Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ƙungiyar ƙwadago ta janye yajin aiki a Kaduna

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da sauran ƙasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur and Umar Mikail

  1. 'An kusa cimma matsaya kan yarjejeniyar nukiliyar Iran'

    An kammala tattaunawa kan ƙoƙarin farfaɗo da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta shekarar 2015 a Vienna, inda mahalarta taron suka ce an samu ci gaba sosai.

    Jami'in Tarayyar Turai wanda ke jagorantar tattaunawar, Enrique Mora, ya ce yana da yaƙinin za a cimma yarjejeniya ta ƙarshe.

    Wakilin Rasha, Mikahil Ulyanov, ya ce yana ganin an kusa cimma yarjejeniya.

    An yi tattaunawar da nufin ganin Amurka ta sake shiga yarjejeniyar yayin da Iran za ta ci gaba da cika alkawuranta na nukiliyar, waɗanda suka haɗa da daina inganta makamashin uranium.

  2. Darajar Bitcoin ta faɗi yayin da China ta haramta amfani da shi

    Farashin kuɗin intanet na Bitcoin ya yi ƙasa da dala 34,000 a karon farko cikin wata uku bayan China ta sanya dokokin haramci kan masu amfani da kuɗaɗen intanet ɗin wato cryptocurrency.

    A jiya Talata ne China ta hana cibiyoyin kuɗi da kamfanoni yin mu'amala da masu hada-hada da kuɗin intanet.

    Haka nan ta gargaɗi masu zuba jari game da mu'amala da su a ɓoye.

    Wannan ya biyo bayan faɗuwar da kuɗin ya yi a makon da ya gabata da kashi 10 cikin 100 bayan kamfanin ƙera motoci na Tesla ya ce ya daina karɓar kuɗin na Bitcoin.

    Zuwa ranar Litinin, darajar kuɗin ta faɗi da kashi 22 cikin 100, faɗuwar da ta kai kusan dala 6,000 a cikin awa 24.

    A gefe guda kuma, kuɗaɗen Ethereum da Dogecoin sun yi faɗuwar kashi 25 da 29 cikin 100 kowannensu.

  3. Kamfanin sufurin jirgin sama na Najeriya zai fara aiki a 2022 - Hadi Sirika

    Ministan Sufurin Jiragen Sama a Najeriya, Hadi Sirika, ya ce sabon kamfanin sufurin jirgin sama na ƙasar zai fara aiki nan da farkon shekarar 2022.

    Rahotanni sun ambato ministan na bayyana haka ne a yau Laraba yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartarwa, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

    "A shekarar nan ta 2021, za mu yi ƙoƙarin yin duk abin da ya kamata, muna sa ran mu fara zirga-zirga a cikin wata huɗu na farkon 2022," in ji ministan.

    Ya ƙara da cewa annobar korona ce ta jawo jinkiri game da ƙarasa aikin buɗe kamfanin da kuma fara zirga-zirgarsa, yana mai cewa har yanzu gwamnati ta duƙufa wajen yin hakan.

    Sirika ya ce ma'aikatarsa za ta miƙa daftari ga masu ruwa da tsaki nan da mako biyu. A wannan shekarar ne aka tsara jirgin zai fara aiki, a cewar Hadi Sirika.

  4. Labarai da dumi-dumi, Ƙungiyar ƙwadago ta janye yajin aiki a Kaduna

    Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) janye yajin aikin da ta shiga a Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

    Nasir Kabir mai magana da yawun ƙungiyar, shi ne ya tabbatar wa da BBC janyewar.

    Ya ce matakin ya biyo bayan kiran da suka samu ne daga fadar shugaban Najeriya a Abuja, inda aka neme su domin tattaunawa da ɓangaren gwamnatin jihar.

    Ministan Ƙwadago na Najeriya, Chris Ngige, shi ne zai shiga tsakani a ganawar da za ta gudana da ƙrfe 10:00 na safiyar gobe Alhamis a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

    A ranar Litinin da ta gabata ne NLC ta shiga yajin aikin kwana biyar na gargaɗi ga gwamnatin Kaduna ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir El-Rufai dangane da korar ma'aikata 7,000 da ta yi.

  5. Joe Biden ya umarci Isra'ila ta sassuata hare-hare kan Falasɗinawa

    Shugaban Amurka Joe Biden ya faɗa wa Firaministan Isra'ila cewa yana son "a sassauta sosai" a hare-hare kan birnin Gaza a yau Laraba.

    Wannan ne karon farko da Joe Biden ya matsa wa Isra'ila kai-tsaye don ta tsagaita wuta a hare-haren - ko kuma dai karon farko da ya nuna ƙaguwa kan hakan.

