Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci hafsoshin tsaron ƙasar

Wannan shafi ne da ke muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Fauziyya Kabir Tukur

  1. Buhari ya yi Allah wadai da kisan mutane a jihohin Benue da Anambra

    Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, Presidency

    Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan mutum 11 a Ƙaramar Hukumar Gwer West ta jihar Binuwai da kisan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da wasu gungun mutane suka tare su a hanya suka yi.

    A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan kafofin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya yi tur da kisan mutane a Anambra.

    "Ba za mu amince da kisan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba daga koma wanene," a cewarsa.

    Shugaban ya ce ƙiyayya da hamayya su ne ke haifar da irin waɗannan kashe-kashen. Ya kuma ce idan aka sa wa irin waɗannan mugayen mutane ido, lallai za su lalata dokokin ƙasar.

    Shugaban ya buƙaci shugabannin gargajiya da na addini sun yi amfani da matsayinsu wajen shawo kan mabiyansu don taimaka wa gwamnati a ƙoƙarinta na tabbatar da zaman lafiya.

    Shugaba Buhari ya gargaɗi ƴn Najeriya kan ɗaukar doka a hannayensu da sunan ramuwa saboda "babu wanda zai yi nasara a tashin hankali".

    Haka kuma, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mutanen da suka rasu da gwamnati da al'umar jihohin Binuwai da Anambra.

    Ya jinjina wa ƴan sanda da sauran jami'an tsaro bisa rawar da suka taka wajen gaggauta shawo kan rikicin.

  2. 'Akwai tsaro a gandayen dajin Najeriya'

    Hukumar Kula da wuraren shakatawa da yawon bude ido ta kasa a Najeriya ta ce ta dakatar da zuwa yawon bude ido a wuraren shakatawa na Cingurmi-Duguma da ke Lake Chad National Park a jihar Borno da kuma Kamukku National Park a jihar Kaduna saboda rashin tsaro.

    Sai dai Hukumar ta musanta rahoton da ya ambato gwamna jihar Taraba na cewa 'yan fashin daji sun mamaye wurin shakatawa na Gashaka-Gumti a jihar wanda ake jin shi ne mafi girma a yammacin Afrika.

    Shugaban hukumar kula da wuraren shakatawar Dokta Ibrahim Musa Goni ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai inda ya ce bayan wadancan biyu, jama'a na iya zuwa yawon shakatawa a dukkanin wuraren shakatawa da ke fadin kasar.

    Dokta Ibrahim ya ce har yanzu akwai masu bincike da ke zuwa Najeriya don gudanar da bincikensu a duka dazukan Najeriya cikin kwanciyar hankali in ba ya ga wasu dazuka ƴan ƙalilan a jihar Borno da yankin Birnin Gwari a Najeriya.

    Ya ce hukumarsa ta haɗa kai da sojojin Najeriya don tabbatar tsaro a gandayen dajin Najeriya.

  3. Atiku ya shawarci gwamnati ta yi wa tsoffin sojoji kiranye don su taimaka wajen yaƙi da ƴan bindiga

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugabancin ƙasar Atiku Abubakar ya yi kira da a kawo ƙarshen matsalolin tsaro a Najeriya cikin gaggawa.

    A wasu jerin saƙonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku ya ce talakawan Najeriya na rayuwa cikin fargaba da ɗar-ɗar.

    Ya ce babu inda ke da tsaro a ƙasar, ba a makaranta ba, ba a kasuwa ba, ba kuma a gonaki ba, ba masallatai ba kuma ba coci-coci ba

    Atiku ya ce abin takaici ne yadda masu ta da ƙayar baya ke saɓaɓowa daga yankin arewa maso gabashin Najeriya suna shiga jihohi kamar jihar Neja wadda ke maƙwabtaka da babban birnin ƙasar.

    Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar yi wa tsoffin jami'an tsaro kiranye su dawo bakin daga don taimakawa wajen yaƙi da masu ta da ƙayar baya.

