Kwamandan Hisbah ya yi bayani kan zargin kaɗaicewa da matar aure a Kano

Wannan shafi ne da ke muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Fauziyya Kabir Tukur

  1. Cutar korona na ci gaba da yaɗuwa a Latin Amurka

    Hukumar lafiya ta duniya WHO da ke Latin Amurka, ta ce cutar korona na ci gaba da yaduwa cikin sauri a yankin.

    Guatemala da Costa Rica na fuskantar karin masu kamuwa da cutar a tsakiyar yankin , ya yin da su ma yankunan Guyanas da Argentina da Colombia.

    Adadin wadanda ke kamuwa da cutar ya rubanya sau biyar idan aka kwatanta da irin wannan lokacin a bara.

    A banagre guda kuma yawan mace-mace sakamakon cutar a Brazil ya karu, kididdiga kuma ta nuna matasa da 'yan kasa da shekara 40 ne suke mutuwa.

    Cutar korona ta girgiza yankin latin Amurka, in da yawancin wadanda ke mutuwa sanadiyyar cutar a duniya suka fito daga yankin.

  2. Najeriya za ta fara aiki da fasahar 5G

    5G

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta sanar da ƙudirinta na fara amfani da fasahar 5G a ɓangaren sadarwa nan ba da jimawa ba.

    Shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya, NCC, Farfesa Umar Garba Dambatta ne ya sanar da haka a lokacin sa hannu kan wata yarjejejniya tsakanin hukumar tasa da Hukumar Tauraron Dan Adam ta ƙasar a Abuja ranar Laraba.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnati ta ce mutane su kwantar da hankalinsu kan duk wata jita-jita da suke ji dangane da fasahar 5G inda ta ce alfanun fasahar ba zai misaltu ba.

    Yarjejeniyar dai sharar fage ce kan samar da kayan aikin ƙaddamar da fasahar a ƙasar.

    Shugaban Hukumar NigComSat Dokta Abimbola Alale ya ce yarjejeniyar da hukumomin biyu suka sa wa hannu za ta sauya fagen sadarwa da harkokin intanet a Najeriya.

  3. An saki sauran ɗaliban kwalejin gandun daji da aka sace a Kaduna

    An saki sauran ɗaliban da aka sace na kwalejin Horar da Harkokin Noma da Gandun Daji ta gwamnatin tarayyya da ke Kaduna.

    Ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban ya tabbatar wa BBC cewa an saki ɗalibai 27.

    Ya ce suna kan hanyar karɓar ɗaliban.

    Shiekh Ahmad Abubakar babbam malamin addinin Islama da ke da'awar yin sulhu da ƴan bindiga ya shaida wa BBC cewa su shiga tsakani da aka saki ɗaliban.

    "Mu muka yi ƙoƙarin ganin an sake su tare da taimakon tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo," in ji Sheikh Gumi.

    Sai dai malamin bai bayyana cewa ko an biya kuɗin fansa ba kafin aka saki ɗaliban.

    Gwamnatin jihar Kaduna ba ta tabbatar da sakin ɗaliban ba kawo yanzu.

    Karanta ƙarin bayani a nan da nan.

  4. Ƴan gudun hijira na 'taimaka wa' mayaƙan Boko Haram wurin kai hari

    BH

    Asalin hoton, AFP

    Ana zargin ƴan gudun hijira a garin Ajiri na ƙaramar hukumar Mafa a jihar Borno da taimaka wa wasu da ake zargin ƴan Boko Haram ne wurin kai hari a garin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na PR Nigeria ya ruwaito.

    Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da motoci biyar tare da kashe ƴan sa kai 15 da farar hula 10 da sojoji 5 a harin da suka kai ranar Litinin.

    Garin Ajiri na da nisan kilomita 20 daga garin Dikwa na jihar Borno.

    Wasu majiyoyin soji sun bayyana cewa maharan sun yi ƙoƙarin shiga wani sansanin sojoji a yanki amma dakarun ba su ba su dama ba, inda suka yi musayar wuta da ƴan bindigar.

    PR Nigeria ta bayyana cewa garin Ajiri bai taba fuskantar harin ƴan bindiga ba sai da gwamnati ta tsugunar da wasu ƴan gudun hijira a garin.

    Bincike ya gano cewa wasu daga cikin ƴan gudun hijrar iyalan manyan kwamnadojin Boko Haram ne kuma suna ganawa da ƴaƴansu da a yanzu suka zama mayaƙan ƙungiyar da ke aiki a yankin Tafkin Chadi.

