Rufewa
Nan muka kawo karshen labarai da rahotannin na mu na wannan rana. Muna muku barka da shan ruwa.
Sai mun sake haduwa a gobe idan Allah ya kai mu.
Wannan shafi yana kawo muku bayanai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Awwal Ahmad Janyau and Buhari Muhammad Fagge
Nan muka kawo karshen labarai da rahotannin na mu na wannan rana. Muna muku barka da shan ruwa.
Sai mun sake haduwa a gobe idan Allah ya kai mu.

Asalin hoton, Reuters
Adadin wadanda annobar Korona ta kashe a fadin duniya sun haura mutun miliyan uku.
Alkaluman da ami'ar John Hopkins ta fitar sun nuna cewa Amurka ce ke da adadi mafi yawa sannan Brazil sai Mexico sai kuma India.
Firanministan India Narendra Modi ya yi kira ga mabiya addinin Hindu da su kauracewa taron al'ada na Kumbh Mela saboda gudun bazuwar cutar Korona.
Miliyoyi a India sun saba haduwa don gudanar da bikin na Kumbh Mela. Kwanaki takwas a jere ana samun sama da mutun dubu dari biyu da suka kamu da cutar Korona.

Asalin hoton, AFP
An sake kashe wasu 'yan kasuwar arewacin Najeriya a Jihar Imo a wasu sabbin hare-hare da aka kai musu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe 'yan kasuwar ne a makon jiya.
An ruwaito cewa an kashe mutum hudu a Orlu aka kuma kashe wasu uku a garin Amaka.
Wani mazaunin garin Owerri Dr Lawal Yusuf ya dora alhakin kisan kan yan kungiyar IPOB.
"Ko a jiya sai da 'yan IPOB suka kai wa yan arewa hari suka kashe mutum uku masu sayar da nama. Da safiyar yau muka binne su."
"Duk lokacin da suka hadu da mutanen arewa sai su tambaye su wanene ya basu izinin zama a yankin Biafara, ko kuma suna da shaidar zama a yankin? in kace a'a sai su yi wa mutum dukan tsiya: an kashe mutanenmu da yawa ta wannan hanyar," in ji Dakta Lawal.

Asalin hoton, Reuters
Iran ta ce ta gano mutumin da take son kamawa wanda ke da alaka da harin da aka kai tashar nukiliyarta ta Natanz, yayin da kasashen duniya ke ci gaba da tattaunawa a Vienna domin dawo da yarjejeniyar makamai ta 2015.
Mutumin mai suna Reza Karimi wanda ake zargi da wannan zagon kasa, gidan talabijin na kasar ya ce hukumar leken asiri ta kasar ce ta gano shi. Tana cewa mutumin ya tsrere ne daga Iran gabanin ranar Asabar din da aka kai harin wanda ta zargi babbar abokiyar hamayyarta Isra'ila da kai wa.
Jami'ai daga sassa daban-daban da suka halarci tattaunawar da aka soma a ranar Alhamis, sun ce ana samun ci gaba a zaman.
Gidan talabijin din ya haska hoton mutumin da ake zargi a wani hoto mai kama da katin shaida tare da rubuta yan sanda kasa da kasa na neman shi ruwa a jallo, a jiki an bayyana shekarunsa 43.
Sarauniya ce ta yi jagoranci iyalinta da sauran jama'ar kasa baki daya wajen makokin jana'izar mijinta Duke na Edinburgh a Windsor.
Ya zuwa yanzu dai an kammala duk abin da za a yi na jana'izar.

Asalin hoton, PA Media

Asalin hoton, PA Media

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
An kashe dan sanda guda a wani musayar wuta da aka yi tsakanin wasu yan bindiga da suka kusa 200 wadanda suka zagaye wurin binciken ababan hawar da jami'an ke aiki a Dogon-Gawa na Karamar Hukumar Takum a jihar Taraba da ke arewacin Najeriya.
Wasu jagora a yankin Shiban Tikari ne ya tabbatarwa da manema labarai faruwar Lamarin, inda ya ce 'yan bindigar sun dira wajen ne a safiyar Asabar.
Yace yana wurin lokacin da 'yan bindigar sama da 200 suka yiwa jami'an kawanya.
Ya ce an dade ana ta musayar harsashi tsakanin mutanen da jami'an da ke kan aiki, abiun da ya yi sanadin mutuwar dan sanda daya kenan.

Asalin hoton, Getty Images
Juventus ta ce dan wasanta na gaba dan kasar Portugal Cristiano Ronaldo ba zai buga wasan da za ta yi ban a Serie A da kungiyar Atlanta.
Kocin kungiyar Andrea Pirlo ya ce dan wasan mai shekara 36 wanda shi ne ke kan gaba a yawan cin kwallaye da 25, zai huta a wasan gudun kar ya kara samun wani rauni mai hadari.
“Wannan rashin na shi babba ne ga kungiyarmu. Cristiano ba zai buga wasannan na saboda raunin da yake fama da shi,” Pirlo ya shaida wa manema labarai.
“Na kwanaki ya yi ta fama da jinya bayan wasan da muka buga da Genoa.”
An ta buga bindiga tun da farko yayin fara jana'izar Duke na Edinburgh Yarima Philip, an kuma yi shiru na minti daya domin nuna bukatar nutsuwa yayin fara jana'izar.

