Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci hafsoshin tsaron ƙasar

Wannan shafi ne da ke muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Fauziyya Kabir Tukur

  1. An ƙara wa'adin haɗa lambar NIN da layukan salula a Najeriya

    Layukan waya

    Asalin hoton, Others

    Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ƙara wa'adin haɗa lambar shaidar ɗan ƙasa ta National Identification Number (NIN) da layukan salula zuwa watan Yuni.

    Ƙarin wa'adin ya biyo bayan wata ganawa da Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, ya yi da shugabannin hukumar sadarwa ta NCC da kuma hukumar samar da lambar NIN wato NIMC.

    Sanarwar da kakakin hukumar NCC da na ma'aikatar sadarwa suka fitar ta ce an ɗauki matakin ƙara wa'adin zuwa 30 ga Yuni saboda buƙatar da mahukunta suka nuna ta cewa hakan zai bai wa 'yan ƙasa damar yin rajistar cikin sauƙi.

    "An samu gagarumin ci gaba a rajistar haɗa NIN da layukan waya," a cewar sanarwar.

    "Kusan mutum miliyan 54 ne suke da lambar NIN a yanzu, abin da ke nufin masu amfani da layin waya kusan miliyan 190 kenan tun da bincike ya nuna cewa kowace lambar NIN na ɗauke da layukan waya uku zuwa huɗu."

    Sanarwar ta ƙara da cewa kamfanonin sadarwa da sauran cibiyoyin hukumar NIMC sun sake buɗe sabbin wuraren rajistar domin bai wa mutane da dama damar yi.

    Gwamnatin Najeriya ta ce haɗa layukan waya da lambar ɗan ƙasa ta NIN zai inganta tsaro da kuma bayanan da take da su na 'yan ƙasa baki ɗaya, yayin da ake ƙara wa lambar muhimmanci a wuraren ayyukan gwamnati a kowane mataki.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  2. Ƙarin mutum 18 sun kamu da korona a Najeriya

    Cutar korona

    Asalin hoton, NCDC

    Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce ƙarin mutum 18 sun kamu da cutar korona ranar Litinin.

    Rahoton da ta wallafa ya nuna cewa an samu mutanen ne a jihohi biyar da suka ƙunshi Lagos mai mutum takwas da Abuja mai shida da Edo mai biyu da kuma Rivers da Ogun masu mutum ɗaiɗai kowaccensu.

    Sai dai babu wanda ya rasu a ranar ta Litinin, kwana biyar kenan a jere ba a samu mutuwa ba.

    Sabbin mutanen sun sa jumillar adadin waɗanda suka kamu da cutar a Najeriya zuwa 165,199.

    Ya zuwa yanzu, mutum 2,063 cutar ta kashe a ƙasar sannan aka sallami wasu 155,371 bayan sun warke.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Maraba

    Masu bibiyarmu Umar Mikail ne ke muku barka da safiyar Talata, sannu da shigowa shafin labarai kai-tsaye an BBC Hausa.

    Za mu mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Ghana da Kamaru da Chadi maƙotansu - har ma da sassan duniya.

    Ku biyo mu.