    Atiku ya ce Najeriya za ta iya koyi da ƙasashe kamar Lebanon da Liberia da Saliyo da suka yi wa tsoffin sojojinsu kiranye kuma suka amsa don yi wa ƙasarsu hidima.

    Sannan ya shawarci gwamnatin tarayya kan ƙara wa jami'an tsaro albashi inda ya ce hakan zai ƙara masu ƙwarin gwiwar yin yaƙi bin haƙƙi da gaskiya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Ƴan bindiga sun yi wa mutum biyar yankan rago a Mozambique

    Mozambique

    Wasu masu iƙirarin jihadi a arewacin Mozambique sun yi wa mutum biyar yankan rago tare da yin garkuwa da wasu da ba a san adadinsu ba a wani hari a ƙauyen Pangane.

    Haka kuma, sun kai hari wani yanki da ke kusa da ƙauyen imda suka yi garkuwa da mutum huɗu.

    Hare-haren sun faru ne ranar JUma;a amma sai yau labarin ya fito saboda hukumomi ba su fiye son bayyana irin waɗannan labaran ba.

    Wasu majiyoyi sun ce ba dan ɗauki da ƴan sa-kai su yi kai ba da munin hare-haren ya fi haka.

    Sun kuma bayyana cewa a bainar jama'a maharan suka kwantar da mutanen suka yanka su.

    Wasu rahotanni na nuna cewa an kama wasu mutum biyu da ake zargin maharan ne kuma an kai su ofishin ƴan sanda.

    Yaƙi da masu ta da ƙayar baya a Cabo Delgado na ci gaba tun shekarar 2017 kuma ya turasasa wa dubban mutane tserewa daga muhallansu.

  5. Majalisar Wakilai za ta yi bincike kan matsalar tikitin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna

    Abuja-Kaduna Train

    Majalisar wakilai a Najeriya ta yanke shawarar gudanar da bincike kan zamba da ake yi wajen sayen tikitin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

    Majalisar ta gabatar da ƙudirin yin binciken ne a zaman da ta yi ranar Talata bayan da wani ɗan majalisa na jihar Kaduna ya shigar da batun.

    A watan Janairu ne gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da wata manhajar sayen tikiti, wadda aka kashe Naira miliyan 900 wajen samar da ita.

    A lokacin ne kuma ministan sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana cewa matakin zai kawo ƙarshen zamba da almundahana da masu bin jirgin suka daɗe suna ƙorafi a kai.

    Jaridar The Cable ta ruwaito cewa kawo yanzu mutane na kuka da yadda jami'an tashoshin jirgin ke cutar matafiya duk da damar sayen tikiti ta intanet.

    Honarabul Ibrahim ya ce an hana matafiya damar amfani da hanyar mai sauki saboda halin da ma'aikatan tashoshin suka ɗauka na sayen tikitin da yawa kuma su ɓoye shi sai matafiya sun zo daf da tafiya sai su fito da shi su sayar da tsadar gaske.

    Majalisar ta ce amince da ƙudirin kuma ta buƙaci Hukumar Jirgin Ƙasa ta Najeriyar da kamfanin da ya samar da manhajar da su ƙarfafa tsare-tsarensu da niyyar shawo kan matsalar .

  6. MDD ta zargi jami'an tsaron Colombia da cin zarafin masu zanga-zanga

    Ofishin majalisar dinkin duniya kan kare hakkin bil adam, ya zargi jami'an tsaron Colombia da amfani da karfi fiye da kima kan masu zanga-zanga.

    A kalla mutum 19 ne suka mutu a mako guda da aka dauka ana zanga-zanga kan sauye-sauyen haraji da gwamnati ta fitar.

    Majalisar dinkin duniya ta ce ta kadu matuka musamman kan abin da ya faru a daren jiya Litinin a birnin Cali, da 'yan sanda sukai amfani da harsashi kan masu zanga-zangar.

