Rufewa
Nan muka kawo karshen labarai da rahotannin namu na wannan rana.
Buhari Muhammad Fagge ke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Umar Mikail
Nan muka kawo karshen labarai da rahotannin namu na wannan rana.
Buhari Muhammad Fagge ke cewa mu kwana lafiya.
Jami'ai a Afghanistan sun ce mayakan Taliban sun karbe iko da madatsar ruwa ta biyu ma fi girma a kasar, bayan shafe watanni ana gwabza fada a kudancin yankin Kandahar.
Madatsar ruwa ta Dahla Dam ita ke bai wa manoman rani ruwan da suke ban ruwa, sannan mutanen yankin Kandahar sun dogara da ruwan don amfanin yau da kullum.
Shekaru 70 da suka wuce Amurka ta gina madatsar ruwan, a shekarar 2019 kumaka kara fadadata.
A bangare guda kuma wasu 'yan bindiga da ba asan ko su waye ba sun harbe wani jami'in gwamnati a birnin na Kandahar.
Mr Nemat Rawan fitaccen dan jarida ne, da ya samu aiki da ma'aikatar kudi da ke kasar makonni uku da suka gabata.
Ya zuwa an yi wa sama da mutum miliyan 10 rigakafin korona a cibiyoyi 587 da ake da su a Saudiyya, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta kasar ta bayyana.
An tanadi duka abubuwan da ake bukata a cibiyoyin domin gudanar da wannan aiki, ana kuma samun hadin kai daga mutanen kasar domin tabbatar da dokokin da aka shimfida na kare kai daga wannan cuta.
Sanarwar da ma'aikatar lafiya ta kasar ta fitar ta ce wurare masu zaman kansu sun rika sanya wa ana yi wa mutane rigakafin kyauta a matsayin gudunmuwarsu.
An kuma samar da manhajar Sehatty wadda za ta bai wa 'yan kasar damar samun cibiyar da ake yin allurar a kusa.
Akalla mutum 25 ne suka mutu ciki har da wani jami'in tsaro a wani harbe-harben bindiga da aka yi a birnin Rio de de Janeiro, na Brazil.
'Yan sanda sun je wani yanki kusa da Re de de Janeiro suna bincike kan wasu miyagun kwayoyi, lokacin da fada ya barke tsakanin 'yan sanda da dilolin kwayar.
An shaida wa 'yan sanda cewa dilolin kwayar suna daukar hayar yara kanana wajen gudanar da ayyukansu.
An harbi wasu fasinjojin mota biyu da suke kan hanyarsu, sai dai babu wanda ya mutu a cikinsu.
Rio de Janeiro na daya daga cikin birane da ake samun tashin hankali a Brazil.
Wasu 'yan bindiga suk kai hari wani ofishin 'yan sanda a Obosi da ke Karamar Hukumar Idemili ta arewa a jihar Anambra da ke kudancin Najeriya.
Yan bindigar sun kona ofishin tare da kashe mutum biyu.
Kwamishinan 'yan sanda na jihar Chris Owolabi ya ce komai ya koma yadda yake a Obosi kuma suna ci gaba da neman 'yan bingidar.
Kuma ya bai wa ma'aikatansa umarnin a duba duk wani lungu da sako domin nemo masu laifin.
Babu dai wanda ya san ya aka yi 'yan bindigar suka afkawa wannan ofishi sai dai ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
An kashe wasu da ake zargin 'yan bindiga ne su uku ciki har da mace daya bayan wani hari da suka yi kokarin kai wa kan wasu Fulani a Karamar Hukumar Goronyo da ke jihar Sokoto a arewacin Najeriya.
A ranar Laraba ne wasu fusatattun matasa suka farwa ofishin 'yan sintiri na yankin da aka tsare wadanda ake zargin.
'Yan bindigar sun je wata ruga ne da ke wajen Goronyo, da nufin su kada shanu cikin dare sai suka gamu da fushin mazauna yankin.
Wani mazaunin wurin ya ce suna jin labarin an kama mutanen suka dira ofishin 'yan sintirin kuma sauka samu nasarar cin musu.
"Daya daga cikin wadanda ake zargi ya mutu yayin da wata mace da kuma wani suka yi yunkurin tserewa ta taga," in ji majiyar.