    Haka kuma, an gano cewa mayaƙan ƙungiyar ISWAP na kai ziyara ƙauyen da talatainin dare.

  5. Majalisa ta buƙaci a ɗage shirin kiɗayar jama'a a 2021 a Najeriya

    Majalisar wakilan Najeriya ta buƙaci a ɗage shirin ƙidayar jama'a da gidaje a Najeriya.

    Hukumar da ke kula yawan jama'a ta Najeriya ta shirya gudanar da ƙidayar ne a 2021.

    Amma majalisar wakilai ta buƙaci a ɗage ƙiɗayar saboda matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Gwamnatin tarayya ta amince da Naira biliyan 6.2 na ayyukan wutar lantarki a Najeriya

    Sale Mamman

    Asalin hoton, Twitter

    Majalisar zartarwa ta amince da ayyukan wutar lantarki da kuɗinsu ya kai dala miliyan 8.29 da kuma Naira biliyan 3.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Ministan Makamashi Injiniya Sale Mamman ya sanar da haka ranar Laraba bayan taron majalisar zartarwa tare da shugaba Muhammadu Buhari.

    Saleh ya ce ayyukan na gyara kamfanonin wutar lantarki ne don samun ƙaruwar wuta a ƙasar.

    Gaba ɗaya kuɗin da za a kashe ya kama naira biliyan 6,156,168,822 idan aka mayar dala.

    Ministan ya ce ayyukan sun ƙunshi sayen kayan aiki da za su taimaka wajen tura wuta zuwa matattarar wutar lantarki ta ƙasa don an tabbatar ko wane ɓangare na Najeriya na samun isasshiyar wutar lantarki.

  7. Kwamandan Hisbah da aka kora ya yi bayani kan zargin kaɗaicewa da matar aure a Otel

    Tsohon kwamandan Hisbah mai kula da kama karuwai a Kano, Sani Sidi Uba, ya yi bayani kan zargin kama shi da laifin kadaicewa da matar aure a otel wanda ya kai ga dakatar da shi

    Ya shaida wa BBC alaƙarsa da matar da ake zargin ya kaɗaice da ita tare da cewa sallamarsa daga aiki da hukumar Hisba ta Kano ta yi ba shi da alaka da laifin da ake zarginsa da aikatawa.

    A ranar Talata ne Hukumar Hisbah ta Kano ta bada sanarwar korarsa, bisa zargin cewa kwamitin da babban kwamandan hukumar ya kafa ya kama shi da laifin kadaicewa da matar aure a otal.

    Amma Sani Uba ya musanta a hirarsa da wakilin BBC a Kano Khalifa Shehu Dokaji.

    Bayanan sautiBayanin Kwamandan Hisbah mai kama karuwai a Kano Sani Sidi Uba
  8. An kama tsohuwa mai shekara 80 da hodar ibilis a Najeriya

    Wata tsohuwa da jikarta

    Asalin hoton, NDLEA

    Hukumar yaƙi da fatauci da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya (NDLEA) ta kama wata tsohuwa mai shekara 80 da jikarta ɗauke da hodar ibilis.

    Hukumar ta ce ta kama Mary Adebayo da jikarta Fumilola mai shekara 19 a garin Akure na Jihar Ondo da zargin sayar da miyagun ƙwayoyi tare da wasu mata guda biyu.

    Ta ce ta kama su da hodar ibilis mai nauyin kilogiram 192 da wasu ƙwayoyi.a ranar 2 ga watan Mayu bayan ta samu wasu wasu bayanan sirri.

    Ta ƙara da cewa an kama gyatumar ce da jikarta da misalin ƙarfe 6:30 na safiyar Lahadi.

    Sauran mata biyun su ne Tessy Mathew da Blessing Adesida masu shekara 25 kowaccensu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Labarai da dumi-dumi, Rabaran Ejike Mbaka ya bayyana

    Mabiya malamin addinin Kirista Rabaran Ejike Mbaka sun ɗauki sowar murna bayan da jagoran nasu ya bayyana jim kaɗan bayan sun gudanar da zanga-zanga bisa zargin jami'an tsaro ne suka kama shi.

    An ga rabaran ɗin sanye da shuɗayen kaya yana ɗaga wa dandazon mutanen da suka taru hannu don nuna murnar ganinsa a Jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya.

    Wani bidiyo da aka wallafa a Twitter ya nuna yadda mutane ke ife-ife a kan ababen hawansu suna cewa '"Mbaka Abata go" cikin harshen Igbo wato "Mbaka ya dawo".

