Sojojin Najeriya sun ce sun kashe kwamandojin ISWAP 18

Wannan shafi yana kawo muku bayanai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge

  1. PDP ta tsoma baki kan rikicin Kwankwaso da Tambuwal

    Shugaban PDP

    Asalin hoton, PDP

    Jam'iyyar PDP reshen jihar Kano ta ce ta kai ƙorafi gaban uwar jam'iyyarsu kan yadda gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ke kokarin kawo rikici wajen zabar mataimakin shugaban jam'iyyar reshen arewa maso yamma.

    PDPn Kano ta zargi Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da ƙoƙarin haifar da ruɗani, da yi musu yankan-baya da kuma yunƙurin hana su damar da aka bai wa kowacce jiha a shiyyar kamar yadda wani taron jagororin arewa maso yamma ya amince kwana guda kafin babban taron.

    A cewarta Aminu Tambuwal ya saya wa wani ɗan takara daga Kano takardun neman kujerar mataimakin shugaban PDP shiyyar arewa maso yamma da kuma dagewa kan lallai sai an yi zaɓe bayan kowacce jiha ta amince da masalaha wajen fitar da duk kujerun da aka keɓe mata.

    Karanta cikakken labarin a nan:

  2. Barkanmu da Juma'a

    Barkanmu da Juma'a. Ku biyo ni Nasidi Adamu Yahaya a wannan shafi domin karanta labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya a Nijar da maƙwabtansu.