    Kafin yanzu, ya yi ta nanata cewa Isra'ila na da 'yancin kare kanta kuma lallai sai Hamas ta daina harba makaman roka cikin ƙasar.

    A yau, ya faɗa wa Firaminista Benjamin Netanyahu cewa wajibi ne a fara kawo ƙarshen hare-haren domin samar da tsagaita wuta.

    Ya alaƙanta maganar tasa da abin da ya kira rage wa Hamas ƙarfin iko da kuma yanayin rayuwa a Gaza, wadda ke ƙara taɓarɓarewa.

    An sha uzura wa Biden cewa ya saka baki sosai don kawo ƙarshen rikicin.

    Yayin da ake shirin gudanar da taron Zauren Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya a gobe Alhamis, da alama ya nuna cewa Amurka ba za ta sake kare Isra'ila ba a siyasance.

  6. Kaduna: Kamfanin lantarki ya ba da haƙuri yayin da aka shiga kwana na 4 cikin duhu

    Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna wato Kaduna Electric ya sake bai wa kwastomominsa haƙuri game da rashin wuta a jihar tsawon kwana huɗu.

    Jihar ta Kaduna ta tsunduma cikin duhu ne tun ranar Lahadi sakamakon yajin aikin da ma'aikata ke yi bayan da suka amsa kiran ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa game da korar abokan aikinsu da gwamnatin jihar ta yi.

    "Muna sane da irin hanƙoron da kwastomominmu ke yi na ganin lantarki ta dawo," a cewar kamfanin cikin wata sanarwa a yau Laraba. "Abin ya fi ƙarfinmu...Muna ba ku haƙuri.

    "Muna masu baƙin cikin shaida muku cewa har yanzu ba a samu wani ci gaba ba game da sasanta rikicin da ya jawo ɗaukewar wutar lantarkin a Jihar Kaduna."

    Kamfanin ya ƙara da cewa yana da ƙarin gwiwar ɓangarorin biyu za su gaggauta sasantawa da juna domin ayyuka su ci gaba da gudana.

    Har yanzu ana ci gaba da cacar baki tsakanin ƙungiyar ƙwadago (NLC) da Gwamna Nasir El-Rufai game da korar ma'aikatan, waɗanda gwamnatin jihar ta ce ta kore su ne "saboda ta yi wa aikikn gwamnati kwaskwarima".

  7. Najeriya ta tsara wasannin sada zumunta a Turai da Amurka duk da rashin kuɗi

    Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Kamaru da Mexico a nahiyar Turai da Kudancin Amurka, duk da rashin kudi da hukumar kwallon kafar kasar ke fama.

    Kocin tawagar kwallon kafar Najeriya, Gernot Rohr, na bin hukumar bashin albashin wata shida da ba a biya shi ba.

    Duk da fama da rashin kudi da take fuskanta, NFF ta tsara wasan sada zumunta da Super Eagles za ta kara da tawagar Kamaru a Vienna, Austia ranar 4 ga watan Yuni.

    Haka kuma, Najeriya za ta kece raini a wasan sada zumuntar dai da Mexico a Los Angeles na Amurka, wata daya tsakani a karawa da Kamaru.

    A watan Janairu shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya, Amaju Pinnick, ya ce yana ta fafutukar ganin ya biya dukkan bashin da ake bin hukumar.

  8. Za a fara barin masu ragakafin korona shiga ƙasashen Turai

    Kasashe mambobin ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) na bayar da shawarar a fara barin mutanen da aka yi wa allurar rigakafin korona ko kuma wadanda suka fito daga ƙasashen da cutar ba ta yi kamari ba damar zuwa Turai.

    Wakiliyar BBC ta ce da safiyar yau Laraba ne jakadun suka goyi bayan kudirin bude iyakokin Turai ga masu zuwa hutu da aka yi wa allurar rigakafin korona da ta samu sahhalewar EUn.

    A ranar Juma'a ne kuma za a fitar da jerin kasashen da za su iya zuwa Turai ba tare da nuna shaidar rigakafin ba.

    Kawo yanzu, babu masaniya ko za a hada har Burtaniya ganin cewa kasar ta samu bullar sabon nau'in cutar da ya yaɗu a Indiya.

    Jakadun Tarayyar Turan sun ce ya rage ga ɗaiɗaikun ƙasashe mambobi su yanke shawara kan wasu takamaiman dokoki kuma za su iya neman a yi gwaji ko kuma mutum ya killace kansa.

  9. Hukumar NDLEA ta kama mota ɗauke da ƙwayoyin Tramadol miliyan 5

    Jami'an hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA sun kama wata kwantena maƙare da ƙwayoyin Tramadol miliyan biyar da nauyinsu ya kai kilogiram 2,498.2 a tashar jirgin ruwa ta Onne a Fatakwal, jihar Ribas.

