Buhari zai karɓo bashin fiye da tiriliyan biyu

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da sauran ƙasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur and Umar Mikail

  1. Wata ƙungiya na so a ba ta damar shan wiwi bisa dalilai na addini

    Rastafarian Society of Kenya

    Asalin hoton, EPA

    Wata ƙungiya a Kenya ta je kotu saboda tana so a ba ta damar shan wiwi bisa dalilai na addini.

    Ƙungiyar Rastafari Society of Kenya, wadda ke kallon kanta a matsayin ƙungiyar addini, ta ce mambobinta na rayuwa cikin fargaba saboda akwai dokokin da ke ja da addininsu.

    Lauyoyi Shadrack Wambui da Alexander Mwenda sun ce shan wiwi nau'i ne na ibada da ke haɗa masu bauta da abin bautarsu.

    Sun zargi hukumomi da ƙin martaba haƙƙoƙin addinin ƙungiyar.

    A shekarar 2019 ne wata babbar kotu a Kenya ta ayyana Rastafarian a matsayin ƙungiyar addini kamar ko wacce.

    Matakin ya biyo bayan wata shari'a ce inda wani mutum ya yi ƙarar wata makaranta bisa korar ƴarsa saboda irin gyaran gashin ƙungiyar Rastafari da ta yi.

  2. El-Rufa'i na neman Ayuba Wabba ruwa a jallo

    Gwamnan Kaduna Nasir Ahmed El-Rufa'i ya ce yana neman Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, Ayuba Wabba da wasu mutane ruwa a jallo.

    Gwamnan ya ce ana nemansu ne bisa laifin yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa da lalata kayan gwamnati ƙarƙashin dokar laifuka ta Miscellaneous Offences Act.

    El-Rufa'i ya ce duk wanda ya san inda ya ke ɓuya ya sanar da Ma'aikatar Shari'a ta jihar inda za a ba shi kyauta mai tsoka.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Guguwa mai karfi ta kashe mutum 20 a Indiya

    Guguwa a Indiya

    Asalin hoton, Getty Images

    A kalla mutum 20 ne wata guguwa mai karfi ta kashe a jihar Gujarat da ke Indiya.

    Guguwar wadda ake kira Tauktae, ta kasance mafi karfi cikin shekaru, sai dai ta fara lafawa a yanzu.

    An rufe manyan tashoshin jiragen ruwa da na sama, abun da ya janyo soke tashin a kalla jirage 50.

    Kimanin mutum 200,000 aka kwashe daga gidajensu don gudun abun da ka je ya zo.

    Masu fama da cutar korona da ke kwance a asibiti na cikin wadanda aka rika kwashewa.

    Guguwar ta yi kaca-kaca da bishiyoyi da layukan wutar lantarki, baya ga yaye rufin gidaje da dama yayin da take kadawa har zuwa gabar tekun arewacin Indiya.

  4. Shugaba Biden ya goyi bayan tsagaita wuta a Gaza bayan kwana takwas

    Joe Biden

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Joe Biden na Amurka ya nuna goyon bayansa ga tsagaita wuta bayan kwashe kwanaki takwas ana rikici tsakanin Isra’ila da Falasdinawa ‘yan gwagwarmaya a Gaza.

    Yayin wani kiran waya da Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, Mista Biden ya ce Amurka na aiki tare da Masar da wasu kasashe don dakatar da yakin.

    Wata sanarwa da fadar shugaban ta White House ta fitar, ta ruwaito shi yana kira ga Isra’ila da ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da kare fararen hula.

    Ya kuma jaddada goyon bayansa ga 'yancin Isra'ila na kare kanta daga hare-haren rokokin da ake kai mata, don haka ba wai ya canja alkibla ba ne, face kawai amsa kiran da ake ta faman yi na ya goyi bayan tsagaita wuta.

    A bangare guda kuma rundunar sojin Isra'ila ta ce ta mayar da martani ta hanyar harba manyan bindigu zuwa Lebanon, bayan harba mata rokoki 6 daga cikin kasar.

    Wannan na zuwa ne yayin kungiyar Hamas mai fafutukar kare Falasdinawa ke ci gaba da harba rokoki zuwa kudancin Isra'ilar.

    Tuni Masar ta fara kai tallafin kayan masarufi zuwa zirin Gazan.

    Kazalika motocin daukar marasa lafiya na kasar na ci gaba da kai Falasdinawan da suka jikkata asibitocin biranen Sinai da Alkahira.

  5. An shiga rana ta biyu ta yajin aiki a Kaduna

    Nasir El-Rufa'i

    Asalin hoton, Kaduna Governor

    An shiga rana ta biyu ta yajin aiki a jihar Kaduna.

