An shiga rana ta biyu ta yajin aiki a jihar Kaduna.
Yajin aikin da kuma zanga-zangar da kungiyoyin kwadago ke yi a
jihar sun janyo tsaiko a akasarin ma’aikatu, da asibitoci da ma makarantun
gwamnati a fadin jihar inda galibin ma’aikata suka shiga cikin yajin aikin.
Duk
da yake a jiya Litinin wato rana ta farko ta yajin aikin, jama’a sun ci gaba da
zirga-zirga kamar yadda suka saba, sai dai kusan akasarin gidajen sayar da man
fetur sun kasance a rufe, lamarin da ya haddasa karancin man fetur din yayin da
kuma aka datse hanyoyin samar da wutar lantarki a fadin jihar---matakin da ya
jefa dubban jama’a zama cikin duhu.
A bangare guda kuma, ko da yake kasuwanni da dama sun buɗe, sai
dai harkokin kasuwanci ba sa tafiya kamar yadda aka saba gani, abin da ya wasu
‘yan kasuwa suka gwammace su yi zamansu a gida.
Kungiyar Kwagado ta NLC dai ta ce a yau Talata ma za ta ci gaba
da gudanar da gangami kamar yadda ta fara a jiya don nuna wa duniya gallaza wa
ma’aikata da take zargin gwamnatin jihar ƙarƙashin Nasir El-Rufai da aikatawa
ta hanyar sallamar dubban ma’aikata ba tare da biyan haƙƙoƙinsu ba.
Sai dai a
wata sanarwa da ta fitar da yammacin jiya, gwamnatin Kaduna ta yi alla-wadai da
zanga-zangar da kuma yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadagon ke yi.
Sanarwar da mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin watsa
labarai Mr Muyiwa Adekeye ya sanya wa hannu, ta ce irin munanan kalamai da
‘yan ƙwadagon ke danganta su da gwamnatin jihar ba za su canza komai ba.
Sanarwar ta kuma yi zargin cewa duk da irin yunƙurin da ‘yan
ƙungiyar NLC suka yi na neman hana wasu ma’aikata shiga sakatariyar gwamnatin
jihar don gudanar da ayyukansu, haƙarsu ba ta cimma ruwa ba.
Gwamnatin ta kuma zargi ƙungiyar da rufe asibitocin gwamnati da
dama a faɗin jihar tare da korar majinyata da suka je don neman magani, ba ya ga
uwa uba datse hanyoyin samar da wutar lantarki, abin da ta ce alama ce ta nuna
tsabar rashin imani- Kuma a cewar gwamnatin, tana nan tana tattara bayanai kan
irin waɗannan ayyuka da suka saɓa wa ka’ida.
Ita dai gwamnatin Kaduna a sanarwar da ta fitar ta buƙaci
al’ummomin jihar su ƙara haƙuri kan mawuyacin halin da suka shiga, inda ta ce
zanga-zangar ta 'yan ƙwadago wata manuniya ce ƙarara kan yunƙurin yi mata zagon
ƙasa.
A ɓangare guda kuma rundunar
‘yan sandan ƙasar ta ce ta tura ƙarin jami’an tsaro da kayan aiki zuwa babban
titin Kaduna zuwa Abuja, wanda ya yi ƙaurin suna kan satar mutane don neman kuɗin
fansa bisa tsammanin samun ƙaruwar ababen hawa saboda rufe filin jirgin sama da
tashar jirgin ƙasa a Kaduna, jihar da ke haɗa mafi yawan yankin arewacin ƙasar
da kudanci.