Sojojin Najeriya sun ce sun kashe kwamandojin ISWAP 18

Wannan shafi yana kawo muku bayanai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge

  1. Bankwana

    Nan muka kawo muku karshen labarai da rahotannin da muke kawo muku a wannan shafin.

    Buhari Muhammad Fagge ke muku fatan an sha ruwa lafiya.

  2. China da Amurka ne suka fi masana'antu masu fitar da hayaki a duniya

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    A cikin wani taro da suka yi tare da shugabannin kasashen Faransa da na Jamus, shugaban kasar China Xi Jinping, ya yi kiran da a hada kai a yakin da ake akan sauyin yanayi.

    Shugaba Xi ya shaida wa takwaransa na Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel cewa, batun sauyin yanayi batu ne wanda mutum ya kirkire shi.

    To sai dai kuma Mr Xi ya soki shirin tarayyar turai na bullo da haraji akan kayayyakin da aka yi su a masana'antun da ke fitar da matukar gurbatacciyar iska wanda hakan zai iya shafar fitar da kayayyakin da kasar china ke yi.

    Wakilin BBC yace China ce kasar da ta fi ko wacce a duniya fitar da hayaki, sai kuma Amurka da ke biye mata.

    Kasashen biyu ne ke fitar da kusan rabin hayakin da ake fitarwa a duniya.

    Kuma Shugaba Biden ya lashi takobin canza haka

  3. Kimanin mata masu juna biyu 124, 817 ne ke fama da HIV/AIDS jihar Ondo

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Duka da kokarin da ake a fadin duniya na ganin an kawar da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDS a duniya, a Najeriya akwai mutum sama da miliyan 1.9 da ke rayuwa da cutar.

    Hukumomi sun bayyana cewa kimanin mata masu juna biyu 124, 817 ne ke rayuwa da wannan mummunar cuta a jihar Ondo kadai.

    Wannan na zuwa ne lokacin da za a bude wani shirin tallafa wa masu mafa da cuatar a Akure babban birnin jihar ta Ondo.

    Sakataren gwamnatin jihar Oladunni Odu, wanda ya wakilci gwamna a yayin taron, ya ce adadin wadannan mutanen an same su ne kawai a cikin kananan hukumomi 18 na jihar.

    Wadanda suka shirya taron sun yi alkawarin za su yi duk mai yiwuwa domin ganin an kawar da wannan cuta daga jihar.

    Sun ce wannan cuta yanzu ba barazana ba ce kamar yadda ake ganinta a baya.

  4. Sojojin Najeriya sun ce sun kashe kwamandojin ISWAP 18

    @HQNigerianArmy

    Asalin hoton, @HQNigerianArmy

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe wani babban kwamandan kungiyar ISWAP mai suna Bukar Gana wanda ake kira da Abu Asiha, tare da wasu mayakansa wadanda suke shirin daukar fansa a yankin Damasak, bayan wani dauki ba dadi da suka yi da sojin Najeriya a ranar Alhamis.

    Cikin wata sanarwa da kakain rundunar Mohammed Yerima ya fitar a wanar Juma'a ta ce, an kuma ta yin lugudan wuta ta sama a yankunan da maharan ke boyewa a yankuna irinsu Kusuma da Sigir a de ke Ngala da Arijallamari.

    Hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar manyan kwamandojin kungiyar irinsu Mohammad Fulloja da Ameer Mallam Bello da Ba'a kaka Tunkushe, da Abu Muktar Al -Ansari, Ameer Abba Kaka, sai kuma Abu Huzaifa, da Ameer Modu Kwayem, yayin da Goni Mustapha wanda shi ne limmamin ISWAP din ya tsere da harsashi a jikinsa.

    A ranar 6 ga watan Afrilun da muke ciki rundunar sojin najeriya ta ce ta yi nasarar kashe wasu manyan dakarun ISWAP biyu da suka hada da Abu-Rabi da Muhammed Likita da kuma wasu mayaka da suke tare da su a dai yankuna da aka bayyana da farko.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    An kuma kai hari kan wani wurin ajiyar makaman 'yan kungiyar ta ISWAP tare da lalata shi baki daya a wani harin sama da rundunar Lafiya dole ta kai.

