Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Buhari zai karɓo bashin fiye da tiriliyan biyu

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da sauran ƙasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur and Umar Mikail

  1. Sai da safenku

    Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi. Mu haɗu da ku gobe idan Allah ya kai mu domin kawo wasu labaran kai-tsaye.

    Umar Mikail ne ke muku fatan alheri.

  2. Rikici ya ƙazanta tsakanin Larabawan Isra'ila da 'yan sanda

    Rikici ya ɓarke tsakanin Falasdinawa da dakarun Isra'ila a yankin Bethlehem da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye.

    'Yan sanda sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye kan masu zanga-zangar da ke goyon bayan wani yajin aikin gamegari da Larabawan Isra'ila suka gudanar.

    Faɗa ya kuma barke a birnin Ƙudus, inda sojojin Isra'ila suka kama mutane da dama.

    An rufe ofisoshin gwamnati da makarantu. Haka ma a gabashin Kudus, an rufe wuraren kasuwancin Larabawa.

    Tun da farko, sojojin Isra'ila sun harbe wani ɗan Falasdinu bayan sun zarge shi da yunƙurin daɓa musu wuƙa a birnin Hebron.

  3. Najeriya ta dakatar da bayar da sabon fasfo

    Najeriya ta dakatar da bayar da sabon fasfo har sai an gama bai wa waɗanda suka nema nan da mako biyu masu zuwa.

    Yayin da yake yi wa 'yan jarida jawabi a Abuja ranar Talata, Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Immigration, Mohammed Babandede ya ce za a fara karɓar buƙatar yin sabon fasfon daga ranar 1 ga watan Yuni.

    Babandede ya ce sun ɗauki matakin ne biyo bayan umarnin da Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola ya bayar.

    "An dakatar da ayyukan bayar da sabon fasfo a ƙasa baki ɗaya har zuwa 1 ga watan Yunin 2021, lokacin da za a fara amfani da sabon tsarin fasfo," a cewarsa.

    "An yanke shawarar dakatarwar ce saboda a gama bai wa dukkan waɗanda suka nemi a ba su fasfo ɗin tun daga 17 ga watan Mayu."

    Ya ce an rufe baki ɗayan hanyoyin biyan kuɗi har zuwa 1 ga Yuni, sannan za a tura tawaga ta musamman domin kammala aikin.

  4. 'Yan bindiga sun kori mutum 10,000 daga gidajensu cikin kwana biyu a Nijar

    Mutum fiye da 10,000 ne suka tsere daga muhallansu a yammacin Jamhuriyar Nijar cikin kwana biyu da suka wuce sakamakon hare-haren 'yan bindiga, a cewar wani rahoton hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).

    Rahoton wanda hukumar kula da ayyukan agaji ta United Nations Office for the Coordination of Humanitarian Affairs (OCHA) ta fitar a Yamai ranar Litinin, ya ruwaito bayanan da mazauna Anzourou suka bayar bayan sun tsere da kuma shugabannin yankin.

    "Mutum 11,000 (iyalai 1,634) sun nemi mafaka a garin Tilaberi daga 14 zuwa 15 ga watan Mayun 2021", kamar yadda kamfanin labarai na AFP ya ruwaito.

    A cewar hukumar, mutanen na ci gaba da yin gudun hijirar, yayin da kaɗan daga cikinsu ke nufar Yamai, babban birnin ƙasar.

    Wani jami'in gwamnatin Anzourou, inda 'yan bindiga ke yawan kai hari, ya faɗa wa AFP cewa tuni fiye da mutum 10,000 suka gudu daga yankin cikin kwana biyu.

    Ya ƙara da cewa wasu mazauna ƙauyen da dama suna kan hanyarsu ta barin garin.

    OCHA ta ce 'yan gudun hijirar sun fito ne daga ƙauye huɗu daga cikin 24 na yankin Anzourou da ke cikin yankin Tilaberi mai fama da hare-haren 'yan bindigar a yammacin Nijar.

