Saudiyya za ta bai wa Afrika tallafin dala biliyan ɗaya don rage raɗaɗin annobar korona
Saudiyya za ta tallafa wa Ƙasashen Afrika da hannun jari da bashi da adadinsu ya kai dala biliyan ɗaya a wannan shekarar don farfaɗo da tattalin arzikin su daga gibin da annobar korona ta bari, in ji Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ranar Talata.
"Asusun Saudiyya na Ci Gaba zai kaddamar da wasu ayyuka nan gaba, da bayar da bashi da kuɗinsu ya kai riyal biliyan uku ko kusan $1,000,000,000 a ƙasashe masu tasowa a Afrika cikin wannan shekarar," a cewar yariman a wani jawabi da ya yi a wani taro a birnin Paris.
Ya ce kuma ce ƙasarsa ta zuba kusan dala biliyan huɗu a fannonin makamashi da haƙar ma'adinai da sadarwa da abinci da sauran ɓangarori a Afrika kuma ya ce za ta ci gaba duba wasu fannonin a wasu ɓangarorin nahiyar.
Shugabannin Afrika da sauran masu ruwa da tsaki sun gana a Paris ranar Talata don lalubo hanyoyin tallafa wa tattalin arzikin ƙasashen Afrika da annobar korona ta shafa da kuma tattauna basukan da nahiyar ke da su.