    Hukumar ta ce baya ga wannan, ta ƙwace kilogiram 218.6 a jihohin Adamawa da Ondo.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun NDLEA Femi Bababfemi ya fitar ranar Laraba, ta ce yunƙurinta na hana shiga da ficen miyagun ƙwayoyi ne ya haifar da wannan nasarar.

    Ya bayyana cewa ƙwace ƙwayoyin da aka ɓoye cikin kwalaye 1,387 ya biyo bayan binciken haɗin gwiwa da hukumar ta yi tare da haɗin gwiwar jami'an hukumar hana fasaƙwabri.

  10. Ana safarar ƙananan yara don noma cocoa a Ivory Coast

    Yan sanda a Ivory Coast sun ce kimanin mutum 22 aka kulle saboda yin safarar kananan yara domin yin noman cocoa.

    An yanke wa biyar daga cikinsu hukuncin shekara 20 a gidan yari yayin da sauran kuma za su shafe shekara biyar a kulle.

    An kama su ne a farkon watan nan inda kuma aka kubutar da yara kusan 70 daga hannunsu. Kusan mutum miliyan shida ne ke aiki a gonakin cocoa da ke kasar.

    Wani bincike da aka yi a baya-bayan nan ya bayyana cewa kimanin dubu dari takwas na ma'aikatan yara ne kuma galibinsu sun fito ne daga makwabtan kasashe kamar Mali da Burkina Faso.

  11. Jirgin ruwa ya nutse da mutum 22 bayan guguwa ta kifar da shi

    Masu aikin ceto a Yammacin Indiya sun gano gawarwaki 22 daga cikin teku, kwanaki bayan da wasu ma'aikatan mai suka yi batan dabo sanadin wata kakkarfar guguwa da ta afku.

    Guguwar mai suna Tauktae ta afka wata tashar mai da ke kusa da Mumbai kuma ta yi sanadiyyar nutsewar wani jirgin ruwa dauke da mutum 261.

    Har yanzu ba a san inda mutum 60 suke ba.

    Rundunar sojin ruwan Indiya ta ce ta aike jiragen ruwa da jiragen sama domin ceton mutanen da suka bata.

    Guguwar mai karfi ta yi barna sosai inda kuma ta halaka dukiya a gabar yammacin kasar.

  12. Ƴan bindiga sun kashe sojoji uku a jihar Neja

    Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya bayyana cewa ƴan bindiga sun kashe sojoji uku a ƙaramar hukumar Magama ta jihar, kamar yadda Jaridar Premium Times ta ruwaito.

    Sai dai Gwamna Abubakar Bello ya ce an kashe wasu daga cikin ƴan bindigar kuma an gano gawarwakin biyu daga cikinsu lokacin da jami'an tsaro suka bi sahun sauran ƴan bindigar.

    Haka kuma, jaridar ta ruwaito cewa al'ummomi 25 da ayyukan ƴan bindiga suka raba da muhallansu sun fara komawa gida a ƙauyukansu da ke ƙananan hukumomin Shiroro da Munya da Mariga.

    Gwamnan ya ce yana sa ido kan ƴan gudun hijira a jiharsa kuma ya ce komai na tafiya yadda ya dace.

    Sai dai gwamnan ya ce har yanzu akwai barazanar tsaro a wasu yankunan jihar amma ya ce jami'an tsaro na aiki ba dare ba rana don shawo kan matsalar.

  13. Jirgi marar matuƙi na kai riga-kafin korona ƙauyuka a Ghana

    Hukumomi a Ghana sun aika jirage marasa matuƙi don kai akwatunan da ke ɗauke da allurar riga-kafin korona a yankunan da ba suda tituna.

    Ƙasar na yi wa mutane allurar guda 360,000 na AstraZeneca da aka ɗakko daga Jamhuriyar Demokuraɗiyyar Congo inda mutane ke jan kafar karɓar allurar.

    Ana aika allurar ne a yankuna 43 kuma mutanen da suka karɓi allurar farko ne kawai za a yi wa ta biyun.

    Kusan mutane 900,000 ne a Ghana aka yi wa allurar tun da aka fara bayar wa a watan Maris.

    Shirin gwamnati na yi wa duka mutanen ƙasar da shekarunsu suka haura 18 zuwa ƙarshen shekara ya fuskanci naƙasu bayan da Indiya ta dakatar da fitar da allurai saboda ƙaruwar yaɗuwar cutar a ƙasarta.

  14. Malawi ta ƙona dubban allurar riga kafin cutar korona

    Hukumomin lafiya a Malawi sun ƙona allurar rigakafin korona 19,610 ta AstraZeneca, inda suka ce hakan zai ƙara tabbatar wa mutane cewa duk allurar da aka yi masu mai inganci ce.