Mai shigar da kara a Qatar ya ba da umarnin cafke ministan kudin kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar ya rawaito cewa ana tsare da Ali Sherif al-Emadi inda ake ma sa tambayoyi kan zargin amfani da mukaminsa ba bisa ka'ida ba, da almubazzaranci da dukiyar kasa, da kuma laifukan a ma'aikatun gwamnati.
Tun daga shekarar 2013 Mr al-Emadi ya ke rike da mukamin ministan kudi a Qatar, kafin wannan mukami ya taba rike babban darakta a babban bankin Qatar da ke birnin Doha.
A Najeriya kungiyar masu sarrafa shinkafa ta kasa ta koka kan wani mataki da kwamitin majalasar kasar mai kula da koken jama’a ya dauka.
Matakin dai shi ne na kira da hukumar hana fasa kwauri ta kasar da ta mayar wa wasu 'yan kasuwar birnin Ibadan na jahar Oyo shinkafar da aka shigo da ita cikin kasa ba bisa ka’ida ba da aka kwace.
A dai ranar Talatar da ta gabata ne a cewar kungiya ta RIPAN kwamitin majalasar ya nemi jami’an na hukuma hana fasa kwauri da su mayar wa ‘yan kasuwar da shinkafar da ake zargin an yi satar shigar da ita cikin kasa.
Somaliya ta sabunta alakar diflomasiyyarta da Kenya bayan ta warwareta a watan Disamba da ya gabata.
Ta rika zargin makociyarta ta da tsoma baki cikin harkokin siyasarta ta cikin gida gabanin babban zaben da aka dage daga baya.
Alaka tsakanin kasashen biyu na fuskantar tsaiko a lokuta da dama.
Sun ta samun matsala kan iyakar ruwa a tsakaninsu na tsawon shekaru, inda ko wanne bangare ke ikirarin mallaka.
Kenya na da dakarunta akalla 4,000 a kudancin Somaliya, a wani kokari da take yi na kare kanta daga maeu ikirarin jihadi.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce sabon shirin haɗa lambar ɗan ƙasa ta National Identification Number (NIN) da lambar waya zai tallafa wajen gano miyagu a ƙasar.
Saboda haka ne ya shawarci 'yan Najeriya da su shiga a dama da su a shirin, wanda ya ce zai taimaka wajen samar da bayanai na intanet da za su taiamaka wa tsaron ƙasa.
Shugaban na magana ne yayin ƙaddamar da shirin Revised National Identity Policy wato sabon tsarin samar da lambar ɗan ƙasa a fadarsa da ke Abuja.
"Lambar NIN za ta gyara wasu daga cikin matsalolinmu na tsaro," in ji shi. "Cikin sauƙi za mu san kowane mutum a Najeriya sannan ta taimaka wajen haɓaka tsaro.
"Lambar wata shaida ce ta ƙasa, ya kamata 'yan Najeriya da kuma waɗanda ke da izinin zama su same ta. Da ita mutum zai samu ayyukan gwamnati sannan ta taimaka mana wajen aiwatar da nagartattun ayyuka cikin ƙwarewa."
Yayin taron ne Ministan Sadarwa Isa Ali Pantami ya gabatar wa da Buhari da sauran manyan jami'an gwamnati sabon katin shaidarsu na ɗan ƙasa mai ɗauke da lambar ta NIN.
Ranar Litinin ne ministan ya ƙara wa'adin haɗa NIN da layukan wayar salula zuwa 30 ga watan Yuni.
Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa mutum miliyan 54 ne suka haɗa lambar tasu da layin waya, abin da ke nufin layin waya kimanin miliyan 200 na da rajista da lambar NIN, a cewar hukumar NCC.
Biyo bayan jerin hare-haren da suka yi sanadiyar mutuwar sojoji da dama da fararen hula a yankunan Tahoua da Tillabery na jamhuriyar Nijar, shugaba Mohamed Bazoum ya gayyaci shugaban rundunar Faransa da ake kira Operation Barkhane mai dakaru 4500.
Shugaban kasar ya nemi jin ta bakin shugaban rundunar game da ayyukansu ganin cewa kusan a kowace safiya ana samun hare hare daga kungiyoyin masu iƙirarin jihadi.
