Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Yan bindiga sun kashe Bashar Namaska ɗan sarkin Kontagora

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da sauran ƙasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. Tattaunawata da Sakataren Rasha Sergei Lavrov ta yi armashi - Antony Blinken

    Sakataren harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya ce tattaunawarsa ta farko da takwaransa na Amurka Antony Blinken, ta yi armashi.

    Sakatarorin biyu sun shafe kusan sa'o'i biyu su na tattaunawa a Iceland, inda suke halartar taron kasashen yankin.

    Ma'aikatar cikin gidan Amurka ta ce sun yi batutuwan da suka shafi kasuwa, Mr Blinkin kuma ya nuna damuwa kan kutsen internet da ake yi, da batun Ukraine da Syria da kuma jagoran hamayya Alexei Navalny da Rashar ke tsare da shi.

    Sannan Mr Blinken ya nanata cewa ya kamata kasashen biyu su hada karfi da karfe domin yin aiki tare, ya ce hakan zai kawo ci gaba mai dorewa a duniya.

  2. Mahaifin yarinyar da gwamnatin Kaduna ta ce an cire wa na'ura ya musanta batun

    Mahaifan jaririyar da Gwamna El Rufa'i ya ce an cire na'urar taimaka wa nunfashi daga fuskarsa a asibitin Barau Dikko don ma'aikatan su shiga zanga-zanga a Kadun sun karyata wannan ikirari.

    Daya daga cikin iyayen ya shaida wa gidan talabijin na NTA cewa yanayin yarinyarsu a lokacin da ake shirin fara yajin aiki ba shi da matsala, kuma babu na'urar taimaka wa nunfashi a fuskarta ma.

    "A lokacin babu na'urar taimakwa nun fashi a fuskarta ma, yanayinta ya yi matukar kyau. Mu ne muka dage cewa sai mun dauki yarinyarmu zuwa wani asibitin na daban," a cewar mahaifin jaririyar.

    A ranar Talata ne gwamnatin El Rufa'i ta ce za ta mika wa ma'aikatar shari'a sunayen majinyatan lafiya uku da aka ce su ne suka cirewa yarinyar na'urar.

    A ranar Litinin ne kungiyar kwadago a jihar ta fara yajin aikin gargadi kan korar na'akatan gwamnati da aka yi.

    Ma'aikatan banki da na sufuri da 'yan kasuwa da gidajen mai da dai sauransu suka dakatar da ayyukansu suka shiga zanga-zangar.

    Sai dai a jiya Laraba ne kungiyar kwadagon ta ba da sanarwar janye yajin aikin na wani lokaci, kafin sakamakon tattaunawar da za a yi tsakaninsu da gwamnatin ta Kaduna.

  3. 'Yan bindiga sun kashe mutum takwas a wani hari da suka kai Kaduna

    Wasu 'yan bindiga sun cinna wa wani gini coci wuta a unguwar Gaida kusa da Kurmin Kaso da ke Karamar Hukumar Chikun da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya.

    Akalla mutum takwas ne suka rasa rayukansu a harin yayin da aka kona gidaje da dama a yankin.

    Samuel Aruwan wanda shi ne kwamishinan cikin gida da tsaro na jihar, ya tabbatar da faruwar harin tare da bayyana sunayen mutane da suka mutu.

    Aruwan ya ce gwamnan jihar El Rufa'i yayi Allah-wadai da harin da aka kai a wurin bautar, ya kuma umarci hukumar ba da agajin gaggauwa ta jihar da ta gudanar da bincike cikin gaggawa kan asarar da aka yi.

    Aruwan ya ce sojojin ruwan Najeriya sun kashe "yan bindiga uku" tare da kama wasu abokansu biyu bayan harin da aka kai Wakwondam kusa da Kasso duka a cikin karamar hukumar Chikun.

  4. Allah ya yi wa Sarkin Funakaye rasuwa

    Gwamnan Jihar Gombe da ke arewacin Najeriya Inuwa Yahaya ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan Sarkin Funakaye Alhaji Muhammadu Kwairanga Abubakar II wanda ya mutu a safiyar yau a Bajoga.

    Mai martaba sarkin Funakaye ya rasu yana da shekara 68 a duniya.

    Cikin wata sanarwa da Gwamnan ya fitar ya bayyana mutuwar sarkin a matsayin gagarumin rashi ba kawai ga iyalansa ba har ma ga mutanen jihar da kuma Najeriya baki daya.

    Ya bayyana sarkin a matsayin jajurtacce mai kuma nuna sadaukarwa ga mutanensa, da jiharsa da ma kasa baki daya, wanda ba za a taba mantawa da bajintarsa ba da kuma kimar da yake da ita a idanun mutanensa.

    An dai nada marigayi Sarki Muhammadu Kwairanga II a matsayinsa ne a watan Mayun 2010.

