Babu tabbas ko Iran na da kyakkyawar niyya kan tattaunawar nukiliya - Amurka

Asalin hoton, AFP
Sakataren harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya shaida wa BBC cewa ƙasarsa ba ta da tabbacin ko Iran da gaske take kan sake komawa yarjejeniyar nukiliyarta wanda hakan zai ba da damar dage mata takunkumai.
Wakilin BBC ya ce tattaunawa kan sake farfado da yarjejeniyar za ta kankama nan ba da jimawa ba a birnin Vienna.
Mr Blinken ya ce Amurka ta nuna bukatarta na sake dawo da yarjejeniyar nukiliyar.
Ya kuma ce Iran na gab da shiga wani mataki na kirkirar kayayyakin samar da makamin nukiliya a cikin ƴan watanni masu zuwa.

