'Yan bindiga sun kashe Bashar Namaska ɗan sarkin Kontagora

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da sauran ƙasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. Ƙarshen rahotannin kenan

    Mun zo ƙarshen labarai kai-tsaye a wannan shafi. Mu haɗu gobe domin samun sabbin labarai.

    Kafin lokacin, Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.

    Kuna iya duba ƙasa domin karanta labaran da muka kawo muku a tsawon yinin yau Alhamis.

  2. Yarjejeniyar tsagaita wuta nasara ce ga Falasɗinawa - Hamas

    Sanarwar yarjejeniyar tsagaita wuta da aka sanar a rikicin Isra'ila da Falasɗinawa na matsayin "nasara ga Falasɗinawa" kuma tana nufin cinye Firaminista Benjamin Netanyahu da yaƙi, a cewar wani jami'in ƙungiyar Hamas.

    Ali Barakeh ya faɗa wa kamfanin labarai na Associated Press cewa mayaƙan Hamas za su ci gaba da kasancewa cikin shiri har sai masu shiga tsakani sun fayyace sauran bayanai game da yarjejeniyar.

    Ƙasashen Masar da Qatar da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya ne suka suka shiga suka fita wajen cimma yarjejeniyar tsakanin Isra'ila da Hamas, wadda ke iko da birnin Gaza.

  3. Isra'ila da Falasɗinawa na ci gaba da fafatawa kafin tsagaita wuta ta fara aiki

    Yayin da ake jiran yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki tsakanin Isra'ila da Falasdinawa, sojojin Isra'ilar sun ce an kunna lasifikar da ke ankarar da mutane cewa an harbo makamin roka a yammacin ƙasar daga Gaza.

    A gefe guda kuma, wata kafar yaɗa labarai a Falasɗinu na cewa Israila ta kai sabbin hare-hare a yankin.

    Ya zuwa yanzu, mutum 232 hare-haren na Isra'ila suka kashe a birnin Gaza, yayin da makaman roka da Hamas ke harbawa suka kashe mutum 12 a Isra'ila.

  4. Labarai da dumi-dumi, Isra'ila ta amince da tsagaita wuta a birnin Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Majalisar zartarwar Isra'ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a rikicinta da Falasɗinawa.

    Sai dai ta ce har yanzu ba a tabbatar da lokacin da za ta fara aiki ba.

    Wata sanawa daga fadar gwamnati ta ce yarjejeniyar wadda ƙasar Masar ta shiga tsakani, za ta kasance "maras iyaka kuma cikin mutuntawa".

    Tun farko wani jami'in ƙungiyar Hamas ya ce za ta fara aiki daga ƙarfe 2:00 na dare agogon ƙasar - 12:00 na dare agogon Najeriya da Nijar.

  5. Isra'ila za ta yarda da yarjejeniyar tsagaita wuta

    Mai shirya shiri na BBC a birnin Gaza, Rushdi Abualouf, ya ruwaito cewa Isra'ila za ta yarda da shirin tsagaita wuta bayan wata ganawa da majalisar tsaron ƙasar ta yi a yammacin yau Alhamis.

    Ya bayyana cewa wasu majiyoyi da ke da alaƙa da yunƙurin sun shaida wa BBC cewa Isra'ila ta faɗa wa Masar matsayinta.

    Masar ce kan gaba a yunƙurin ƙulla yarjejeniyar tsagaita wutar tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hamas da ke Falasɗinu, yayin da ɓangarorin biyu ba sa magana da juna gaba da gaba.

    Ɓangarorin biyu sun shafe kwana 11 suna kai wa juna hare-hare.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. 'Yan bindiga sun kashe Bashar Namaska ɗan sarkin Kontagora

    'Yan bindiga

    Wasu 'yan fashin daji sun halaka Alhaji Bashar Saidu Namaska, ɗan sarkin Kontagora da ke Jihar Neja a arewacin Najeriya yayin wani hari da suka kai gonar mahaifin nasa a ranar Laraba.

    Wata majiya a fadar gwamnatin jihar ta shaida wa BBC cewa maharan sun kashe wasu dabbobin kiwo a gonar.

    Majiyar ta ƙara da cewa 'yan bindigar sun je gonar ce kai-tsaye, inda suka yi awon gaba da shanu da dama.

    Kafin rasuwar Bashar Saidu Namaska, shi ne Hakimin Cikin Gari kuma Sardaunan Kontagora.

  7. Hukumar EFCC ta ƙwato Naira biliyan 1 daga hannun wani ma'aikacin gwamnati

    EFCC Chairman

    Asalin hoton, EFCC

    Hukumar EFCC a Najeriya ta ce ta ƙwato naira biliyan ɗaya daga hannun wani ma'aikacin gwamnatin Najeriya da ba a bayyana sunansa ba.

