Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 200 a Gaza zuwa yanzu

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur and Umar Mikail

  1. Yadda ƴan ƙungiyar ƙwadago ke gudanar da zanga-zanga a Kaduna

    Ma’aikata sun fara cincirindo a ofishin NLC domin zanga-zangar korar ma’ikata a jihar Kaduna.

    NLC Strike
    NLC Strike
    NLC Strike
    NLC Strike
  2. Sojojin Najeriya sun 'kashe mayaƙan Boko Haram 40' a Borno

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe mayaƙan Boko Haram a kalla 40 bayan da suka sa abun fashewa a wani taron ƴan ƙungiyar a kauyen Dawuri a ƙaramar hukumar Konduga a jihar Borno.

    Wata majiyar rundunar ta ce an kai harin ne bayan da ta samu bayan sirri kan cewa Boko Haram na shirin kai hari a Miaduguri babban birnin jihar.

    Shugaba Muhammadu Buhari na fuskantar matsin lamba a lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙaruwar matsalar tsaro a faɗin ƙasar.

    Jami'an tsaron Najeriya na ƙoƙarin shawo kan matsalolin ayyukan masu iƙirarin jihadi da ,masu garkuwa da mutane don kuɗin fansa da ɓarayin daji da ƴan aware.

    Nigerian Army

    Asalin hoton, Nigerian Army

  3. Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila ta ƙaddamar da gwamman hare-hare ta sama a Zirin Gaza ranar Litinin, bayan da ƴan bindigar Falaɗinu suka harba rokoki a biranen kudancin Isra'ilar.

    Hare-haren da aka kai cikin dare a Gaza na cikin mafiya muni tun da aka fara rikicin mako ɗaya da ya gabata.

    Isra'ila ta ce ta kai harin ne a gine-ginen ƴan Hamas amma an lalata tituna da layukan wutar lantarki.

    kasashen duniya na ci gaba da kira da a tsagaita wuta.

    Kwamiitn tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi ganawar gaggawa ranar Lahadi kuma Sakatare-Janar António Guterres ya yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da faɗan yankin na iya fuskantar matsalolin agaji.

    Ya yi kira da gaggauta kawo ƙarshen tashin hankalin.

    Amma babu alamar hakan zai yiwu yayin da aka shiga mako na biyu a rikicin.

    An fara rikicin ne bayan kwashe makonni ana rashin jituwa tsakanin Isra'ila da Falasɗin a yankin Gabashin Birnin Ƙudus da aka ƙwacewa Falaɗinawa.

    Wannan ya janyo karawa a masallacin da Musulmi da Yahudawa ke girmamawa.

    Ƴan ƙungiyar Hamas, wadda ke da iko da Gaza sun fara harba rokoki bayan yi wa Isra'ila gargaɗi cewa ta janye daga masallacin, kuma wannan ya haifar da hare-haren sama don nuna ramuwa.

  4. Man fetur na daf da ƙarewa a Zirin Gaza

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa man fetur a zirin na Gaza na gab da karewa, abun da ke yin barazana ga ayyukan yau da kullun.

    Wata jami'ar Majalisar Dinkin Duniya a Gabas ta Tsakiya Lynn Hastings, ta shaida wa BBC cewa an katse ko lalata layukan wutar lantarki yayin rikicin.

    Bugu da kari, ta ce aikin kai man fetur da Majalisar Dinkin Duniya ke yi zuwa wasu sassa da ke bukatar taimako sun tsaya cik a yankin a makon da ya gabata.

    Ta yi gargadin cewa asibitoci za su tsaya cik, kana za a fada halin rashin ruwa da matsalar muhalli a Gaza matsawar ba a kai dauki ba.

  5. Ficewar Amurka daga Afghanistan zai jawo ƙaruwar tashin hankali

    Babban kwamandan Amurka a Afghanistan ya shaida wa BBC cewa yana sa ran tashin hankali zai karu, yayin da Amurka da kawayenta na NATO ke ci gaba da ficewa.

    A wata hira da ba kasafai ake yi ba a sansanin NATO da ke arewacin Afghanistan, Janar Scott Miller ya yaba da karfin sojojin Afghanistan.

    Ya ce ana sa ran dakarun Amurkar za su kammala ficewa daga kasar a watan Satumba, shekaru ashirin bayan shigarsu.

  6. An kashe fararen hula 12 a Sudan ta Kudu

    Sudan ta Kudu

    Asalin hoton, AFP

    Mahukunta a Sudan ta Kudu sun ba da rahoton cewa mayakan wata kungiya sun kashe fararen hula goma sha biyu a yankin Abyei mai arzikin man fetur.

    Cikin wata sanarwa a hukumance, Sudan ta Kudu ta zargi makwabciyarta Sudan da taimaka wa mayakan sa-kai na Mis-seriya a harin da aka kai jiya Lahadi.

    Gwamnatin Sudan ba ta ce komai a kan zargin ba.

    Kasashen biyu sun jima suna ikirarin mallakar yankin na Abyei, baya ga tashin hankali da dama da wajen ya sha fama da shi.

  7. Indiya na dakon isar gagarumar guguwa

    Ana sa ran dubbban mazauna yankunan da ke kusa da gabar tekun yammacin Indiya za su fice daga gidajensu yayin da guguwar farko ta bazara ke ci gaba da kusanto su.

    Tuni guguwar mai suna Taukte ta fara haifar da ruwan sama kamar da bakin kwarya da iska mai karfi a jihohin Karnataka, da Kerala da Goa.

    Mutane 6 sun mutu kawo yanzu.

    Ana sa ran guguwar za ta kada zuwa garin Gujarat a ranar Talata.

  8. Maraba

    Barkanku da safiyar Litinin.

    Marabanku da shigowa wannan shafin, wanda ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta kamar Nijar da Chadi da Ghana da Kamaru da ma wasu ƙasashen ƙetare.

    Gahawa