    Gwamnatin Colombia ta ce za ta sauya dokokin harajin da ta yi wa kwaskwarima, amma duk da hakan masu zanga-zangar sun ki janyewa daga titunan biranen kasar, inda suka shirya gagarumar zanga-zanga a gobe Laraba.

  7. Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci hafsoshin tsaron ƙasar

    Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci hafsoshin tsaro da sauran shugaban dukkanin hukumomin tsaron kasar domin duba yadda rashin tsaro ke kara kazanta a kasar.

    Wannan dai ya biyo bayanai da wani dan majalisar daga jihar Naija Hon Sani Musa ya bayar a makon jiya inda ya ce kusan kauyukka 42 ne ke hannun ‘yan bindiga a mazabar da yake wakilta kadai.

    Bashir Hayatu Jantile, babban mai taimaka wa shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan kan hulda da jama’a ya bayyana wa BBC cewa batun da ɗan majalisar ya yi ya tayar wa da ƴan majalisar hankali matuƙa shi ya sa suka buƙaci ganin hafsoshin tsaron.

    Ya ce majalisar dattijan ta yi zazzafan muhawara ba tare da duba da jam'iyya ko ɓangare ba don samun mafita dangane da matsalar tsaro da Najeriya ke fuskanta.

    "Daga nan ne aka yanke hukuncin a gayyaci hafoshin tsaron ƙasar su zo a tattauna tare da sanatocin nan na al'umar Najeriya don gano asalin abin da ke faruwa dangane da tsaro."

    "Harkar tsaro ta wuce inda ake tunani yanzu matsalar a gaba ɗaya Najeriya ta ke," a cewarsa.

    Jantile ya ce baya ga Hafsoshin tsaro, majalisar dattijan ta gayyaci sauran hukumomin tsaro kamar Jami'an tsaro na farin kaya da Civil Defence da dai sauransu saboda lamarin ya kai matsayin da sai kowa ya sa hannu a ciki.

    Saurari cikakkiyar hirar da Haruna Shehu Tangaza ya yi da Bashir Hayatu Jantile:

    Bayanan sautiMajalisar Dattijai ta gayyaci Hafsoshin Tsaron Najeriya
  8. Ɓangaren adawa a Indiya na so a sanya dokar kulle a faɗin ƙasar saboda korona

    India Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

    Babbar jam'iyyar adawa ta Congress Party a Indiya ta yi kira da gwamnati ta sanya dokar kulle a daukacin kasar, a dai-dai lokacin da yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar korona ya haura miliyan biyu.

    Shugaban jam'iyyar Rahul Gandhi, ya ce babu wata hanyar da ta rage na yaki da yaduwar cutar face dokar kullen.

    Mai magana da yawun jam'iyyar Pawan Kehra ya shaida wa BBC cewa fannin kiwon lafiya a Indiya na gab da durkushewa, yayin da mutane ke shiga shafukan sada zumunta domin neman taimako.

    Firai minista Narendra Modi ya na duba yananin tattalin arzikin da kasar ka iya fuskanta, shi ya sa ya ke dakewa matsin lamabar da ake ma sa kan sanya dokar kulle.

  9. Kun san manyan attajiran duniya da aurensu ya mutu?

    Jeff Bezos da matarsa Mackenzie

    Asalin hoton, Getty Images

    Aure wani muhimmin jigo ne a rayuwar kowane bangare na halitta wanda ta hanyarsa ne al'umma ke yaduwa.

    Sai dai a duk lokacin da aure ya mutu, hakan yana taɓa zukatan jama'a.

    Haka lamarin yake idan aka ce auren wasu mashahurai ko attajirai ya mutu a duniya - lamarin na jan hankalin al'umma har ta kai an samar da maudu'i a shafukan sada zumunta musamman a Tuwita domin tattauna abin.

    Hakan ne ya sa labarin rabuwar auren Bill da Melinda Gates ya ja hankalin duniya, lamarin da har yanzu yake cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a kansu a shafukan intanet.

    Baya ga mutuwar auren Bill da Melinda Gates, akwai wasu manyan attajirai da su ma a baya aurensu ya mutu.

