Ƙungiyar ƙwadago ta janye yajin aiki a Kaduna

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da sauran ƙasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur and Umar Mikail

  1. Saudiyya za ta bai wa Afrika tallafin dala biliyan ɗaya don rage raɗaɗin annobar korona

    Mohammed Bin Salman

    Asalin hoton, Reuters

    Saudiyya za ta tallafa wa Ƙasashen Afrika da hannun jari da bashi da adadinsu ya kai dala biliyan ɗaya a wannan shekarar don farfaɗo da tattalin arzikin su daga gibin da annobar korona ta bari, in ji Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ranar Talata.

    "Asusun Saudiyya na Ci Gaba zai kaddamar da wasu ayyuka nan gaba, da bayar da bashi da kuɗinsu ya kai riyal biliyan uku ko kusan $1,000,000,000 a ƙasashe masu tasowa a Afrika cikin wannan shekarar," a cewar yariman a wani jawabi da ya yi a wani taro a birnin Paris.

    Ya ce kuma ce ƙasarsa ta zuba kusan dala biliyan huɗu a fannonin makamashi da haƙar ma'adinai da sadarwa da abinci da sauran ɓangarori a Afrika kuma ya ce za ta ci gaba duba wasu fannonin a wasu ɓangarorin nahiyar.

    Shugabannin Afrika da sauran masu ruwa da tsaki sun gana a Paris ranar Talata don lalubo hanyoyin tallafa wa tattalin arzikin ƙasashen Afrika da annobar korona ta shafa da kuma tattauna basukan da nahiyar ke da su.

  2. Ba sabon bashi Shugaba Buhari zai karbo ba - Majalisa

    'Yan majalisar dokokin Najeriya sun yi karin haske a kan wata wasika da shugaban kasar ya aike wa majalisar dattawa da ta wakilai, wadda a ciki ya nemi amincewarsu domin ya karbo rancen naira tiriliyon biyu da miliyan dari uku, don cike gibin kasafin kudin kasar na wannan shekarar.

    Tuni dai maganar rancen ta fara jan hankalin 'yan Najeriya, har wasu na sukar gwamnatin APC mai mulki, wadda a cewar su karbar rancen na neman wuce kima.

    Amma shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan kasar, Sanata Yahaya Abdullahi ya bayyana cewa ba wani sabon bashi shugaban kasar zai ciwo ba, kudurin majalisar kawai yake neman don cika sharadin karbar rance, wanda aka yi maganarsa tun lokacin da aka gabatar da kasafin kudin wannan shekarar.

    Ga yadda hirarsa da Ibrahim Isa ta kasance:

    Bayanan sautiHirar Ibrahim Isa da Sanata Yahaya Abdullahi
  3. An shiga rana ta goma ta faɗa tsakanin Hamas da Isra'ila

    Gaza Hamas

    Asalin hoton, Reuters

    An ci gaba da gwabza fada tsakanin kungiyar Hamas mai fafutukar kare Falasɗinawa da Isra'la a rana ta goma a jere.

    Kafin wayewar garin nan Isra'ila ta rika kai hari da jiragen sama a garin Khan Younus , yayin da Hamas din ke harba manyan rokoki zuwa kudancin Isra'ilan.

    Wakilin BBC yace fadar gwamnatin Faransa ta ce za ta gabatrwa majalisar dinkin duniya wani kuduri kan rikicin na gaza, a maimakon fitar da sanarwa kawai domin a kada kuri'a.

    Shugaba Emmanuel Macron ne ya amince da matakin wanda zai taimaka wajen kai kayan agaji zuwa zirin na Gaza, bayan wata zantawa da takwarorinsa na Masar da kuma Jordan.

  4. Ana ci gaba da binciken kamfanin Donald Trump

    Donald Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Ofishin babban lauyan gwamnatin New York a Amurka ya ce binciken da yake gudanarwa kan wasu zarge zarge da ake yi wa kamfanin tsohon shugban kasar Donald Trump da ake kira Trump Organisation ya zama na aikata babban laifi.

    Binciken yana duba zargin ko kamfanin ya yi karya wajen bayyana kimar kadarorinsa don samun rance.

    Wakilin BBC ya ce matakin ya kara matsi ga Mista Trump sosai.

    Kazalika binciken na kuma duba zargin badakalar haraji da zamba cikin aminci da amfani da bayanan kasuwanci na bogi.

    Mista Trump ya sha musanta aikata ba daidai ba.

  5. China ta zargi Amurka da barazana ga zaman lafiya a mashigin Taiwan

    China ta zargi Amurka da yin barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan, bayan da ta gindiya jirgin ruwanta tsakanin kasashen biyu.

    Jiya Talata, jirgin ruwan yakin mai suna USS ya yi abin da Sojojin Amurka suka kira dan yada zango kamar yadda dokar kasa da kasa ta bashi dama.

    Beijing wadda ke kallon Taiwan a matsayin wani bangarenta, ta ce babu abunda hakan zai haifar face dagula al'amura.

    Ba dai wannan ne karon farko da sojojin Ruwan na Amurka ke irin wannan yada zaggo a wajen ba.

  6. Buɗewa

    Barkanku da kasancewa da mu a wannan shafin mai kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da sauran ƙasashen duniya.