    Ita ce ƙasar Afrika ta farko da ta ƙona rigakafin a bainar jama'a.

    Da farko Hukumar Lafiya ta Duniya ta bukaci ƙasashe kan kada su lalata rigakafin da ta lalace amma a yanzu ta sauya matsaya.

    Mutane da yawa a Malawi ba su mika wuya ga karɓar allurar ba amma ma'aikatan lafiya na fatan wannan matakin zai sauya ra'ayin mutane.

    Cikin mutane miliyan 18 da ke kasar, mutum 32,232 ne suka yi cutar korona kuma 1,153 ne suka mutu.

  15. Kalli bidiyon zanga-zangar Ƙungiyar Ƙwadago a Kaduna

    An shiga rana ta uku a zanga-zangar da ƙungiyar ƙwadago a Najeriya ta shirya kan korar ma'aikatan gwamnati da gwamnan jihar Nasir El-Rufa'i ya yi.

    kungiyar ƙwadagon da gwamnan dai na takun saƙa kan wannan mataki, kuma ta bukace shi da ya mayar da ma'aikatan bakin aikinsu yayin da shi kuma gwamnan ya kafe ya kuma ce yana kan bakansa.

    Kawo yanzu an dakatar da duka ayyukan kasuwanci da kusan duka masana'antu a jihar.

  16. Ƴan sanda sun hana masu zanga-zanga wucewa a Kaduna

    Ƴan sanda a jihar Kaduna sun tare titin da ofishin Ƙungiyar Ƙwadago reshen jihar Kaduna ya ke.

    Wannan na nufin masu zanga-zanga ba za su iya wucewa ba.

  17. Ana kira a ƙarfafa tsaro a mashigar Tekun Guinea

    Kusan kungiyoyi dari da ke gudanar da harkar safara ta jiragen ruwa sun yi kira da a hada karfi da karfe don yaki da matsalar fashin teku a mashigar Guinea, inda ake yawan kai wa jiragen ruwa hari.

    Cikin hare hare hare dari da talatin da biyar da aka kaiwa jiragen ruwa a duniya kusan fiye da biyar an kai su ne a wannan yanki.

    Ba abun mamaki ba ne da ake kira a ƙara ba da tsaro a mashigar tekun Guinea.

    Cikin hare-hare 135 da aka kai wa jiragen ruwa a faɗin duniya, guda biyar ne kawai ba a kai ba a mashigar tekun Guinea.

    Gungun ɓarayi da ke ayyukansu a Najeriya ne ke kai mafi yawan hare-haren.

  18. Isra'ila da Hamas sun musanta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

    Ƙungiyar Hamas ta Falasɗinu da Isra'ila sun musanta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da rahotanni suka ce za a fara ranar 20 ga wannan watan na Mayu.

    Rikicin Isra'ila da Falasɗinawa ya shiga kwana na goma a yau da kisan Falasɗinawan 218 a Zirin Gaza da 25 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

    A Isra'ila, mutum 12 aka kashe tun da aka fara rikicin ran 10 ga watan Mayu.

    Dama dai an fara rikicin ne lokacin da wata kotu a Isra'ila ta yanke shawarar bayar da umarnin cire iyalan Falasɗinawa daga gabashin Birnin Ƙudus a unguwar Sheikh Jarrah don bai wa Yahudawa damar zama.

    Amurka da Faransa da Jamus da Masar da Jordan duk sun goyi bayan tsagaita wuta.

  19. An yi garkuwa da wani alƙali a cikin kotu a Katsina

    An yi garkuwa da wani alƙali ranar Talata a cikin kotunsa a jihar Katsina.

    Rahotanni sun bayyana cewa an yi garkuwa da alƙalin kotun shari'ar mai suna Alhaji Husaini Sama'ila ne da rana lokacin da wasu ƴan bindiga suka auka wa kotun a ƙauyen Bauren Zakat.

    Ba a san dalilin da ya sa alƙalin ke cikin kotun ba a lokacin tunda ma'aikatan shari'a na yajin aiki a faɗin ƙasar.

    Dama dai an mayar da kotun garin safana saboda matsalolin tsaro a ƙauyen na Bauren Zakat.

    Jihar Katsina na ɗaya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro.

  20. Ƴan bindiga sun kashe mutane 7 a majalisarsu ta hira a Zamfara

    A kalla mutum 7 aka kashe a wani hari da yan fashin daji suka kai kan wani ƙauye cikin gundumar Dan Sadau ta ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara da yammacin jiya.

    Wani mazaunin ƙauyen Hanhan ya ce an kashe mutanen ne lokacin da aka buɗe musu wuta suna zaune suna hutawa a majalisa. Ga ƙarin bayani a rahoton Mukhtari Adamu Bawa