  10. Ƴan taliban sun kashe jami'an tsaro takwas a Afghanistan

    Hukumomi a Afghanistan sun ce akalla jami'an tsaro takwas ne suka mutu a taho mu gama da mayakan Taliban kudancin yankin Helmand.

    Shugaban yankin ya ce masu tada kayar bayan sun karbe iko da wuraren zaman jami'an tsaro kusan goma da ke kusa da birnin Lashkar Gah.

    Ma'aikatar tsaron Afghanistan ta ce ta aike karin dakaru yankin, kuma a taho mugamar an kashe kwamandan Taliban a hare-hare ta sama da aka kai maboyarsu.

    Fadan da ake yi a Helmand na zuwa ne adaidai lokacin da sojojin Amurka suka fara janyewa daga kasar, wanda kashin karshe za su fice a watan Satumba mai zuwa.

    Mayakan Taliban na kara kai munanan hare-hare a gundumomin kasar.

  11. Wakilan ƙasashen G7 sun haɗu gaba da gaba a karon farko cikin shekara biyu

    Dominic Raab da Luigi Di Maio

    Asalin hoton, Getty Images

    A karon farko cikin kusan shekaru biyu, ministocin harkokin wajen kasashe masu karfin masana'antu na G7 na yin taron gaba da gaba a birnin Landan.

    Za su mayar da hankali kan tattaunawar yadda kasashen za su hada hannu dan magance kasashe masu mulkin danniya kamar Rasha da China.

    Za kuma su duba batun amfani da matakan diflomasiyya kan kasashe kamar Iran da Syria.

    Wakilan kasashen Indiya da Australia da Afirka ta Kudu da Koriya ta Kudu da Brunei na cikin mahalarta taron.

    Sakataren harkokin wajen Birtaniya, Dominic Raab, ya ce halartar taron da suka yi ya nuna kasashen sun aminta da hada karfi da karfe domin magance matsalolin da ake fuskanta.

  12. Iyayen ɗaliban da aka sace a Kaduna sun yi zanga-zanga a Abuja

    Zanga-zanga
    Bayanan hoto, Rabi Zakariya Magaji na cikin iyayen ɗaliban da aka sace a kwalejin Federal College Of Forestry Mechanization

    Iyayen ɗaliban Kwalejin Nazarin Gandun Daji da aka sace a Jihar Kaduna sun gudanar da zanga-zanga a Abuja domin nuna fushinsu game da halin da yaransu ke ciki.

    Mutanen waɗanda suka taru a ƙofar ginin majalisar tarayya, sun yi kira ga gwamnati ta ƙara azama wajen ceto 'ya'yan nasu.

    Sun fara tattaki ne daga dandalin Unity Fountain zuwa ginin majalisar ɗuke da kwalaye da sauran kayayyaki masu ɗauke da saƙonni iri-iri.

    Zanga-zanga

    A watan Maris da ya gabata ne 'yan bindiga suka yi garkuwa da ɗaliban guda 39 a ɗakunan kwanansu, inda daga baya suka saki 10 daga cikinsu.

    Sai dai gwamnatin Jihar Kaduna ta ce ba za ta biya kuɗin fansa ba wajen karɓo ɗaliban yayin da suka shafe kusan wata biyu a hannunsu.

    'Yan bindiga sun sace ɗlibai fiye da 800 a Najeriya tun daga watan Disamban 2020.

  13. Fiye da mutum miliyan 20 sun kamu da korona a Indiya

    Indiya

    Asalin hoton, Getty Images

    Waɗanda suka kamu da cutar korona a Indiya sun zarta miliyan 20 duk da cewa gwamnati ta ce mutanen "na raguwa".

    An samu ƙarin mutum 355,000 da suka kamu da cutar a yau Talata, ƙasa da 400,000 da aka samu ranar 30 ga Afrilu.

    Adadin mutanen da ake yi wa gwaji ma ya ragu sosai, abin da ya sa ake fargabar haƙiƙanin adadin masu kamuwa da cutar ya fi haka yawa.

