Halin da ake ciki kan korona a Najeriya

Asalin hoton, NCDC
Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 84 da suka kamu da cutar korona a ƙasar ranar Asabar.
Bisa sabbin alkaluman hukumar, a wannan rana, Legas ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar a kasar da mutum 26 da aka gano.
Alƙaluman hukumar sun nuna cewa an samu mutum 16 a Akwa Ibom da gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu, abin da ke nufin cewa jihar ce ta biyu a wannan rana.
A jihar Rivers da ke Kudancin Najeriya an samu mutane 10 da gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu da cutar ta korona, sai kuma jihar Ebonyi inda aka gano mutane tara.
Ga adadin waɗanda suka kamu a wasu jihohi
- Abia-6
- Kano-6
- Osun-3
- Bauchi-2
- Delta-2
- Edo-1
- Jigawa-1
- Kaduna-1
- Ogun-1
Zuwa yanzu dai adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya jimlatan ya kai 163,736 ko da yake daga cikinsu an sallami 154,098, sai kuma wasu 2,060 da su kuma suka mutu.