    Tun da farko makusantansa sun faɗa wa masu ibada da suka taru a yau Laraba cewa ba su sake ganin Mbaka ba tun bayan da ya faɗa musu cewa zai je wata ganawa da Bishop Onaga kwana biyu da suka wuce.

    Mutanen sun yi zargin cewa jagoran nasu ya ɓace ne 'yan kwanaki bayan ya nemi Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka daga muƙaminsa saboda ƙaruwar matsalolin tsaro a ƙasar.

  10. Labarai da dumi-dumi, Mabiya Rabaran Mbaka na zanga-zanga a Enugu kan 'ɓacewar malamin'

    Mabiya malamin addinin Kirista Rabaran Ejike Mbaka sun mamaye tituna a Jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya suna zanga-zanga bisa zargin cewa an kama jagoran nasu.

    Mutanen sun yi zargin cewa jagoran nasu ya ɓace ne 'yan kwanaki bayan ya nemi Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka daga muƙaminsa saboda ƙaruwar matsalolin tsaro a ƙasar.

    Masu zanga-zangar na kiraye-kiraye ga cocin Catholic Bishop of Enugu da ta bayyana musu inda ya shiga.

    Makusantansa sun faɗa wa dandazon mabiyansa da suka taru a yau Laraba cewa ba su sake ganinsa ba tun bayan da ya faɗa musu cewa zai je wata ganawa da Bishop Onaga kwana biyu da suka wuce.

  11. 'Umaru Yar'Adua ɗan kishin ƙasa ne, shugaba mai tausayi'

    Umaru Musa Yar'Adua

    Asalin hoton, Others

    Shekara 11 bayan rasuwarsa, tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana alhinin rabuwa da mai gidansa Umaru Musa Yar’Adua.

    Shugaba Yar’Adua ya rasu ranar 5 ga watan Mayun 2010 bayan ya sha fama da jinya yayin da Jonathan ke matsayin mataimakinsa kuma ya gaje shi daga baya.

    "A yau ina tunawa da mai gidana, abokina, abokin aiki kuma ɗan uwa, Shugaban Ƙasa Umaru Musa Yar’Adua wanda ya bar duniya shekara 11 da suka wuce," in ji tsohon shugaban a shafinsa na Twitter.

    "A matsayinmu na 'yan siyasa, muna da buri iri ɗaya na samun dunƙulalliyar ƙasa mai cike da zaman lafiya da adalci."

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Shi ma tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma jigo a jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana Yar'Adua a matsayin "ɗan kishin ƙasa kuma shugaba mai tausayi".

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

  12. 'Miliyoyin mata da jarirai na mutuwa saboda rashin ƙwararrun unguwar zoma'

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari bayanin Nabeela Ismail, wata unguwarzoma a Jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya

    Wani rahoto ya ce miliyoyin mata da jarirai ne ke mutuwa yayin da wasu miliyoyin ke fama da rashin lafiya ko kuma rauni saboda ba a martabawa ko fifita bukatun mata masu ciki da kuma ƙwararrun unguwarzoma.

    Rahoton ya ce duniya a yanzu na fama da ƙarancin unguwarzoma 900,000, abin da ke nufin kashi ɗaya cikin uku na dukkan unguwarzomar da ake buƙata a duniya.

    Rahoton wani ɓangare ne na ranar tunawa da gudunmawar unguwarzoma a duniya wanda ake yi duk ranar 5 ga watan Mayu.

  13. Mun bai wa sojojin Najeriya naira tiriliyan 1 cikin shekara biyu - Ministar Kuɗi

    Zainab Shamsuna Ahmed

    Asalin hoton, @ZShamsuna

    Ministar Kuɗi da Tsare-Tsare a Najeriya, Zainab Shamsuna Ahmed, ta ce ma'aikatarta ta bai wa rundunar sojan ƙasar naira tiriliyan ɗaya (N1.008.47) daga Janairun 2019 zuwa Afrilun 2021.

    Ministar ta bayyana haka ne ranar Talata lokacin da take amsa tambayoyin kwamitin Majalisar Dattijai kan Sojojin Ƙasa.

    Kwamitiin ya gayyaci ministar ce biyo bayan ƙorafin da rundunar ta yi cewa akwai sauran naira biliyan 50 da ba ta karɓa ba daga ma'aikatar kuɗin, waɗanda suke cikin kasafin kuɗin da aka yi don yaƙar ta'addanci.

    Sai dai Zainab ta faɗa wa kwamitin cewa rundunar ta karɓi fiye da abin da aka ware mata a tsakanin lokacin da ake magana.