  5. Shugaban Faransa na so a kyautata hanyoyin bai wa ƙasashen Afirka tallafi

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kiran kawo babban sauyi game da yadda ake bai wa ƙasashen Afirka tallafin kuɗi.

    Macron na magana ne yayin wani taro da shugabannin Afirka ke halarta a babban birnin Faransa, Paris tare da manyan cibiyoyin kuɗi na duniya.

    Mahalarta taron na duba hanyoyin kauce wa lahanin da annobar korona ta yi wa tattalin arzikin ƙasashensu.

    Bankin Raya Afirka ya yi hasashen cewa miliyoyin mutane za su faɗa matakin ƙarshe na talauci a shekarar nan, yayin da ƙasashe da yawa a Afirka ke fama da bashi saboda annobar.

    Mista Macron ya alaƙanta matsalar tattalin arzikin da kuma hare-haren 'yan bindiga masu iƙirarin jihadi sannan ya nemi a yi wa dokokin da ke tsara harkar kuɗaɗe kwaskwarima.

  6. Gwamnonin APC sun shawarci El-Rufai ya sasanta da ƙungiyar ƙwadago

    Gwamnonin jam'iyyar APC mai muliki a Najeriya sun shawarci Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna da ya koma kan teburin tattaiunawa da ƙungiyar ƙwadago domin kawo ƙarshen yajin ma'aikata a jihar.

    Gwamnan Kebbi Abubakar Bagudu wanda shi ne shugaban ƙungiyar Progressive Governors Forum (PGF), shi ne ya yi kiran yana mai gargaɗin kar yajin aikin ya gurgunta tattalin arziƙin jihar.

    "[Ƙungiyar] PGF na sane kuma ta damu da abubuwan da ke faruwa tsakanin ƙungiyar ƙwadago ta NLC da gwamnatin Kadiuna game da rage yawan ma'aikatan ƙananan hukumomi," a cewar Gwamna Bagudu cikin wata sanarwar a yau Talata.

    "Ganin irin ƙalubalen da ke gaban jihohinmu, musamman yadda kuɗin shiga ya yi ƙaranci, muna roƙon 'yan Najeriya har da NLC da su tattauna da gwamnatoci a kowane mataki domin kawo ƙarshen matsalar.

    "A matsayinmu na gwamnonin APC, muna goyon bayan gwamnatin Kaduna wajen gyara tsarin ma'aikatan ƙananan hukumomi domin su yi aiki yadda ya kamata.

    "A loƙaci guda kuma, muna kira ga gwamnatin Kaduna ƙarƙashin shugabancin abokin aikinmu, Malam Nasir El-Rufai, ya bi duk hanyoyin da suka kamata wajen sasanta rikicin bisa masalahar 'yan Kaduna.".

    A ranar Litinin ne ƙungiyar ta shiga yajin gargaɗi na kwana biyar game da korar ma'aikata 7,000 da Gwamna El-Rufai na APC ya yi.

  7. An gano wani kauye a ƙarƙashin tafki

    An gano wani ƙauye a ƙarƙashin wani tafki a lokacin da ake aikin wani gyara a Italiya.

    Sai dai da ruwan tafkin ya janye ma ɗan wani lokaci, mazauna yankin sun ga ragowar wani ƙauye da ya taɓa zama muhallin ɗaruruwan mutane kafin a cika shi da ruwa don ginin madatsar ruwa a 1950.

    Tafkin Resia na Kudancin Tyrol a yankin Alpine da ke da iyaka da Austria da Switzerland.

    Hotunan da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna bene da bangwaye.

    A 1950 da hukumomi suka yanke shawarar gina madatsar ruwan a ƙauyen Curon, mazauna yankin sun nuna rashin jin daɗnsu.

    Sama da gidaje 160 ne suka nutse kuma al'umar Curon suka rabu da muhallansu, amma wasu sun koma wani sabon ƙauyen da aka gina a kusa da nan.

  8. Buhari zai karɓo bashin naira tiriliyan biyu

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na son ya sake ranto dala biliyan 6.1 daga ƙungiyoyin ƙasar waje domin cike giɓin kasafin kuɗi na 2021.