Asalin hoton, RAF/MOD/Crown Copyright/Reuters

Asalin hoton, MOD/EPA

Asalin hoton, Reuters
Kafafen yada labarai na Qatar sun ce Ministan harkonkin wajen kasar ya ce kasarsa da ke shirin daukar nauyin gasar cin kofin duniya a shekara mai zuwa, tana magana da kamfanonin da suke samar da rigakafin korona domin tabbatar da an yi wa duk wadanda suka je kallon gasar rigakafin.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa “A yanzu haka a kwai shirin da muke yin a yi wa duka wadanda za su zo kallon gasar rigakafin. Muna da kwarin gwiwar za mu iya daukar nauyin kasar ba tare da kowa ya kamu da cutar ba,”in ji Sheik Mohammed bin Abdulrahman al-Thani, wanda shi ne mataimakin Firaiministan kasar.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Giani Infantino, ya ce a watan Fabrairu shekara mai zuwa za a buga wasanni a filayen wasa na kasar a gasar cin Kofin Duniya mai zuwa.

Asalin hoton, GETTY IMAGES
Sojojin Najeriya sunkashe ‘yan bindiga biyar wadanda suka kai hari wani yanki a karamar hukumar Makurdi da ke jihar Benue.
Rahotanni sun ce sojojin sun dirarwa maboyar ‘yan bindiga da ke tsakanin iyakar jihar Benue da ta Nasarawa.
Sun kuma bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai hari kan kauyen Anune tun da fari, wani karamin kauye da ke yankin Makurdi tare da kashe mutane a cikinsa.
Wani wanda ya shaida faruwar lamarin ya ce tun da misalign karfe 9 zuwa 10 na safiyar Asabar suka ga jirgi mai saukar angulu yana shawagi a saman inda aka kai harin, kafin daga bisani motocin ‘yan sanda su isa wurin.
Shaidar ya ce sojojin sun kutsa kai cikin dajin da ake zargin yan bindigar suka ciki, daga baya kawai sai aka ga sun fito da gawa kimanin guda biyar.
Shugaban Windsor David Conner da Archbishop na Canterbury Justin Welby ke jagorantar bikin a Cocin St George.
Su suka karɓi gawar Yarima Philip bayan iso da gawar kafin fara addu'o'in binne shi.


Gidan sarautar Burtaniya sun taru a Fadar Windsor, kusa da London, domin jana’izar Duke na Edinburgh.
An saka gawarsa a cikin motar da ya taimaka aka ƙera Land Rover.

An shiru na minti ɗaya bayan ɗauko gawarsa
An taƙaita yawan mutanen da za su halarci jana’izar a Cocin St George zuwa mutum 30 saboda matakan korona.
Amma sama da sojoji 700 ne suka shiga fadar.

Yarima Philip ya mutu a makon da ya gabata yana da shekara 99. Sun yi rayuwar aure da Sarauniya Elizabeth sama da shekaru 70.
Ana sa ran miliyoyin mutane ne a duniya za su kalli bikin jana’izarsa a kafafen talabijin da rediyo.


Bello Bala Shagari, jikan tsohon shugaban Najeriya marigayi Alhaji Shehu Shagari ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya ƙarfafa masa guiwa shiga harakokin siyasa.
Bello Shagari na neman kujerar shugaban ƙaramar hukumar birnin Abuja da kewaye AMAC.
Matashin wanda tsohon shugaban majalisar matasa ta Najeriya NYCN ne, ya ce ya yanke shawarar tsayawa takara ne saboda "goyon baya da ƙwarin guiwa da muka samu daga shugaba Muhammadu Buhari."
"Shugaba Buhari ya ƙarfafa muna guiwa ne a ziyarar da muka kai masa cikin tawagar matasa a fadarsa inda ya nemi mu tsaya takara domin kawo sauyi," in ji shi.
A ranar Talata ne za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Abuja.
Hukumomi a jihar Kaduna arewacin Njeriya sun gudanar da wani taro na malaman addinin Musulunci da nufin tattauna yadda za a kaucewa yin wa’azi da kan haifar da rarrabuwar kai tsakanin al’umma musamman yayin gudunar da tafsirin watan Ramadana.
Haka kuma taron ya duba yadda za a ci gaba da kiyaye matakan kariya daga cutar korona yayin fara gudanar da Tafsirin.
Yusuf Tijjani ya tattauna da Shiekh Hashim Bindawa babban limamin Masallacin Shiekh Dahiru Usman Bauchi da Shiekh Ishaq Al Madani babban limamin masallacin Matazu Road da ke Tudun Wada Kaduna da kuma Shiekh Jamil Al Bani Zaria Daraktan da ke kula da harakokin addinin musulunci a jihar Kaduna.

