Jagoran jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce wajibi ne 'yan majalisa da ɓangaren zartarwa su yi aiki tare wajen samar da kuɗi don rage talauci da rashin aikin yi a ƙasar.
Tsohon gwamnan na Legas kuma tsohon sanata ya bayyana hakan ne a Jihar Kano yayin jawabinsa a wurin taron bikin cikarsa shekara 69 da haihuwa ranar Litinin.
Ya ce dole ne shugaban ƙasa ya sauya salonsa na matse bakin aljihun gwamnati, ya mayar da hankali wajen sakin kuɗi da za su kai ga talakawa.
A cewarsa: "Lokaci ya yi da za a saka shirin bayar da tallafi a gaba, lokacin matse bakin aljihu ya wuce. Babu wani sauran lokaci na matse tattalin arziki, lokaci ne na samar da damarmaki."
Tinubu ya bayar da misali da kasafin kuɗi na tallafi da gwamnatin Amurka ta samar a kwanan nan, sannan ya soki halin rashin aikin yi da ake ciki a Najeriya.
"Ƙididdigar rashin aikin yi ta kai kashi 33 cikin 100 amma kuna so mu ci gaba da azumi. Azumin da muke yi na nafila ne kuma mun daɗe muna yi. Ina fatan shugaban ƙasa da majalisa ba za su karkata ga matse bakin aljihu ba. Jihohi ne kaɗai ya kamata su matse bakin aljihu domin aiwatar da kasafin kuɗinsu.
Har wa yau, Tinubu ya shawarci gwamnatin tarayya ta ɗauki mutum miliyan 50 aikin samar da tsaro.