Sai dai a nasu bangare, al'ummar kasar na ganin cewa dakarun ba su da amfani kasancewar ba sa gyara komai.
Kafafen yaɗa labarai na ƙasar sun ruwaito ranar Talata cewa kusan sojoji 30 ne 'yan bindiga suka kashe a fafatawar da suka yi a yankin Tilaberi mai fama da rikice-rikice.
Gwamnatin sabon Shugaban Ƙasa Mohamed Bazoum ta fara ne da fuskantar hare-haren 'yan bindiga a yankunan da ke fama da rikici kamar Tillaberi da Tahoua da Diffa.
Daga yanzu shafin Twitter zai dinga matsa wa mutane su sake duba "kalaman zagi ko waɗanda da ba su dace ba" kafin su wallafa su a dandalin.
Dandalin sadarwar wanda ya sha fuskantar suka kan kalaman rashin kyautawa, ya fara gwada tsarin a shekarar da ta gabata.
Twitter ya ce sakamakon gwajin ya nuna raguwa a yawan kalaman zagi a dandalin.
A ranar Laraba ne kamfanin ya ce zai bai wa masu amfani da turancin Ingilishi damar fara amfani da shirin a kan wayoyin Apple da Android.
Twitter ya ce sun gano matsawar ta sa kashi 34 cikin 100 na mutune sun sauya saƙon da suka yi niyyar wallafawa ko kuma sun fasa turawa gaba ɗaya.
A cewarsa, masu amfani da shafin sun rage wallafa zage-zage ko cin zarafi da kashi 11 cikin 100 bayan an matsa musu a karon farko.
Kazalika, su ma ba lallai ne a zage su ba ko kuma yi musu kalaman ɓatanci.
Da ma shafin na amfani da shigen wannan shiri domin rage yaɗa labaran ƙarya, inda ake matsa wa mutum ya shiga adireshin wani labari da yake son yaɗawa ya karanta kafin ya sake yaɗa shi.
Indiya ta sake samun adadi mafi yawa na waɗanda cutar korona ta kashe a rana guda, inda mutum kusan 4,000 suka mutu cikin awa 24.
Ma'aikatar lafiyar ƙasar ta ce ƙarin mutum 3,980 ne suka mutu, jumillar adadinsu ya zama 230,168 a ranar Alhamis.
Kazalika, ƙarin mutum 412,262 sun kamu da cutar, wanda ya sa jumillarsu ya kai miliyan 21.1 a ƙasar.
Shugabannin tsaron Najeriya da na 'yan Majalisar Dattijan Najeriya na tattaunawar sirri.
Hafsoshin tsaron na amsa gayyatar 'yan majalisar ce domin bayyana musu halin da ake ciki game da taɓarɓarewar tsaro a faɗin ƙasar.
Babban Hafsan Tsaro, Manjo Janar Leo Irabor ne ya jagoranci hafsoshin tsaron zuwa majalisar, inda Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ya karɓe su.
Sauran jamia'n da ke amsa gayyatar sun haɗa da da shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA da kuma na 'yan sandan DSS.
Bayan Sanata Ahmad Lawan ya gode musu bisa ayyukan kare tsaron ƙasa a madadin majalisar sai suka shiga tattaunawar sirri da misalin ƙarfe 11:21.
Muna tafe da ƙarin bayani da zarar mun samu.
Biyo bayan rabuwar aure tsakanin Bill Gates da Melinda Gates, yanzu Melinda ta zama biloniya sakamakon kuɗin da ta karɓa daga hannun tsohon mijin nata, kamar yadda jaridar Forbes ta ruwaito.
Kamfanin Bill mai suna Cascade Investment ya bai wa Melinda kuɗi dala biliyan 1.8 a matsayin na tsaro ranar Litinin da ta wuce, wato ranar da ma'auratan suka sanar da rabuwarsu.
Duk da cewa babu tabbacin ko kuɗin wani ɓangare ne na abin da za ta samu daga mutuwar auren, haka ma babu tabbas ko sun yi wata yarjejeniya a baya game da ko zai ba ta wani abu yayin rabuwa ko kuma a'a.