    A ranar Asabar 10 ga watan Afrilu rundunar ta cikin sanarwar ta ce ta kara kashe wasu kwamandoji uku da suka hada da Ameer Umar, da Abu Ubaida da kuma Abu Salim wadanda aka yi wa kwantan bauna a yankin Wulgo zuwa Logomani da ke kusa da kan iyakar Kamaru lokacin da suke yunkurin yi wa makiyaya kwacen shanunsu.

    A ranar 11 kuma an samu nasarar kashe wasu mambobin ISWAP da Boko Haram da ke kan wasu motoci masu bindiga a Damasak. Wadanda suka yi yunkurin fasawa tare da sace kayan da ake ajiye da su a dakin ajiye kayayyaki na Majalisar Dinkin Duniya da magunguna da kuma motocn asibiti.

    @HQNigerianArmy

    Asalin hoton, @HQNigerianArmy

  5. Turkiyya ta haramta amfani da kudin intanet na cryptocurrency

    GETTY IMAGES

    Asalin hoton, GETTY IMAGES

    Babban Bankin Turkiyya ya haramta amfani da kudin Intanen irin su Bitcoin domin harkokin kasuwanci, yana cewa hakan na da matukar hadari.

    A ranar Juma'a bankin ya bayyana hakan yana cewa kuma haramcin zai fara aiki daga ranar 30 ga watan Afrilu da muke ciki.

    Wannan sabuwar dokar ta haramta aika kudi a wajen siyayya ko kuma a biya wanda ya yi wani aiki da irin kudin.

    Bankin ya ce dole a dakatar da aiki da wadannan kudade saboda hadarin da ke cikin amfani da su.

  6. Robar ruwan Zamzam 200,000 ake rabawa duk rana a Masallacin Ka'aba

    zamzam

    Asalin hoton, Haramin Sharifain

    Hukumar masallatan harami na raba robar ruwan Zamzam 200,000 a kullum ga masu Umrah da kuma masu bauta a masallatan a yayin watan Azumin Ramadana, lokacin da suke bin dokar da aka shimfida ta annobar korona a yayin gudanar da ibada, in ji kafafen yada labaran kasar.

    Ana rabon ruwan ne a Mataf da kuma inda mutane ke sallah a dandalin hawan farko na masallacin da kuma inda aka kara domin yin sallah da aka yi wa suna da Sarki Fahad da kuma na Sarki Abdallah.Kimanin mutane 20 ake ajiye wa a ko wacce kofar shiga masallaci suna rarrabawa mutane da suke ziyyara da kuma masu bauta.

  7. Saudiyya ta aika Ƙur'anai miliyan ɗaya cikin harsuna 21 ga ƙasashe 29

    Kur'anai

    Asalin hoton, SPA

    Ma'aikatar kula da harkokin addini ta saudiyya, ta fara raba kur'anai miliyan 1,200,000 fassararru cikin yaruka 21 zuwa kasashe 29 a fadin duniya a matsayin kyauta.

    Jirgin wanda ya fara hadin kai tsakanin ofishin jakadancin Saudiyya da ibiyoyin addini da al'ada da kuma Saudiyya a wadancan kasashen.

    Da yake magana a lokacin gabatar da taron, Ministan harkokin addinin musulunci Dakta Abdallatif Al Al-Sheik, wanda kuma yake lura da harkokin cibiyar dab'i ta Sarki Fahad, ya yi matukar godiya ga mai yi wa masallatan harami hidima Sarki Salman kan wannan taimako wanda ke nuna yadda yake damuwa ga addinin Musulunci.

  8. 'Yan ci rani 20 sun mutu a tekun Tunusia

    PA Media

    Asalin hoton, PA Media

    Masu gadin teku a Tunusia sun ce akalla ‘yan cirani 20 ne suka mutu sakamakon nutsewar da kwale-kwalensu ya yi a gabashin kasar.