    Sanarwar ta ce za a yi jana'izar marigayin a yau Alhamis da misalin karfe 2 na rana a fadar Sarkin Bajoga da ke Karamar hukumar Funakaye a jihar ta Gombe.

  5. Za a biya matan da aka yi wa cikon mama diyya a Faransa

    Ana sa ran kotun daukaka kara a birnin Pari na Faransa za ta yanke hukuncin ko za a ba da diyya ga mata 2500 da da aka yi wa ciko a Nono shekaru 10 da suka gabata.

    Wani kamfanin Faransa ne ke samar da sinadarin Slikon da ake cikon Nonon da shi ba bisa ka'ida ba, sai dai an gurfanar da kamfanin Jamus da ya bai kamfanin shaidar rashin ingancin sinadarin a gaban kuliya.

    Tun a shekarar 2010 aka rufe kamfanin na Faransa tare da tsare mamallakinsa a gidan kaso, bayan gano rashin ingancin sinadarin da sam bai dace da jikin dan adam ba, wanda ka iya janyo mummunar illa ga lafiyar matan da akai wa aiki da shi.

  6. Abin da ya sa ƙungiyar ƙwadago ɗage yajin aikin Kaduna

    A yau Alhamis ne babbar ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC za ta gudanar da wani taro da ayarin gwamnatin ƙasar bayan jingine yajin aikin gargaɗi na tsawon kwana biyar da ta fara a jihar Kaduna.

    Ƙungiyoyin ƙwadagon Nijeriya sun tsunduma yajin da kuma zanga-zangar da ta durƙusar da harkoki a Kaduna ne don nuna adawa da gwamnatin Nasir El-Rufa'i a kan sallamar ɗumbin ma'aikata daga aiki.

    El-Rufa'i dai ya sha nanata cewa ba zai sauya matsayinsa a kan ma'aikatan da ya kora.

    To, ko me ya sa ƙungiyar ƙwadago ɗage wannan yajin aiki?

    Tambayar ke nan da na yi wa Comrade Kabir Nasir, sakataren tsare-tsare na hadaddiyar kungiyar kwadago wato NLC ta kasa.

  7. Mutum miliyan 55 ne ke gudun hijira a fadin duniya - MDD

    Sakamakon wani sabon bincike da aka gudanar, ya nuna sama da mutum miliyan 55 a fadin duniya sun tsere daga muhallansu, inda suke zaman gudun hijira a cikin kasashensu.

    A rahoton cibiyar da ke sanya ido kan wadanda suka rasa muhallansu na shekara-shekara, cibiyar ta ce an samu matukar karuwa kan hijirar dole da mutane ke yi.

    Wakiliyar BBC ta ce sabon tashin hankalin da ake yi a kasashe Habasha da Muzambique, ya tilastawa dubban mutane tserewa daga muhallansu, ya yin da shekarun da aka dauka ana yaki a kasashen Syria da Afghanistan da Yemen da sauransu na ci gaba da tilastawa 'yan kasashen zama 'yan gudun hijirar dole, sai kuma wadanda ibtila'in ambaliyar ruwa ko fari ke tilastawa yin hijirar.

    Cikin shekaru 10 an samu karuwa fiye da kima, tare da gargadin idan ba a dauki mataki na rikice-rikicen siyasa da na addini da kabilanci, da sauyin yanayi ba, yanayin zai kara munana.

  8. Isra'ila ta kare shafe dare tana luguden wuta a Gaza

    An sake shafe dare Isra'ila na kai hare-hare ta sama a zirin Gaza, duk kuwa da rahotannin da ke cewa bangarorin biyu sun amince da dakatar da bude wuta.

    Wakilin BBC a Gaza ya ce an kai samame a wuraren ababen more rayuwa na Hamas dari da ke arewacin Gaza, sai dai su ma mayakan Falasdinwa sun maida martani da harba rokoki Isra'ilar.

    Wakilin BBC ya ce lamarin na kara zafi musamman sa'o'i 2 da suka gabata a arewacin Gaza, mazauna yankin da jami'an tsaro sun ce sojojin Isra'ila sun harba sama da makamai masu linzami 20.

    Ya yin da kasashen duniya ke ci gaba da matsawa bangarorin biyu lambar dakatar da hare-haren, wani babban jami'in kungiyar Hamas ya shaidawa gidan talabijin din Labanun cewa ya na fatan dakatar da budewa wutar cikin kwanaki biyu masu zuwa.

    Sai dai a jiya Laraba, firai ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya ce sojoji za su ci gaba da kai hare-hare babu kakkautawa, duk kuwa da kiran da shugaban Amurka Joe Biden ya yi na dakatar da hakan nan take.

  9. Budewa

    Barkanmu da safiya da fatan an tashi kalau.

    Buhari Fagge ne zai kasance da ku a wannan yini domin kawo muku labarai da rahotanni da ke faruwa kai tstsaye a fadin duniya.