Hakan ya sa Melinda ta zama biloniya da dala biliyan 1.8, wanda hakan ya jawo dukiyar Bill ta ragu zuwa dala biliyan 128.6 daga 130.4.
Sai dai har yanzu Bill Gates ne mafi arziki na huɗu a duniya, in ji Forbes.
An yi jana'izar Sarauniyar Zulu, Mantfombi Dlamini Zulu, a yankin KwaZulu-Natal na Afirka ta kudu.
A makon da ya gabata Sarauniya Dlamini ta yi mutuwar farat-ɗaya, wata guda bayan mutuwar mijinta, Sarki Goodwill Zwelithini.
Har yanzu dai ƴan uwanta ba su bayyana abin da ya yi ajalinta ba.
'Yan matan Zulu sun yi gawarta rakiya zuwa fadarta a jiya Laraba.
Ana sa ran sanar da mutumin da zai ci gaba da mulkin masarautar nan ba da jimawa ba.
Hukumar jarrabawar kammala sakandare a Najeriya ta NECO ta saki sakamakon jarrabawar na shekarar 2020.
Hukumar ta National Examination Council ta sanar da hakan ne a birnin Minna na Jihar Neja a yau Alhamis.
Rajistira kuma shugaban hukumar, Godswill Obioma, ya ce ɗalibai 41,459 ne suka yi rajistar rubuta jarrabawar, sai dai 39,503 daga cikinsu ne suka rubuta ta.
Ya ce an samu waɗanda suka aikata ba daidai ba guda 6,465 a 2020, ba kamar a 2019 ba inda aka samu 17,004.
Ya ƙara da cewa ɗalibai 26,277 sun samu kiredit biyar zuwa sama ciki har da Ingilishi da lissafi, yayin da 34,014 suka samu kiredit biyar ɗin ba tare da maudu'an guda biyu ba.
Shugaban wanda ya jaddada matsayar hukumar wajen ƙin amincewa da ayyukan rashin gaksiya, ya ce sun bi dukkan matakai da ƙa'idoji kafin sanar da sakamakon.
Dakarun sojan Najeriya sun yi nasarar kuɓutar da mutum 13 daga hannun 'yan fashin daji da suka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Wata sanarwa da ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar ta fitar a daren jiya Laraba ba ta bayyana lokacin da lamarin ya faru ba.
Mutanen a cewar Kwamishinan Tsaro Samuel Aruwan, sun je Bakin Kasuwa da ke Ƙaramar Hukumar Chikun domin yin aikatau a wata gona lokacin da 'yan bindigar suka kai musu harin.
Bayan samun bayanan sirri, sojojin sun bi sahun 'yan fashin cikin dajin da ke kusa da ƙauyen Bana, abin da ya kai ga ceto mutanen kenan.
A gefe guda kuma, 'yan bindigar sun kashe mutum biyu da aka bayyana da Ezekiel Iliya da Nasara Yohanna kafin zuwansu wurin, inda suka ƙona wata coci da kuma yashe kayayyaki daga wasu shaguna.
Kungiyar kwadago ta Najeriya ta gargadi gwamnatin tarayya da ta dakatar da yunkurin da take yi na rage albashin ma'aikata, tana mai cewa irin wannan mataki zai sa ma'aikata su shiga cikin wani hali na ha'u'la'i.
A ranar Talata ne minister kudi ta Najeriya Zainab Ahmed Shamsuna ta bayyana cewa gwamnati na nazari akan yadda za ta zaftare yawan kuɗaɗen da take kashewa ta hanyar rage albashin ma'aikata.
Rahotanni sun kuma ce ministar ta umarci hukumar albashin ma'aikata ta yi nazari akan albashi da yawan ma'aikatun gwamnati da ke kasar.
Sai dai shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Ayuba Wabba ya yi kira ga gwamnati a kan ka da ta zaftare albashin mafi kankanta na naira dubu talatin na ma'aikata, yana mai cewa albashin masu karbar albashi mai tsoka ne kawai ya kamata a rage musamman masu rike da mukaman siyasa.
"Abu ne da ba za a taɓa tsammani ba cewa gwamnati za ta yi niyya ta rage albashin ma'aikatan Najeriya a wannan lokacin''.