    Shugaban Hukumar, AbdulRasheed Bawa ya bayyana haka a loakcin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa da ke kula da sashen kuɗaɗen shiga na hukumomin gwamnati.

    Ya bayyana cewa a makon da ya gabata ne aka gano kuɗin da ke ajiye a asusun bankin ma'aikacin gwamnatin.

    A watan Fabrairu ne Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa AbdulRasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar bayan sauke Ibrahim Magu.

  8. Mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza sun kai 232 zuwa yanzu

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Adadin Falasɗinawa da aka kashe sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kaiwa a birnin Gaza ya kai 232, a cewar ma'aikatar lafiya da ke ƙarƙashin ikon ƙungiyar Hamas.

    Adadin ya ƙunshi yara 66 da kuma mutum 1,900 waɗanda aka jikkata.

    A Isra'ila kuma, mutum 12 ne aka kashe sakamakon makaman roka da Hamas ke harbawa, ciki har da yara biyu a cewar sashen lafiyar ƙasar.

  9. Tsohon shugaban Faransa Sarkozy ya sake gurfana kan zargin kashe kuɗin kamfe

    Nicolas Sarkozy

    Asalin hoton, Reuters

    Nicolas Sarkozy, tsohon shugaban Faransa, ya sake gurfana a gaban kotu kan zargin saɓa doka wajen ɗaukar nauyin kamfe ɗin zaɓensa.

    Mista Mr Sarkozy wanda ya musanta zarge-zargen, yana fuskantar tuhuma ne tare da wasu mutum 13 bisa zarginsu da hannu a badaƙalar "Bygmalion".

    Ana zargin su da kashe miliyoyin yuro yayin kamfe ɗin, sannan suka ɗauki hayar wani kamfanin hulɗa da jama'a domin ya shafe batun.

    Wannan ce shari'ar baya-bayan nan da ake yi wa tsohon shugaban bayan kotu ta ɗaure shi a farkon shekarar nan da laifin cin hanci.

    Ya kamata a yi shari'ar tun a watan Maris, amma sai wani lauya ya kwanta jinyar cutar korona.

  10. Jihohin Adamawa da Gombe sun haramta ayyukan mafarauta da 'yan banga

    Inuwa Yahaya

    Asalin hoton, @GovernorInuwa

    Sakamakon rikicin ƙabilanci tsakanin al'ummar Lunguda da Waja, gwamnatocin Adamawa da Gombe sun haramta ayyukan ƙungiyoin 'yan banga da mafarauta a yankunan.

    Lunguda da Waja ƙabilu ne maƙotan juna da ke zaune a jihohin na Adamawa da Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Umarnin hanin na ƙunshe ne cikin wata sanarwar bayan taron sulhu da aka gudanar tsakanin al'ummomin, wanda aka yi a Ƙaramar Hukumar Numan ta Adamawa, kamar yadda kamfanin labarai na NAN ya ruwaito.

    Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa da Muhammad Yahaya na Gombe, su ne suka saka wa sanarwar hannu.

    "Dukkan sansanin 'yan gudun hijira a yankunan za a rufe su tsawon mako ɗaya kuma mutane za su koma gidajensu," a cewar sanarwar.

    "Haka nan, an soke ayyukan dukkan ƙungiyoyin mafarauta da na 'yan banga a yankunan jihohin guda biyu."

  11. Sojojin Najeriya na bincike kan labarin mutuwar Shekau

    Leo Irabor

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Rundunar sojan Najeriya ta ce tana bincike game da rahotannin da ke cewa an kashe shugaban ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau.

    Ya zuwa yanzu ba a san inda Shekau yake ba tun bayan samun rahotannin da ke cewa ya mutu sakamakon wata fafatawa tsakanin dakarunsa da kuma na ƙungiyar ISWAP, wadda ta ɓalle daga Boko Haram.

    Mai magana da yawun rundunar, Birgediya Mohammed Yerima, ya faɗa wa BBC cewa suna bincike kan lamarin amma ba za su ce komai har sai sun samu cikakkiyar hujja game da mutuwar tasa.

    Wata kafar labarai mai majiya daga hukumomin tsaro ce ta fara ruwaito mutuwar ta Shekau a faɗan da ya ɓarke a Dajin Sambisa da ke Jihar Borno.

    'Yan Najeriya da dama na murna da labarin mutuwar musamman a shafukan sada zumunta.

    Ƙungiyoyin biyu sun sha fafatawa kan iko da wasu yankuna, a cewar kamfanin labarai na AFP.

    An sha bayyana kisan Abubakar Shekau a baya amma yana fitowa ya ƙaryata, sai dai wannan ne karon farko da rahotanni ke cewa mayaƙan wata ƙungiya ne suka kashe shi ba jami'an tsaro ba.

