFP

    Asalin hoton, AFP

  5. Korona ta kama Shugaban kasar Namibia

    G

    Asalin hoton, Getty Images

    Cutar korona ta kama shugaban kasar Namibia Hage Geingob.

    An kuma tabbatar da cewa cutar ta kama mai dakin shugaban Monica Geingos wadanda a yanzu su duka suka killace kansu.

    "Duka su biyu suna cikin yanayi mai kyau" kamar yadda aka wallafa a shafin shugaban kasar na Twitter.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Akwai mutum 53,432 da aka tabbatar sun kamu da cutar ciki har da wadanda ta kashe 779, kamar yadda bayanan hukumar lafiya ta Duniya suka bayyana.

    An samar da rigakafin cutar 67,984 a fadin kasar baki daya ya zuwa yanzu.

  6. Shugabannin kasashen Kudancin Afirka na taro kan masu ikirarin jihadi a Mozambique

    A

    Asalin hoton, AFP

    Shugabannin kasashen Kudancin Afirka za su gana a yau domin tattauna shirye-shiryen magance rikicin masu ikirarin jihadi da ke ci gaba da karuwa a arewacin Mozambique.

    Kungiyar raya kasashen Kudancin Afirka ta nuna damuwa kan yadda rikicin masu ikirarin Jihadi ka iya bazuwa a dukkanin yankin matukar aka gaza daukar mataki.

    A watan Maris ne masu da'awar Jihadin suka kwace iko da garin Palma da ke arewacin Mozambique inda suka rufe wata babbar masana'antar iskar gas ta dala biliyan 20.

    Yan Mozambique kimanin dubu dari bakwai ne suka daidaita sanadin tashin hankalin a cikin yan shekarun nan.

  7. Budewa

    Barkanmu da safiya da fatan an tashi lafiya.

    Buhari Muhammad Fagge ke fatan kasancewa da ku a wannan yini domin kawo muku labarai da rahotanni daga ko ina cikin sassan duniya.