    "A 2019, an ware wa sojan Najeriya biliyan 19.6 kuma an ba ta 12.84 wato kashi 64.37 cikin 100 na kuɗin," in ji ta.

    "A 2020, jumillar kasafin rundunar soja naira biliyan 34.37 ne kuma an ba su 100 bisa 100 na kuɗin.

    "A 2021, wannan shekarar kenan, kasafinsu biliyan 29 ne. Ya zuwa watan Afrilu, mun saki biliyan 17.98 na kuɗin wato kashi 68.92 cikin 100. Hakan na nufin mun kusa ba su kashi 100 kenan."

    A watan Maris ne mai bai wa Shugaba Buhari shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, ya ce sun kasa gano inda maƙudan kuɗaɗen da aka ware don sayen makamai suka shiga a ƙarƙashin tsoffin hafsoshin tsaro da aka sauke a watan Janairu.

  14. 'Yaƙi na haifar da ƙarancin abinci mai gina jiki ga masu jego a Ethiopia'

    Wata mace

    Asalin hoton, AFP

    Kungiyar agaji ta Doctors Without Borders ta bayyana kaduwarta da yadda ake samun matsalar rashin abinci mai gina jiki a wasu sassan Tigray na Habasha da ke fuskantar rikice-rikice.

    A cewar kungiyar, lamarin na iya ta'azzara saboda zuwan lokacin damina.

    Kungiyar ta MSF ta ce mazauna yankin na fafutukar samun abinci inda ta koka cewa agajin da ake kaiwa ba ya isa zuwa yankunan Tigray da dama.

    "Tawagar MSF na duba matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara da mata masu juna biyu da mata masu shayarwa a cibiyoyin tafi da gidanka da ke wurare daban-daban a dukkanin yankin Tigary da ke Arewa maso Yammacin Habasha." in ji Karline Kleijer, Shugabar sashen ba da kulawar gaggawa na MSF.

    Kleijer ta ce cikin yara 309 da aka duba a cibiyoyin a makwannin da suka gabata, kashi 26.6 suna fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki sannan kashi 6 matsalar ta yi muni a jikinsu.

    A cewarta, akwai bukatar a kai daukin gaggawa.

    Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya aike dakaru zuwa Tigray a watan Nuwamba domin tsare yan aware na TPLF, jam'iyyar da ke mulki a yankin da ta taba mamaye siyasar kasar.

  15. Alamomin Lailatul Ƙadari da kuma dacewa da shi

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bayanin Sheikh Aminu

    Daren Lailatul Ƙadari dare ne mafi girma da ɗaukaka ga Musulmi.

    A daren ne wanda ke cikin kwanaki 10 na ƙarshen wata Ramadan aka saukar da Al ƙur’ani mai tsarki.

    Musulmi kan yi fatan dacewa da daren wanda Allah Ya ce ya fi wata 1,000 daraja.

    Ɗaya daga cikin manyan malamin addinin Musulunci a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Sheikh Aminu Daurawa, ya yi bayani game da daren da kuma alamominsa.

    Ɗaukar Bidiyo da Tacewa: Yusuf Ibrahim Yakasai

  16. Ba zan dawo Najeriya ba sai na samu tabbacin tsaron lafiyata - Jaafar Jaafar

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari cikakkiyar hira da Jaafar Jaafar

    Ɗan jaridan da ya fitar da jerin bidiyon da ke zargin Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da karɓar cin hanci ya ce ya bar Nijeriya ne saboda ba shi da ƙwarin gwiwar hukumomi za su kare rayuwarsa.

    Cikin hirarasa da BBC Hausa daga Ingila, Ja'afar Ja'afar ya ce zai ci gaba da neman mafaka a Birtaniya tare da iyalinsa har sai ya samu tabbacin za a kare rauywarsa idan ya koma Najeriya.

    Kazalika, ya yi zargin cewa cin hanci da rashawa a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari sun ƙara ta'azzara, inda ake yaƙar masu fallasa badaƙalar maimakon ainihin masu aikata cin hancin.

    A shekrar 2018 ne mawallafin jaridar Daily Nigerian ɗin ya saki wasu bidiyo da ke zargin cewa Gwamna Ganduje ne yake karɓar damman daloli daga hannun wani ɗan kwangila a matsayin cin hanci.

    Sai dai gwamnan ya sha musanta zargin yana mai cewa ƙirƙirar bidiyon aka yi.