  12. Ba mu yarda Buhari ya ranto kudi ba daga kasashen waje - PDP

    Bayanan sautiRahoton Ibrahim ISa kan matsayar PDP game da rancen kudi da APC za ta yi

    A Najeriya, babbar jam`iyyar hamayyar kasar, wato PDP ta soki lamirin gwamnatin APC mai mulki dangane da aniyarta ta cin bashin fiye da naira tiriliyon daga kasashen waje don cike gibin kasafin kudin wannan shekarar.

    Shugaba Muhammadu Buhari ya tura wa majalisun dokokin kasar bukatar amincewarsu don karbar rancen, wanda gwamnatin ta ce za ta yi amfani da shi wajen samar da abubuwan more rayuwa ga al`umma.

    Amma jam`iyyar PDP ta ce cin bashin da gwamnati ke yi ya wuce kima, kuma yunkuri ne na sayar da `yancin kasar.

  13. An daga babban zabe a Ehiopia zuwa watan gobe

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar zabe ta Habasha ta dage babban zaben kasar da kwana 16 kan yadda aka tsara tun da farko.

    Yanzu sai ranar 21 ga watan Yuni za a gydanar da zaben.

    Wannan ne karo na biyu da aka dage zaben.

    A bara ya kamata a gudanar da zaben amma an dage saboda annobar korona.

    Wannan jinkiri ya kara ta'azzara rikicin siyasa a kasar yayin da wasu kungiyoyi ke zargin gwamnatin Abiy Ahmed da amfani da annobar domin ci gaba da zama a kan mulki ba bisa ka'ida ba.

  14. Sifaniya ta zargi Moroko da bata mata suna kan 'yan cirani

    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

    Sifaniya ta zargi Moroko da bata mata suna kan matsalar 'yan cirani, biyo bayan karuwar tururuwar dubban 'yan cirani da aka samu zuwa Sifaniya daga arewacin Afrika.

    Ministan harkokin wajen kasar Margarita Robles, ya ce Sifaniya ba za ta sarayar da kimar kasarta ba ya kuma yi kira da Moroko ta girmama dokar kasa da kasaa.

    Madrid ta zargi Rabat d kyale 'yan ciranin suna tsallaka wa kasarta, saboda shugaban 'yan aware Brahim Ghali na karbar magani a kasar.

  15. Rigakafin korona na China na da tasiri akan sabon nau'in cutar

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani babban jami'i a China ya ce alluran rigakafin korona na kasar suna da tasiri a kan sabon nau'in annobar da ya bulla a India sai dai bai yi karin bayani kan lamarin ba.

    Mai binciken daga cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta China ya ce gwaje-gwajen farko da aka yi sun nuna cewa alluran rigakafin korona na China suna ba da kariya ga cutar.

    Bai yi karin haske kan alluran ko nau'ukan cutar da aka yi gwajin a kai ba.

    A yanzu dai China ta yi wa kusan mutum miliyan dari hudu da hamsin rigakafin cutar.

  16. Gwamnonin Kudu ba su da 'yancin hana kiwo - Abubakar Malami

    BBC

    Ministan Shari'a na Najeriya Abubakar Malami ya ce gwamnonin Kudancin kasar ba su da hurumin da za su hana kiwo a jihohinsu.

    A makon da ya gabata ne kungiyar gwamnonin Kudancin Najeriya suka yi wani taro tare da haramta kiwo a yankin saboda matsalar tsaro.

    Wannan mataki na gwamnonin ya ci karo da suka ta ko ina a fadin kasar.

    Da yake amsa tambaya a cikin shirin gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, Malami yace matakin ya saba doka, kuma hakan take hakkin 'yan Najeriya ne.

    Gwamnonin sun ce karuwar garkuwa da mutane da kashe-kshen da yankin yake fama da shi ne ya ja sauka dauki wannan mataki.

    Sai dai malami yace babu wani dan Najeriya da ke da 'yancin hana wani dan Najeriya 'yancin zuwa inda yake so a kasar>

  17. Yara na shan wahala a rikicin Mozambique - Save the Children

    Wata kungiyar agaji ta kasa da kasa ta ce yara na shan wahala sakamakon rikicin masu ikirarin jihadi a arewacin Mozambique.

    A wani sabon rahoto, Kungiyar Save the Children ta ce yara da dama ba su san inda iyayensu suke ba, ba sa iya zuwa makaranta sannan sun rasa takardunsu na shaidar zama yan kasa.

    Rikicin ya daidaita sama da yara dubu dari uku sannan yara kimanin dubu biyu da dari biyar sun rabu da iyayensu.