    Jumillar kuɗin a naira sun kai tiriliyan N2.343 - kan canjin N379 a kowace dala.

    Cikin wata wasiƙa da ya aike wa majalisun tarayyar ƙasar a yau Talata, Buhari ya nemi amincewarsu domin karɓo wani sabon bashin.

    Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Idris Wase, shi ne ya karanta wasiƙar a zauren majalisar, yayin da Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya karanta a tasu majalisar.

    Kasafin kuɗin na 2021 ya nuna cewa za a samu giɓin naira tiriliyan biyar daga cikin jumillar tiriliyan 13.6.

  9. 'A dakatar da zuba jari wajen samar da makamashi daga tsirrai'

    Hukumar sarrafa makamashi ta duniya wadda ke wakiltar akasarin kasashe masu arziki ta buƙaci a kawo ƙarshen zuba hannun jari wajen samar da makamashi daga tsirrai.

    A cewar wakilin BBC, hukumar ta ce tsare-tsaren gwamnatoci na baya-bayan nan domin rage fitar da hayaƙi ba su wadatar ba wajen hana fitar da hayaƙi mai gurɓata muhalli nan da shekarar 2050.

    Hukumar ta ƙara da cewa abin da ake buƙata shi ne sauya tsarin makamashin duniya baki ɗaya tare da zuba jari mai gwaɓi a harkar wanda, a cewar hukumar, zai taimaka wajen samar da miliyoyin ayyukan yi.

  10. Majalisar Dattawa ta umarci JAMB ta dakatar da amfani da NIN wajen rajista

    Majalisar Dattawan Najeriya ta umarci Ma'aikatar Ilimi da hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta Joint Admission and Matriculation Board (JAMB) da su sake duba shirinsu na amfani da lambar ɗan ƙasa ta National Identity Number (NIN).

    'Yan majalisar sun ba su umarnin ne a yau Talata domin ƙara wa'adin rajistar jarrabawar ko kuma soke shirin haɗa rajistar da kuma NIN ga ɗalibai har sai an samar da wani tsari cikakke na samun lambar ta ɗan ƙasa.

    Kazalika, ƙudirin ya ƙunshi umarni ga Ma'aikatar Ilimi da hukumar samar da NIN ta National Identity Management Commission (NIMC) da su samar da wani tsari mai sauƙi da zai bai wa ɗaliban samun lambar ta NIN a makarantunsu.

    A 'yan kwanakin nan ne JAMB ta mayar da NIN wajibi ga duk ɗalibin da ke son shiga jami'a a ƙasar.

    Sanata Ifeanyi Ubah daga Jihar Anambra wanda ya gabatar da ƙudirin, ya ce matakin na JAMB "rashin tausayi ne kuma ya yi wuri".

    Ƙudirin ya bayyana cewa shirin na JAMB ya saka ɗaliban Najeriya masu son shiga jami'o'i cikin tasku.

    Wasu iyayen ɗaliban sun faɗa wa BBC yadda shirin ke wahalar da su da yaran nasu sakamakon rashin sauƙi wajen shigar da lambar NIN ɗin yayin rajistar jarrabawar.

  11. Isra'ila ta sake rufe wata hanyar shiga Zirin Gaza

    Isra'ila ta sake rufe wata babbar hanya da ta tsallaka zuwa Zirin Gaza bayan kungiyar Hamas ta kai wasu hare-haren roka a Kudancin Isra'ila.

    Wasu ma'aikata yan Thailand biyu sun mutu sannan yan Isra'ila 10 sun jikkata kusa da wata babbar hanyar ta daban da aka sake buɗewa yan sa'oi da suka gabata.

    A iyakar Gaza da Masar, manyan motocon dakon mai 15 sun tsallaka zuwa yankin da akasarinsa ya kasance ba hasken wutar lantarki.

    Wasu manyan motocin kuma dauke da kayan abinci da tan 65 na magunguna sun samu wucewa ta birnin Rafah.

    A wani ɓangaren, Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya ce ƙasarsa na kokarin ganin kawo karshen tashin hankalin da ake tsakanin Palasɗinawa da Isra'ila.