    Ana kuma ci gaba da neman wadanda suka bata, amma aikin na fuskntar tangarda saboda rashin kyawun yanayi kuma kawo yanzu mutum uku kadai aka kubutar.

    Jirgin ruwan ya taso ne daga birnin Sfax na Tunusia, inda ta zamo tashar da masu fasa kwaurin mutane ke amfani da gabar teku wajen tsallakawa da ‘yan ciranin da ke son shiga kasashen Turai.

    Ko a watan da ya gabata kusan ‘yan cirani 40 ne suka nutse a tekun, lokacin da kwale-kwalensu ya kife.

    A kowacce shekara dubban ‘yan cirani ne ke kokarin tsallaka tekun Mediterranean daga kasashen Afirka da nufin shiga kasashen Turai domin fatan samun ingantacciyar rayuwa.

  9. Muric ta koka kan hana malamai mata sa hijabi mai tsayi a Ogun

    Kungiyar kare hakkin Musulmi ta yi kira da a sauke shugaban hukumar koyar da malamai ta jihar Ogun.

    Ta zargi shugaban hukumar koyar da malamai a jihar da cewa yana nuna bambanci ga malamai mata Musulmi da ke sanya da hijabi.

    Ƙungiyar Musulmi ta ce shugaban hukumar Evanjalist Ifede ya umarci mata Musulmi da su rage hijabinsu zuwa kafadunsu ko kuma baza a bar su su zauna jarrabawar zuwa mataki na gaba ba.

    Wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman ya aiko mana da wannan rahoto.

    Bayanan sautiRahoto kan Elleman kokawar da Muricta yi na hana malamai mata sa hijabi mai tsayi a Ogun
  10. Buhari ya mika sakon jaje kan mutuwar ɗalibai a Nijar

    Buhari

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike sakon jaje kan mummunar gobarar da ta tashi a makarantar firamare da ke Pays Bas a Jamhuriyar Nijar tare da halaka dalibai 20.

    A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Malam Garba ya fitar, Buhari ya jajanta wa gwamnatin Shugaba Bazoum Mohammed da al’ummar kasar.

    Ya bayyana lamarin mutuwar ‘yan makarantar wanda akasari shekarunsu uku ne zuwa biyar a matsayin "mai tayar da hankali".

    ‘A madadin gwamnati da al’ummar Najeriya, muna jajanta wa makobtanmu kan halin da suka tsinci kan su a ciki," in ji sanarwar.

    "Mu na mika sakon ta’aziyya ga iyalai da ‘yan uwan mamatan da wadanda lamarin ya shafa. Muna musu fatan warkewa cikin gaggawa.’’

  11. Ku saurari Labaran Duniya Cikin Minti Ɗaya

    Bayanan sautiLabarai Cikin Minti Ɗaya Da BBC Hausa Na Rana 16/04/2021
  12. Kotu ta daure wata mata wata 3 kan wallafa hoton tsiraici a intanet

    Ghana

    Wata kotu a kasar Ghana ta yanke wa wata fitacciya a shafin sada zumunta Rosemond Brown hukuncin zaman kaso na wata uku, sakamakon kama ta da laifin wallafa hotonta tsirara tare da danta a gefe.

    Ta fashe da kuka a lokacin da alkalin kotun da ke birnin Accara ya sanar da hukuncin da aka yanke mata.

    A hoton da ta wallafa tun a watan Yuli na ranar murnar zagayowar ranar haihuwa, ta fuskanci danta mai shekara bakwai tsirara kuma ta rike hannunsa, shi kuma yana sanye da dan kamfai, sannan dogon gashinta ya rufe kirjinta.

    Hoton ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta, inda mutane ke ta yi mata tofin Allah tsine. Duk da cewa ta nemi afuwa, amma ‘yan sanda sun gayyace ta domin amsa tambayoyi.

    Kungiyar kare hakkin yara ce ta shigar da karar tare da tabbatar da an yanke mata hukuncin da ya dace da laifinta.