    Yajin aikin da kuma zanga-zangar da kungiyoyin kwadago ke yi a jihar sun janyo tsaiko a akasarin ma’aikatu, da asibitoci da ma makarantun gwamnati a fadin jihar inda galibin ma’aikata suka shiga cikin yajin aikin.

    Duk da yake a jiya Litinin wato rana ta farko ta yajin aikin, jama’a sun ci gaba da zirga-zirga kamar yadda suka saba, sai dai kusan akasarin gidajen sayar da man fetur sun kasance a rufe, lamarin da ya haddasa karancin man fetur din yayin da kuma aka datse hanyoyin samar da wutar lantarki a fadin jihar---matakin da ya jefa dubban jama’a zama cikin duhu.

    A bangare guda kuma, ko da yake kasuwanni da dama sun buɗe, sai dai harkokin kasuwanci ba sa tafiya kamar yadda aka saba gani, abin da ya wasu ‘yan kasuwa suka gwammace su yi zamansu a gida.

    Kungiyar Kwagado ta NLC dai ta ce a yau Talata ma za ta ci gaba da gudanar da gangami kamar yadda ta fara a jiya don nuna wa duniya gallaza wa ma’aikata da take zargin gwamnatin jihar ƙarƙashin Nasir El-Rufai da aikatawa ta hanyar sallamar dubban ma’aikata ba tare da biyan haƙƙoƙinsu ba.

    Sai dai a wata sanarwa da ta fitar da yammacin jiya, gwamnatin Kaduna ta yi alla-wadai da zanga-zangar da kuma yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadagon ke yi.

    Sanarwar da mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin watsa labarai Mr Muyiwa Adekeye ya sanya wa hannu, ta ce irin munanan kalamai da ‘yan ƙwadagon ke danganta su da gwamnatin jihar ba za su canza komai ba.

    Sanarwar ta kuma yi zargin cewa duk da irin yunƙurin da ‘yan ƙungiyar NLC suka yi na neman hana wasu ma’aikata shiga sakatariyar gwamnatin jihar don gudanar da ayyukansu, haƙarsu ba ta cimma ruwa ba.

    Gwamnatin ta kuma zargi ƙungiyar da rufe asibitocin gwamnati da dama a faɗin jihar tare da korar majinyata da suka je don neman magani, ba ya ga uwa uba datse hanyoyin samar da wutar lantarki, abin da ta ce alama ce ta nuna tsabar rashin imani- Kuma a cewar gwamnatin, tana nan tana tattara bayanai kan irin waɗannan ayyuka da suka saɓa wa ka’ida.

    Ita dai gwamnatin Kaduna a sanarwar da ta fitar ta buƙaci al’ummomin jihar su ƙara haƙuri kan mawuyacin halin da suka shiga, inda ta ce zanga-zangar ta 'yan ƙwadago wata manuniya ce ƙarara kan yunƙurin yi mata zagon ƙasa.

    A ɓangare guda kuma rundunar ‘yan sandan ƙasar ta ce ta tura ƙarin jami’an tsaro da kayan aiki zuwa babban titin Kaduna zuwa Abuja, wanda ya yi ƙaurin suna kan satar mutane don neman kuɗin fansa bisa tsammanin samun ƙaruwar ababen hawa saboda rufe filin jirgin sama da tashar jirgin ƙasa a Kaduna, jihar da ke haɗa mafi yawan yankin arewacin ƙasar da kudanci.

  6. Akwai tsuntsayen daji biliyan 50 a duniya

    tsuntsaye

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani sabon bincike ya nuna cewa adadin tsuntsayen daji a doron duniya ya kai akalla biliyan hamsin, kana suna iya karuwa har zuwa biliyan dari hudu da talatin.

    Binciken wanda aka buga a mujallar kimiyya ta duniya na zaman irinsa na farko da aka yi don kimanta yawan tsuntsayen da ake da su.

    Ya tattara tarin bayanai daga kwararru da kuma masu bibiyar lamuran tsuntsaye a duniya.

    Sakamako ya nuna cewa mafi yawan jinsin da ake samu shi ne na Benu, da yawansu ya kai kusan biliyan daya-da miliyan 600.

    Wani abun jan hankalin shi ne adadin yawancin sauran nau'ukan tsuntsaye bai wuce dubu diyar biyar ba.

    Masu wannan bincike dai na fatan aikin da suka yi zai taimaka wajen kiyaye bacewar tsuntsayen daga duniya.

  7. Buɗewa

    Marabanku da shigowa wannan shafin wanda ke kawo maku labarai daga Najeriya da maƙwabtanta kamar Nijar da Ghana da Kamaru da Chadu da ma sauran ƙasashen duniya.

    Da fatan kun wayi gari lafiya.

    Kayan ƙwalam