Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An kashe wata 'yar bingida tare da kama mutum biyu a Sokoto

Wannan shafi ne da ke muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Babu tabbas ko Iran na da kyakkyawar niyya kan tattaunawar nukiliya - Amurka

    Sakataren harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya shaida wa BBC cewa ƙasarsa ba ta da tabbacin ko Iran da gaske take kan sake komawa yarjejeniyar nukiliyarta wanda hakan zai ba da damar dage mata takunkumai.

    Wakilin BBC ya ce tattaunawa kan sake farfado da yarjejeniyar za ta kankama nan ba da jimawa ba a birnin Vienna.

    Mr Blinken ya ce Amurka ta nuna bukatarta na sake dawo da yarjejeniyar nukiliyar.

    Ya kuma ce Iran na gab da shiga wani mataki na kirkirar kayayyakin samar da makamin nukiliya a cikin ƴan watanni masu zuwa.

  2. Cutar korona a Najeriya: Mutum biyu sun mutu, 52 sun kamu ranar Laraba

    Ƙarin mutum 52 sun kamu da cutar korona a Najeriya ranar Laraba tare da mutuwar mutum biyu, a cewar hukumar yaƙi da yaɗuwar cutuka ta ƙasar, NCDC.

    Bisa alƙaluman da ta wallafa, sabbin kamuwar sun fito ne daga jihohi bakwai na ƙasar har da Abuja.

    Jihohin su ne: Taraba (18), Abuja (9), Rivers (9), Legas (7), Akwa Ibom (6), Kano (2), Kaduna (1).

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 165,273 ne suka kamu da cutar a Najeriya, 2,065 sun mutu da kuma 155,403 da aka sallama bayan sun warke.

  3. Barka da hantsi

    Maraba da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa. Umar Mikail ne zai ja ragamar shafin a yanzu.

    Ku biyo mu don sanin abubuwan da ke faruwa a duniya, musamman a Najeriya da Nijar da Kamaru da Ghana da Chadi.