    A Jihar Maharashtra, an samu raguwar masu kamuwa, inda ita ce kan gaba tun bayan sake ɓarkewar cutar a karo na biyu daga farkon Afrilu.

    Sai dai har yanzu akwai matsalar ƙarancin iskar oxygen a yankunan da ke da yawan masu cutar, ciki har da Delhi babban birnin ƙasar.

    Ya zuwa yanzu, an bayar da rahoton mutuwar mutum 222,000 a ƙasar sakamakon cutar.

    Sai dai wasu na cewa adadin ya zarta haka saboda abin da mutane ke gani a ƙasa sun fi na rahoton gwamnati yawa.

  14. Buhari ya jagoranci taron majalisar tsaro karo na biyu

    Najeriya

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar tsaro a fadarsa ta Aso Rock Villa da ke Abuja.

    Taron na zuwa ne kwana huɗu kacal bayan ya jagoranci makamancinsa tare da shugabannin tsaron ƙasar.

    Daga cikin mahalarta taron akwai Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, da Sakataren Gwamnati Boss Mustapha, da Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Ibrahim Gambari.

    Najeriya

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Sauran su ne: Ministan Tsaro Bashir Magashi, da Mai Ba wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro Babagana Monguno, da sufeto janar na 'yan sanda da kuma manyan hafsohsin tsaro.

    Babu wani ƙarin bayani zuwa yanzu game da abin da aka tattauna a taron.

    Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro iri daban-daban a dukkan ɓangarorin ƙasar, abin da ya sa rundunar 'yan sandan ƙasar ta ce za ta baza dakarunta a kan dawaki da babura saboda inganta tsaro a Abuja.

  15. An ƙaddamar da rigakafin korona a jihohin Nijar

    Dr Illiyassou Idi Mainasara

    Hukomomi a Jamhuriyar Nijar sun ƙaddamar da allurar rigakafin cutar korona a dukkan jihohin ƙasar.

    Ministan Lafiya Dr Illiyassou Idi Mainasara ne ya ƙaddamar da shirin, wanda ake sa ran za a yi wa mutum 800.000 rigakafin a faɗin ƙasar.

    Wata ɗaya kenan da fara yi wa mazauna birnin Yamai allurar, inda a yau Talata aka ƙaddamar da zagaye na biyu wanda ya ƙunshi jihohi.

    Cutar ta kama jumillar mutum 5,251 a Nijar, a cewar alƙaluman Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), kuma ta yi ajalin 191 tun bayan ɓullarta a ƙasar.

    Ma'aiaktan lafiya a Nijar
  16. Hatsarin mota ya kashe mutum 6 a Jihar Ogun

    Hatsari

    Asalin hoton, NAN

    Mutum aƙalla shida ne suka rasa rayukansu sakamakon wani hatsarin mota da daren Litinin a Jihar Ogun da ke kudancin Najeriya.

    Hatsarin wanda ya ritsa da ababen hawa guda uku, ya faru ne a kan titin Sagamu zuwa Benin, a cewar kwamandan hukumar kiyaye haɗura na Ogun Ahmed Umar.

    Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito shi yana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:01 na dare kuma kuskure wajen wuce abokan tafiya da kuma gudun rashin kan gado ne suka haddasa shi.

    Ya ƙara da cewa mutum 39 ne hatsarin ya ritsa da su, maza 25 da mata 14, inda maza biyar da mace ɗaya suka mutu.

    "Babbar motar bas ce ta daki mota ƙirar Toyota Sienna da kuma Mazda," in ji shi.

    "Nan take direban motar ya gudu saboda dukkan fasinjojin cikin Sienna sun mutu yayin da na Mazda suka ji raunuka."

  17. Gwamnatin Mexico ta nemi afuwar ƙabilar Maya

    Shugaban Mexico ya nemi afuwar kabilar Maya kan abin da ya kira mumunan cin zarafin da suke fuskanta tun lokacin da Spaniya ta ci su da yaƙi shekara 500 da suka gabata.