    Da yake magana a Iceland, Blinken ya ce wani jakadan Amurka Hady Amr yana tubutbar shugabannin Isra'ila da shugaban Palasdinu Mahmnoud Abbas.

    A birnin Paris kuma, Shugabannin Faransa da Masar za su gana domin tattauna hanyoyin da za su taimaka wajen ganin an tsagaita wutar rikicin.

    Sarkin Jordan ma zai halarci taron da za su yi amma ta intanet.

  12. Ana ci gaba da ce-ce ku-ce kan haramta kiwon yawo a Najeriya

    A Najeriya, ana ci gaba da mai da martani game da matsayin da kungiyar gwamnonin PDP ta dauka cewar tana goyon bayan a haramta kiwon yawo a kasar.

    Kungiyar gwamnonin ta ce ta wannan hanyar ne kawai za a cimma maslaha tsakanin makiyaya da manoma.

    Amma kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah, wato MACBAN ta ce babu wanda ya tuntube ta, duk kuwa da cewa lamarin ya shafi rayuwar `ya`yanta.

    Kungiyar gwamnonin PDP ta yanke shawarar goyon bayan haramta al`adar kiwon yawo ne a taron da ta yi jiya a birnin Badun na jihar Oyo, inda ta ce ta amince da matsayin da wasu masu irin wannan ra`ayin suka dauka tun da farko, kuma babu abin da ya fi kafa rugage na zamani al`ala.

    Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, shugaban kungiyar Gwamnonin ya ce "taron na goyon bayan matsayin da kungiyar gwamnonin Najeriya da ta gwamnonin arewacin kasar da kuma kungiyar gwamnonin kudancin kasar suka dauka na rungumar tsarin kiwo na rugage a matsayin sahihiyar hanyar magance rikicin makiyaya da manoma a Najeriya."

    Ita kuwa kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN cewa ta yi ita ma da wai-wai take jin wannan matsayi na gwamnonin PDP.

    Kuma a cewar shugaban kungiyar na kasa, Muhammad Kiruwa Ardon Zuru ba su da ta cewa sai dai zuba wa ikon Allah ido.

    Makiyaya da dama dai na kallon wannan matsayi na gwamnonin PDP a matsayin furuci na siyasa kawai, ko kuma yaudara ta fi yawa a ciki, saboda wasu daidaiku daga cikin makiyayan sun shaida wa BBC cewa suna zargin cewa wasu gwamnatocin wasu daga cikin jihohin da ke wannan maganar sun sha nuna cewa ba za su amince da kafa rugagen ma a yankunansu ba.

    Taron gwamnonin na PDP ya tabo wasu batutuwa da dama ciki har da maganar kara wa jihohi iko ta yadda za su fuskanci kalubalen tsaro.

    Kazalika kungiyar ta bukaci shugaba Buhari da ya shirya taron majalisar kula da harkar `yan sanda, wadda ta kunshi dukkan gwamnonin kasar da sauran jiga-jigai don sama wa Najeriya mafita.

    Sai kuma maganar garambawul ga dokar zabe, inda kungiyar gwamnonin ta PDP ta ce ya kamata `yan majalisar dokokin Najeriya su hanzarta zartar da ita domin a kamanta adalci a zabukan da ke tafe, tana jaddada muhimmancin amfani da na`ura wajen tantance masu zabe da tattarawa da sanar da sakamakon zabe tun daga rumfunan da aka kada kuri`a.

  13. Ƴan sanda sun sa hayaƙi mai sa hawaye a zanga-zangar Kaduna

    Rahotanni na cewa 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen raba wata arangamar da aka yi tsakanin 'yan kungiyoyin kwadago da ke zanga-zanga da wasu matasan da ke goyon bayan gwamnati da suka so tarwatsa zanga-zangar.

    Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnan jihar Nasir Elrufa'i ya wallafa wani sako a shafinsa na Twitter inda ya ayyana shugaban kungiyar kwadagon kasar Ayuba Wabba a zaman wanda ake nema ruwan jallo tare da cewa akwai lada mai tsoka ga duk wanda ya kamo shi.