Asalin hoton, EPA
Tsohon shugaban kasar Cuba, Raúl Castro, ya tabbatar da cewa zai yi murabus daga shugabancin Jam’iyyar Kwaminisanci, abin da zai kawo karshen jagorancin sama da shekaru sittin da danginsu suka shafe suna yi.
Mista Castro mai shekara 89 yanzu a duniya, ya ce zai miƙa jagorancin ne ga ƴan Cuba da ya kira sabbin jinin, masu cike da ƙauna da nuna adawa da mulkin mallaka.
Raúl Castroƙani ne ga shugaban juyin juya halin Cuba, marigayi Fidel Castro.
Fiye da mutum miliyan uku cutar korona ta kashe zuwa yanzu a faɗin duniya kamar yadda alƙalumman Jami'a Johns Hopkins da ke sa ido kan annobar a duniya suka nuna.
Alƙalumman sun ce sama da mutum miliyan 141 cutar ta shafa a ƙasashe 192.
Cutar ta fi yin kisa a Amurka inda ta kashe mutum 566,224. Brazil ce ta biyu inda cutar ta kashe mutum 368,749. Indiya ce kuma ƙasa ta uku da cutar ta fi yin kisa inda ta halaka mutum 175,649.

Asalin hoton, Getty Images

Sarauniya Elizabeth ta Ingila na shirin yin ban kwana da mijinta da suka shafe shekara 73 a tare.
An yi shirin bikin jana’izarar Yarima Philip a yau Asabar. Daga cikin shirye-shiryen sun haɗa har da mota ƙirar Land Rover da za a ɗauki gawarsa.
Shi ya taimaka aka zana motar a tsawon shekaru 16, kafin a aka yi mata kwaskwarima a 2019.
Iyalan gidan sarautar za su yi jerin gwano a bayan Land Rover, yayin da kuma Sarauniya za ta shiga wata motarta ta daban ƙirar Limousine.

A 2002 aka gabatar da motar ga Sarauniya lokacin da ta cika shekara 50 a gadon sarauta.

Gwamnatin Rasha ta buƙaci jami'an diflomasiyar Amurka 10 su fice daga ƙasarta, Kwana guda bayan sanarwar da Amurka ta yi na ƙaƙaba sabbin takunkumai kan Rasha.
Ministan harakokin wajen Rasha Sergei Lavrov wanda ya sanar da ɗaukar matakin ya ce ƙasarsa ta ɗauki matakin ne a matsayin martani ga takunkumin da Amurka ta ƙaƙabawa kamfanonin Rasha 32 da kuma korar jami'an diflomasiyarta 10 daga Amurka.
Mr Lavrov ya ce ma'aikatar harakokin wajen Rasha tana son jakadan ƙasar a Amurka ya dawo gida.
Isra'ila ta ce ta kai harin bama-bamai a Gaza a matsayin martani ga hare-haren rokoki da aka kai mata daga kudancin Gaza.
Karo na biyu kenan a baya-bayan nan da ake cilla wa Isra'ila rokoki daga Zirin Gaza.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta tarwatsa wani sansanin soja da inda ake bayar da horo na ƙungiyar Hamas.
Majiyoyin Falasdinawa sun ce hare-haren sun lalata gonakinsu.
Jihar Kaduna ta tara sama da naira biliyan 50 a 2020 inda ta kasance ta biyar a jerin jihohin da suka fi samun kuɗaden shiga, kamar yadda rahoton hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS ya bayyana.
Rahoton ya ce jihar Kano cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya ta kasance matsayi na takwas a jerin jihohin inda ta tara sama da naira biliyan 31.
Hakan na nufin jihar Kaduna ta ba jihar Kano tazarar kusan naira biliyan 19.
Rahoton ya ce jimilar naira tiriliyan 1.31 jihohin na Najeriya suka tara a 2020, amma adadin ya yi ƙasa idan aka kwatanta da 2019 inda suka tara naira tiriliyan 1.33.
Jihar Legas ce ta farko inda ta samu sama da naira biliyan 418, jihar Rivers ce ta biyu da ta samu sama da naira biliyan 117, sai birnin tarayya Abuja a matsayin na uku da ya samu sama da naira biliyan 92.
Jihar Delta ce ta huɗu inda ta samu sama da naira biliyan 59 a 2020.
Ogun da ke matsayi na shida ita ke bi wa Kaduna inda ta tara sama da naira biliyan 50.
Jihar Yobe ce ta ƙarshe a jerin matsayin jihohin na tara kuɗaɗen shiga a jihohinsu.

Asalin hoton, NBS