    Andres Manuel Lopez Obrador ya ce abin da aka aikata a kansu abin kunya ne.

    Ministan Harkokin Cikin Gida, Olga Sanchez, ya ce al'ummar Maya sun ci gaba da fuskantar wariya da rashin kulawa.

    Waɗanan kalamai na zuwa ne a taron da jami'an Mexico da shugaban Guatemala, Alejandro Giammattei, ke halarta a kudu maso gabashin Mexico.

    Mista Gimmattei ya ce har yanzu ƙabilar Maya na cikin wahala sakamakon mugayen laifuka da rashin abinci mai gina jiki da sauya matsuguni a kokarin neman rayuwa mai inganci.

  18. Mutum miliyan 3 ne suka yi Umara a watan Ramadan

    Masallacin Harami

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutum fiye da miliyan uku ne suka gudanar da aikin Umara a Masallacin Harami a cikin watan Ramadan, a cewar wasu alƙaluma da shafin Haramain Sharifain ya wallafa.

    Miliyoyin Musumai ne bisa al'ada ke zuwa masallacin duk watan Ramadan kafin al'amura su sauya sakamakon annobar korona da ta jawo soke yin Hajji da Umara ga 'yan ƙasar waje a 2020.

    Wannan adadi ya nuna irin ci gaban da aka samu wajen sassauta dokokin bayar da tazara.

    A watan Maris ne aka bai wa tsofaffi 'yan shekara 60 damar gudanar da aikin bayan an dakatar da su saboda tsoron kamuwa da cutar.

    Cutar korona ta kashe mutum 6,979 a Saudiyya yayin da ƙasar ta yi wa mutum kusan miliyan tara rigakafin cutar.

  19. Hatsarin jirgin ƙasa ya kashe mutum 23 a Mexico

    Mexico

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani hatsarin jirgin ƙasa a Mexico ya yi sanadin mutuwar mutum 23 tare da jikkata wasu da dama ranar Litinin a babban birnin ƙasar.

    An ga yadda taragon jirgin ke reto a jikin wata gada cikin wasu wayoyi, inda goshin jirgin ke kallon ƙasa.

    "Abin baƙin ciki mutum 20 ne suka mutu zuwa yanzu, ciki har da yara," a cewar Magajin Garin Mexico City, Claudia Sheinbaum.

    Sashen tsaro na birnin ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa kusan mutum 70 ne suka ji raunuka.

  20. An umarci makarantu a Ghana su ƙyale ɗalibai su yi azumi

    Ɗaliban Ghana

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ilimi ta Ghana ta umarci dukkan makarantu da su bai wa ɗlibai Musulmai damar yin azumi ba tare da tsangwama ba biyo bayan ce-ce-ku-ce da ya ɓarke game da hana wata ɗalibar sakandare yin azumin.

    A makon da ya gabata ne rahotonni suka bayyana yadda wani mahaifi ya yi dirar mikiya a Wesley High School da ke yankin Capecoast don cire `yarsa daga makarantar bayan ta yi masa korafin cewa hukumumin makarantar sun ƙi amincewa ta yi azumi.

    Lamarin ya janyo muhawara tskanin Musulmai da Kiristoci musamman a kafafen sada zumunta.

    Sanarwar da hukumar ilimin Ghana ta fitar ta ce wajibi ne makarantu su ƙyale yara su yi azumin amma da sharaɗin babu haƙƙinsu kan duk abin da ya samu ɗliban sakamakon yin hakan.

    Isma'ila Zakariyya Alasan, shi ne mahaifin ɗalibar da ake zargin hana ta azumin mai Bushira kuma ya shaida wa BBC Hausa cewa ya ji daɗi da ganin sanarwar amma har yanzu bai gamsu ba.

    Shi ma babban limamin Ghana Sheikh Osmanu Nuhu Sharubutu ya bayyana jin daɗinsa da matakin da hukumar ilimin ta ɗauka.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X