    A ranar Laraba ne alkalin kotun ya same ta da laifin wallafa hotunan badala da cin zarafi da take hakkin sirrin wani mutum.

    An dakatar da sanar da hukuncin kotun har zuwa ranar Juma’a bayan an yi mata gwajin ciki, wanda ya nuna ba ta dauke da juna biyu. Kuma kotun ta ce an yanke mata hukuncin ne domin ya zama darasi ga masu son aikata hakan.

    Tuni ma’abota shafukan sada zumunta suka fitar da maudu’in #FreeAkuapemPolootare da kiran a sake ta.

    Shi ma fitaccen mawakin salon raff na Ghana Sarkodie ya ce hukuncin da aka yanke mata ya yi tsanani na raba da da mahaifi.

  13. Ɗan bindiga ya kashe mutum takwas a Amurka

    ƳAR SANDA A AMURKA

    An kashe mutum takwas sannan aka ji wa wasu da dama rauni a wasu harbe-harbe da aka yi a birnin Indianapolis na Amurka, kamar yadda ƴan sanda suka ce.

    Shaidu sun ji ƙarar harbe-harbe a ofishin FedEx kuma ɗaya daga cikinsu ya ce ya ga wani mutum yana harba bindiga.

    Rahotanni sun ce ɗan bindigar, wanda yake sha'aninsa shi kaɗai, ya kashe kansa. Hukumomi sun ce babu sauran wata barazana ga tsaron mutane.

    Ƴan sanda sun ce waɗanda suka ji raunukan suna asibiti. Sannan lamarin bai shafi hada-hadar jirage a filin jirgin da ke kusa da yankin ba.

    Mai maganda yawun ƴan sanda Genae Cook ta ce, "A yayin da jami'ai suka isa wajen, sun ga an yi harbe-harbe sosai," kuma lamarin ya faru ne da ƙarfe 3 na tsakar dare agogon GMT."

  14. Sama da mutum 60,000 sun tsere daga Damasak

    Sojoji

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum 60,000 ne suka tsere daga garin Damasak da ke jihar Borno a arewa maso gabshin Najeriya bayan munanan hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai.

    A ranar Laraba ne mayakan su ka sake farwa garin, da ke iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar a karo na uku cikin mako guda.

    Jami’an yankin sun ce akalla mutane takwas ne suka mutu a harin da aka kai na baya-bayan nan.

    Kungiyoyin agaji sun janye daga garin na Damasak saboda hare-haren da ‘yan Boko Hram ke yawan kai wa.

    Wani bidiyo da kungiyar ISWAP ta fitar, ya nuna mayaka sanye da kakin soja da manyan makamai sun a ta harbi daga a kori-kurar da suke ciki.

    Haka kuma bidiyon ya nuna mayakan jihadin sun bude wuta, ya yin da gine-gine ke ci da wuta.

    A wannan makon, su ma dakarun sojin Najeriya sun wallafa wani bidiyo da ya nuna sojoji a garin na Damasak sun a aikin sintiri, inda sojojin suka ce su ke iko da garin domin haka jama’a su kwantar da hankalinsu.

    A wannan lokacin hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla kasha 80 cikin 100 na mazauna Damasak sun tsere daga muhallansu.

  15. CBN zai daina bayar da tallafin sayo sikari da alkama daga waje

    Emefiele

    Asalin hoton, CBN

    Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya ce kasar ba za ta kara bai wa masu shigo da sikari da alkama kudaden kasar waje.

    Najeriya wadda ita ce mafi yawan al’umma a Afirka, kuma jagaba ta fuskar karfin tattalin arziki, ta dogara da shigo da abincin da ta ke ciyar da sama da ‘yan kasar miliyan 200 daga kasashen ketare.

    Babban bankin Najeriyar ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Sikari da alkama za su shiga cikin jerin kayan da za a haramta shigo da su Najeriya. Ya kamata mu yi aiki tare dan ganin an fara samar da su a cikin gida maimakon shigo da su daga kasashen ketare".