    Kungiyar ta ce da yawan yaran sun fuskanci mummunan tashin hankali.

    Fiye da shekara uku ke nan masu ikirarin Jihadi na zafafa kai hare-hare a arewacin Mozambique inda suke kai hare-hare kan garuruwa da kauyuka da kuma kona gidaje.

  18. Mutum miliyan 55 sun tsere daga muhallnsu a fadin duniya - Bincike

    Sakamakon wani sabon bincike da aka gudanar, ya nuna sama da mutum miliyan 55 a fadin duniya sun tsere daga muhallansu, inda suke zaman gudun hijira a cikin kasashensu.

    A rahoton cibiyar da ke sanya ido kan wadanda suka rasa muhallansu na shekara-shekara, cibiyar ta ce an samu matukar karuwa kan hijirar dole da mutane ke yi.

    Sabon tashin hankalin da ake yi a kasashen Habasha da Mozambique ya tilasta wa dubban mutane tserewa daga muhallansu, yayin da shekarun da aka dauka ana yaki a kasashen Syria da Afghanistan da Yemen da sauransu na ci gaba da tilasta wa 'yan kasashen zama 'yan gudun hijirar dole.

    Sai kuma wadanda ibtila'in ambaliyar ruwa ko fari ke tilastawa yin hijirar.

    Cikin shekara 10 an samu karuwa fiye da kima, tare da gargadin idan ba a dauki mataki na rikice-rikicen siyasa da na addini da kabilanci, da sauyin yanayi ba, yanayin zai kara munana.

  19. Gwamnan Cross Rivers ya koma APC

    ik

    Asalin hoton, Other

    Gwamnan Jihar Cross Rivers Ben Ayade ya fice daga PDP ya koma jam'iyya mai mulkin kasar ta APC, tare da kira ga sauran takwarorinsa na PDP su bi sahunsa.

    Gwamnan ya bayyana sauya shekar ta sa ne a gidan gwamnatin kasar da ke Calabar yayin wata tattaunawa da ya yi da shugabannin APC a JIhar.

    Ayade ya ce dalilin komawar ta sa, ya zama shi ne shugaban APC a jihar, kuma duk wani abin da jam'iyyar za ta yi zai zaman karkashin ikonsa.

    Yace akwai bukatar da ke kansa da sauran gwamnoni ta su hada hannu domin aiki tare da shugaba Muhammadu Buhari.

    Ayade ya ce "Akwai bukatar hada karfi wuri guda domin aiki da shugaba Buhari don ganin yadda za a gyara goben kasar nan.

    "Ina bukatar sauran gwamnoni da su bi sahu na su kuma fahimci mataki na na komawa APC. Muna da bukatar aiki da Buhari domin samar da hadin kai da kuma dunkulalliyar Najeriya a gobe. Akwai bukatar zama kasancewa wuri daya da Shugaban ksa domin ciyar da Najeriya gaba," in ji Ayade.

    Cikin gwamnonin da suka karbe shi akwai Kayode Fayemi (Ekiti), Simon Lalong (Plateau), Hope Uzodinma (Imo) and Abubakar Badaru (Jigawa).

    Duka a karkashin shugabancin Mai Mala Buni na Yobe, wanda shi ne shugaban kwamitin rikon jam'iyyar a yanzu.

  20. Gwamnoni ba su goya min baya a rikicina da NLC ba - El-Rufa'i

    GETTY IMAGES

    Asalin hoton, GETTY IMAGES

    Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i ya zargi takwarorinsa gwamnoni kan cewa ba su bashi goyon bayan da ya kamata ba lokacin da yake fuskantar bore daga NLC.

    NLC ta janyo koma bayan tattalin arziki a Kaduna kan abin da ta kira manufofin El-Rufa'i na kin al'umma.

    A yajin aikin gargadin da suka yi, wanda aka dakatar bayan kwana uku da farawa, kuma aak yi zanga-zanga kan titi suna kiran a dawo da ma'aikata 4,000 da aka kora.

    Sai dai jaridar Daily Trust ta ce ta yi ta kawo labaran da kungiyar gwamnonin take kira ga El-Rufa'i da kuma shugabannin NLC domin a zauna a teburin sulhu a samu matsaya a daina ta da jijiyoyin wuya.

    "Wannan ba lokacin ta da jijiyoyin wuya ba ne. Klubale da yawan sun mamaye Najeriya. A wannan lokaci da tafiyar dimokradiyyarmu ta fara nisa. Ya kamata a rika duba yadda za a shawo kan matsalar da ke faruwa tsakanin gwamnatin Kaduna da NLC. Mun nemi duka bangarorin biyu su sausauta fushinsu," Kamar yadda Gwamna Atiku Bagudu ya fitar a sanarwarsa.