    Sai dai kamar yadda za ku ji a cikin wannan hirar da Haruna Shehu Tangaza ya yi da Comrade Nasir Kabir sakataren tsare-tsare na Kungiyar ta NLC hakan bai hana su ci gaba da zanga-zangarsu ba:

  14. Shugaba Macron na karɓar baƙuncin shugabannin Afirika a Paris

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron na karɓar baƙuncin taron shugabannin Afirka da shugabannin cibiyoyin hada-hadar kuɗi na duniya da nufin samar da kuɗaɗe don magance illar da annobar korona ta yi wa tattalin arziki.

    Dokokin kulle da rashin bukatar kayayyaki da kuma rashin tafiye-tafiyen yawon buɗe ido sun yi tasiri sosai a Afirka.

    Galibin ƙasashe da suka samu habakar tattalin arziki na fuskantar ƙarancin kuɗaɗe.

    Wasu cibiyoyin hada-hadar kuɗi sun dakatar da biyan kuɗin ruwa amma ana ci gaba da kiraye-kiraye na neman a yi rangwami kan rancen kuɗi a nan gaba.

  15. Malami ya ce Najeriya ta amshi £4.2m cikin kuɗin da Ibori ya sata

    Antoni-Janar kuma Ministan Shari'a a Najeriya, Abubakar Malami, SAN ya tabbatar da cewa gwamnatin taryya ta amshi Pan 4,214,017.66 na kuɗin da tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori ya sata.

    Mai taimaka wa ministan kan yaɗa labarai, Dokta Umar Jibril Gwandu ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

    A cewar sanarwar, an aika kwatankwacin kuɗin a Naira zuwa asusun gwamnatin tarayya ranar 10 ga watan Mayun 2021.

    Dama dai Abubakar Malamin ya sa hannu kan wata yarjejeniyar dawo da kuɗina amadadin gwamnatin Tarayya.

    Malami ya ce wannan matakin na nuna cewa Najeriya na da mutunci a idon duniya kan yadda ta ke amfani da kuɗinta da aka sata wanda ake dawo mata da su, wajen samar da abubuwan more rayuwa ga ƴan ƙasarta.

  16. An kama ɗan siyasar Najeriya da zamba a Amurka

    An kama wani ɗan siyasar Najeriya kan laifukan zamba a Amurka ta hanyar satar bayanan mutane sama da 100.

    An kama Abidemi Rufai, mai taimaka wa Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, ranar Juma'ar da ta gabata ne kuma ana zarginsa da satar sama da $350,000 a kuɗaɗen rage raɗaɗin talauci daga Ma'aikatar Ayyukan Yi ta jihar Washington, a cewar sanarwar Ma'aikatar shari'ar Amurka.

    Ana sa ran zai gurfana a gaban kotu ranar Laraba.

    Gwamnatin jihar Ogun ta dakatar da Abidemi Rufai daga muƙamin nasa.

    Ana zargin Mista Rufai, mai shekaru 42 da satar bayanan mazauna Washington 100 tsakanin watan Maris zuwa Agustan shekarar 2020.

    Hukumomin Amurka sun ce an aika sama da $288,000 wani asusun bankinsa.

    Ma'aikatar shari'ar ta ce Mista Rufai ya yi amfani da adireshin email guda ta hanyar da matakan tsaron da aka sa a na'urori yadda ba za su gane ba.

    Baya ga jihar Washington, Rufai ya yi irin wannan a Hawaii da Wyoming da Massachusetts da Monatan da New York da Pennsylvania.

    Yana fuskantar shekaru 30 a gidan yari .

  17. Hukumar Hisbah ta kama mata da miji da jaririn sata a Kano

    Hukumar Hisba a jihar Kano ta ce ta kama wata mata, Salomi Jerome da mijinta Igina Salomi da ake zargi da safarar wani jariri daga jihar Delta zuwa Kano, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Shugaban hukumar Dokta Harun Ibn-Sina ya tabbatar da kama mutanen a wata sanarwa ranar Talata a Kano.