  17. Derek Chauvin: Ɗan sandan da ya kashe George Floyd ya nemi a sake yi masa shari'a

    Tsohon jami'in ɗan sanda a Minneapolis na Amurka kuma farar-fata da aka samu da laifin kashe George Floyd a watan da ya gabata ya bukaci a sake masa sabuwar shari'a.

    Tawagar lauyoyin Derek Chauvin sun shigar da ƙorafi suna mai zargin an aikata ba daidai ba daga bangarorin masu gabatar da ƙara da taimaka wa alƙali.

    Sun ce akwai rashin adalci da bangaranci.

    A watan da ya gabata aka samu Mista Chauvin da duk lafukan da ake tuhamarsa da su na kisa da gangan da kisa ba da gangan ba.

    Sai nan gaba ne za a yanke masa hukunci game da laifukan.

  18. Hukunta 'yan fashin daji ba alhakin gwamnatin tarayya ba ne - Lai Mohammed

    Lai Mohammed

    Asalin hoton, @FMICNigeria

    Ministan Yaɗa Labarai na Najeriya Lai Mohammed ya nemi jam'iyyar adawa ta PDP da ta tuhumi gwamnonin ƙasar game da rashin hukunta 'yan fashin daji da masu garkuwa da mutane da aka kama maimakon gwamnatin tarayya.

    A cewar ministan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata, alhakin hukunta masu aikata fashi da kuma garkuwa da mutane ba na gwamnatin tarayya ba ne.

    Lai Mohammed ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga kalaman da ya ce PDP ta yi tana mai sukar gwamnatinsu ta APC game da matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar a nata taron manema labaran na ranar Litinin.

    "PDP ta yi zargin cewa ba a gurfanar da 'yan fashi a gaban kotu...abin mamaki ne a ce jam'iyyar PDP da ta mulki ƙasar nan tsawon shekara 16 ba ta san cewa hukunta masu fashi da garkuwa da mutane ba haƙƙin gwamnatin tarayya ba ne," in ji shi.

    "Saboda haka, ya kamata PDP ta matsa wa jihohi da kuma gwamnoni domin tabbatar da cewa an gurfanar da 'yan fashi da kuma masu garkuwa da mutane da aka kama."

    Tun farko PDP ta nemi Shugaban Ƙasa Buhari ya kafa dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a ƙasar baki ɗaya sakamakon kashe-kashen da 'yan fashi da Boko Haram ke aikatawa a arewaci da kuma masu fafutikar ɓallewa daga Najeriya a kudanci.

    Ministan ya zargi PDP da "yin wasa da kuma siyasantar da matsalolin ƙasa".

  19. 'Yan bindiga sun kashe sojojin Nijar kusan 30

    Sojojin Nijar

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Jamhuriyar Nijar da dama ne suka rasa rayukansu yayin wani hari da wasu mutane kan babura suka kai masu a yankin Tillabery.

    Kafafen yaɗa labarai na ƙasar sun ruwaito cewa kusan sojoji 30 ne suka rasu a fafatawar da suka yi da 'yan bindigar da ake zargin 'yan tawaye ne.

    Wata wasiƙa da rundunar sojan ƙasar ta aike wa magabatanta, ta ce maharan sun cinna wa gawarwakin sojin wuta bayan sun yi galaba a kansu.

    Takardar ta ƙara da cewa da taimakon 'yan gari aka samu gawar sojoji guda 16 da b asu ƙone ba.

    Gwamnatin sabon Shugaban Ƙasa Mohamed Bazoum ta fara ne da fuskantar hare-haren 'yan bindiga a yankunan da ke fama da rikici kamar Tillaberi da Tahoua da Diffa.

  20. Cutar korona a Najeriya: Mutum 34 sun kamu ranar Talata

    Cutar korona

    Asalin hoton, PA Media

    Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce ƙarin mutum 34 sun kamu da cutar korona ranar Talata.

    Rahoton da ta wallafa ya nuna cewa an samu mutanen ne a jihohi huɗu da suka ƙunshi Enugu mai mutum 19 da Legas mai 13 da Abuja da Kaduna masu mutum ɗaiɗai kowaccensu.

    Sai dai babu wanda ya rasu a ranar ta Talata, kwana shida kenan a jere ba a samu mutuwa ba.

    Sabbin mutanen sun sa jumillar adadin waɗanda suka kamu da cutar a Najeriya zuwa 165,215.

    Ya zuwa yanzu, mutum 2,063 cutar ta kashe a ƙasar sannan aka sallami wasu 155,371 bayan sun warke.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X