    A shekarar 2015 ne babban bankin Najeriyar ya sanar da janye tallafin bai wa masu shigo da kayan abinci dalar Amurka, kayan da suka hada da shinkafa, da sauran kayan abinci nau’i 41.

    A watan Agustan shekarar 2019 babban bankin ya sanar da dakatar da bai wa masu shigo da madara daga kasashen ketare dalar Amurka, inda ya ce za a iya bunkasa wadda ake da ita a gida.

    Amma daga bisani ya dage haramcin ga kamfanoni shida na Najeriyar.

  16. APC za ta sayar da fom na gwamnan Anambra kan naira miliyan 20

    Tutar APC

    Asalin hoton, Getty Images

    Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sanya ranar 26 ga watan Yuni a matsayin ranar da za a gudanar da zaben fid da gwani na gwaman jihar Anambra.

    Daraktan shirye-shirye na jam’iyyar Al-Mustapha Medaner ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai.

    Kamar yadda sanarwar ta ce, za a saida fom ga din na-gani-ina-so akan Naira miliyan 2 da dubu 500, ya yin da fom din ‘yan takara kuma Naira mliyan 20.

    Sai dai sanarwar ta ce mata da masu lalurar nakasa za su biya kashi 50 cikin 100 na kudaden.

    Ya kuma ce za a fara sayar da fom din ne daga ranar 15 ga watan Afirilu, zuwa 8 ga watan Yuni mai zuwa.

    Mandener ya kara da cewa za a rufe karbar fom da takardun da suka kamata ranar 8 ga watan na Yuni, inda za a fara tantance ‘yan takara ranar 10 ga watan.

  17. 'Gwamnatin Buhari ta kwashe watanni 10 ba ta biya jami'an tsaron iyakoki alawus ba'

    Jami'an tsaron Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami’an tsaron da aka girke domin tsaron iyakokin Najeriya, sun ce watanni 10 kenan ba a biya su alawus-alawus ba, kamar da yadda jaridar Daily Trust ta ce yawancin jami’an sun shaida mata.

    Dama dai alhakin tabbatar da tsaro da sa ido a kan iyakokin kasar, ya rataya ne a wuyan ofishin mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, da hukumar shige da ficen kasar, ciki har da sa ido domin hana kayan da aka haramta shiga ko fita da su ta iyakokin.

    Daruruwan jami’an tsaron hukumar tsaron farin kaya ta DSS, da ‘yan sanda, da hukumar shige da fice, da hukumar tattara bayanan sirri, da sojoji aka girke a iyakokin Najeriya domin tabbatar da tsaro.

    Batun rashin biyan albashi ko alawus ga jami’an tsaron da ake aikin tabbatar da zaman lafiya a kasar , ba sabon abu ba ne a Najeriya.

    Inda jami’an kan yi korafin ko dai ba a biyasu akan lokaci ba, ko ma rashin biyan baki daya na tsahon lokaci.

  18. Yau za a soma riga-kafin Covid-19 a fadin Nijar

    Riga-kafi

    Asalin hoton, Reuters

    A yau ne ake sa ran gwamnatin Jamhuriyar Nijar za ta fara kai riga-kafin cutar korona, zuwa jIhohin kasar 7 domin fara yi wa mutane allurar.

    Baya ga babban birnin Yamai, ita ma jihar Damagarm na kan gaba a yawan mutanen da ke kamuwa da wannan annoba hakan ya sa mazauna jihar kaguwa wajen ganin an kai masu wannan riga-kafi.

    A watan jiya ne kasar China ta aike wa Jamhuriyar Nijar kwalabe 400,000 na allurar riga-kafin Sinopharm.

    Wani dan jarida mai suna Ibrahim Mallam Tchillo mazaunin jihar Damagaram ya shaida wa wakiliyarmu Tchima Illa Issoufou cewa: "Tun farkon bullar cutar korona, jihar Damagaram na daga cikin johohin da aka samu yawanin wadanda suka kamu da cutar korona. Don haka mutane sun kagu domin ganin an kawo allurer riga-kafin nan an fara yi musu".