    Daily Trust ta ce Ibn-Sina ya ce ma'aikatan hukumar da ke aiki a tashoshin mota ne suka kama mutanen ranar Litinin.

    Sanarwar ta ce kafin matar ta amsa laifin zarginta da ake yi, Salome ta ce ita ta haifi jaririn.

    "Daga baya ne suka bayyana cewa sun sayi jaririn ne daga wata malamar asibiti a Delta kan Naira 900,000," a cewarsa.

    Shugaban ya ce an mika mutanen ga hedikwatar ƴan sanda ta jihar Kano inda za a zurfafa bincike.

    Ibn-Sina ya bai wa iyaye shawara su ƙara sa ido kan yaransu don gujewa irin waɗannan sace-sacen.

  18. Rahoto kan kudurin kafa asusun musamman da zai taimaka wa inganta harkar tsaro

    Wani kwamitin tsaro na majalisar wakilan Najeriya ya yi wani zama na sauraron ra'ayin jama'a dangane da wani kuduri na kafa asusu na musamman da zai taimaka wajen inganta harkar tsaro a kasar.

    'Yan majalisar sun bayyana cewa sojin kasar na bukatar kudi sosai don shawo kan kalubalen da Najeriya ke fuskanta ta fuskar tsaro, kuma kafa asusun ya zama wajibi saboda a rage dogaron sojin ga iya abin da ake kebe musu a cikin kasafin kudi na shekara-shekara.

    Honarabul Shehu Koko shi ne shugaban kwamitin majalisar wakilan a kan harkokin sojin sama, ga kuma karin bayanin da ya yi wa Ibrahim Isa:

  19. NITDA ta shawarci ƴan Najeriya kan sabbin ƙa'idojin amfani da Whatsapp

    Hukumar NITDA a Najeriya ta shawarci ƴan Najeriya kan yadda za su guje wa shiga tarkon mulkin-mallaka ta intanet.

    Shawara dai na cikin wata sanarwa da babbar jami'a mai kula da hulɗa da walwalar jama'a ta hukumar, Mrs Hadiza Umar ta fitar ranar Litinin kan sabbin dokokin manhajar Whatsapp.

    Sanarwar ta ce ta na ba ƴan Najeriya shawarar duba sabbin ƙa'idoji da tsare sirrin masu amfani da manhajar wanda suka fara aiki ranar 15 ga watan Mayun 2021.

    Sanarwar ta ce "Miliyoyin ƴan Najeriya na amfani da Whatsapp saboda kasuwanci ko sada zumunta da sauran abubuwa."

    "Don fahimtar yadda abin ke aiki, NITDA ta haɗa kai dai Hukumomin da ke kare bayanan sirri na Afrika don tattaunawa sa Facebook, kamfanin da ke da Whatsapp."

    NITDA ta shaida wa ƴan Najeriya cewa suna da ƴancin ɗaukar matakin bai wa Whatsapp damar amfani da bayanansu amma ta ba su shawarar taƙaita bayar da bayanansu na sirri a shafukan sada zumunta.

  20. Spaniya ta aika dakaru iyakar Moroko don hana 'yan ci rani kwarara kasarta

    Spaniya ta aike dakaru kan iyakarta da Arewacin Afirka domin hana tururuwar 'yan ci rani da ke shiga kasar daga Moroko.

    A ranar Litinin kawai mutum 5,000 ne suka shiga Spaniya. Masu gadin kan iyaka na Moroko ba su yi wani katabus ba wajen hana su.

    Majiyoyin 'yan sanda sun ce akwai yiwuwar yawan masu shigar ya karu.

    Jami'an Spaniya sun zargi Moroko da amfani da 'yan ci rani wajen bata suna.

    Huldar diflomasiyya na kara yin tsami bayan da aka bar jagoran Polisario Front ya shiga Spnaiya don a yi masa maganin cutar korona.

    Polisario yana fada da Moroko kan neman yin iko da yankin Western Sahara.

    Moroko ta yi watsi da cewa akwai alaka tsakanin kwararar 'yan ci rani da Polisario.