Biden ya ɗage takunkumin da Trump ya ƙaƙaba wa Fatou Bensouda

Asalin hoton, Reuters
Gwamnatin Joe Biden ta ɗage takunkumin da gwamnatin Trump ta ƙaƙaba kan babbar mai gabatar da kara ta Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC.
Amurka ta kakaba wa Fatou Bensouda takunkumin ne a shekarar da ta gabata bayan da ta sanar da bincike kan zarge-zargen laifukan yaki da ƙasar ta tafka a Afghanistan.
Amurka ba ta taba zama mamba a kotun ICC ba kuma sakataren harkokin wajen kasar, Anthony Blinken ya ce har yanzu Amurka ba ta amince da binciken ba amma ta fi son tattaunawa da masu ruwa da tsaki.
Kotun ICC ta ce ta ji dadin ɗage takunkumin wanda zai tabbatar da gaskiya a kokarin da ake na bin diddigin manyan laifukan.