    A wasu kasashen ana samun wadanda ba su amince ayi musu rigakafin cutar koronar ba, sai dai Malam Ibrahim ya ce lamarin ya dan sha bamban a jihar Damagaram saboda mutane sun amince akwai wannan cuta, don haka sun amince baya ga daukar matakan kariya daga kamuwa da ita, riga-kafi wata babbar hanya ce kare kai.

    Ya kara da cew: "’Daman akwai mutanen da tun farkon bullarta sun bijire mata, ba su amince da ita ba. Don haka a yanzu ma ba za su yadda ayi musu riga-kafin cutar koronar ba. Amma dole sai an fadakar da su an wayar da kai musamman ga wadanda suke ma ta kallon shaci fadi."

  19. An sanar da ranar zaben shugaban kasar Mali

    Mali

    Asalin hoton, EPA

    Gwamnatin hadin kasa a Mali ta sanar cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun dokokin kasar a ranar 27 ga watan Junairun 2022.

    Ana sa ran kasar za ta koma tafarkin dimukradiyya, bayan juyin mulkin da sojojin kasar suka yi a bara wanda ya hambarar da gwamnatin shugaba Boubacar Keïta.

    Za a fara shirye-shiryen zaben da kuri’ar jin ra’ayin jama’a, ranar 31 ga watan Oktoba a shekarar nan, sai kuma zaben kansiloli a ranar 26 ga watan Disamba.

    Za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu zagaye na biyu a watan Maris din 2022, idan babu dan takarar da ya yi nasarar lashe kshi 50 cikin 100 na kuri’un da aka kada.

    Kasashen duniya dai sun bukaci a dawo da mulkin dimukradiyya a Malin tun bayan juyin mulkin da aka yi.

    A watan Junairun bana ne aka kawo karshen mulkin sojojin da suka yi juyin mulki, sai dai manyan hafsan sojojin sun ci gaba da rike manyan mukaman gwamnatin hadin kan kasar mai mambobi 25.

  20. Lai Mohammed ya zargi 'yan jaridar Najeriya kan rashin bude ofishin Twitter a kasar

    Ministan yada labarai na Najeriya Lai Mohammed, ya dora alhakin rashin bude hedikwatar ofishin Twitter na Afirka a Najeriya kan ‘yan jaridar kasar.

    Mista Lai ya ce yadda ‘yan jaridar kasar ke gudanar da aikinsu da shafa wa kasar kashin kaji ne ya janyo Twitter ya kai hedikwatarsa kasar Ghana.

    Mista Lai na mayar da martini ne kan sanarwar da shugaban kamfanin Twitter Jack Dorsey ya yi a ranar Litinin cewa ya yanke hukuncin zabar kasar Ghana matsayin inda za a bude ofishi na farko a Afirka, "saboda kasar ta zamo zakara ta fuskar tabbatar da dimukradiyya, da goyon bayan ‘yancin fadar albarkacin baki, da yanci a shafukan sada zumunta."

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Mista Lai ya kara da cewa: "Yan jaridar Najeriya sun bata wa kasar suna, ta hanyar nuna tamkar kasar ita ce mafi hadari a duniya. Wannan shi ne sakamakon da kake samu idan ka wulakanta kasarka,’’ in ji Lai Mohammed.

    Najeriya dai ita ce ja gaba da fuskar karfin tattalin arziki a Afirka, tana kuma da karfin da za a bude kamfanin fasaha a ciki. Sai dai tana fama da matsalolin tsaro, da uwa uba zanga-zangar da aka yi kan cin zarafin da ‘yan sanda SARS suke yi wa jama’a.

    Zanga-zangar da akai amfani da Twitter wajen yada ta mai mau’du’in #EndSars, ta janyo shugaba Muhammadu Buhari rusa rundunar da daukjrwa masu zanga-zangar alkawarin yin sauyi kan aikin ‘yan sandan kasar.